44

624 42 0
                                    

*MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*




*STORY AND WRITEEN BY......*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*(maryam Obam)*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{united we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*wattpad @maryam-obam*

*instagram@maryam_obam*

*WWW.Maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

*MARUBUCIYAR.....*
*1)FATIMA ZARAH*
*2)DUKIYAR MARAYA*
*3)BA'KIN ALJANI*
*4)BANDA ZABI*
*5)AMINIYA TACE*
*6)KISSA KO MAKIRCI*
*7)SAINA AURESHI*
*8)SUHAILAT*
*9)TAMBARIN TALAKA*
*10)JAWAHEER*
*AND NOW.... MIYE ILLAR Y'AY'A MATA*

*DEDICATED TO...*
*MY LOVELY MUM*

PAGE 44



Amina tace rahma mai kike fad'a haka? Tace mum abunda na fad'a shi nake nufi, zarah tace rahma miye haka kin san abunda kike fad'a kuwa shin.....  Tace zarah dan Allah ya isa haka bana son wannan auren plz Kar Wanda ya takura min akai tana fad'in haka ta haura Sama da sauri, kowa shiru yayi dan mamaki alh Mahmud ne ya Katse musu shurun da fad'in plz zan iya ganinta muyi magana, zarah tace eh muje in raka ka, tashi yayi suka haura sama a falon sama suka ganta zaune zarah fita tayi ta koma, matsawa yayi kusa da ita tare da kiran sunanta, d'ago dakai tayi ta kalleshi ido suka had'a sunyi wajan minti biyu suna kallon juna Kafin ta kawar da idonta, murmushi yayi tare da fad'in naga sona a cikin idonki, amma rahma mai yasa kika ce kin fasa auren bayan Nasan kina so na? Kuka ta saki mai sauti zama yayi kusa da ita tare da rarrashinta, yace haba my princess ki daina Yimin asaran wannan hawayen naki plz, dan tsagaita kukan tayi yaci gaba da fad'in Rahma din dana sani bata boye abunda ke ranta dan haka fad'amin miye dalilinki?tace Mahmud bazan iya aure ba har sai naga khairat tayi, ta girmeni nice kanwarta, mutane za suyi ta Mata surutu, wannan shine dalili na, murmushi yayi tare da fadin hakane rahma, inaso ki sani ina sonki sannan duk wani abu da Kike so zan miki, zan jira har khairat tayi aure sai muyi namu, wani irin murmushi ta saki cikin jin dad'i, tace amma dan Allah kamin alkawari kar kowa ya Sani, yace na miki my love, tace nagode fita sukayi tare alh Mahmud yace mama munyi magana da rahma Nima banso Ayi auren yanzu har sai ta yarda yana fad'in haka yayi musu sallama tare da tafiya, dukansu an barsu cikin duhu Toh Mai rahma take nufi? Amina ce ta kama hannun rahma sukai ciki, tace mai kike nufi rahma? Rahma tace mum bazanyi aure ba har sai Khairat tayi aure sannan nima zanyi, Amina tace what? Kina da hankali kuwa? Yanzu saboda khairat kika 'ki yarda da aurenki? So kike kiyi ta zama a gida, har yanzu babu wanda ya taba cewa yana son khairat koh yazo da Sunan zance, dan haka sam ban amince da wannan maganan naki ba, rahma tace mum nariga na yanke hukunci bana tunanin zan canza, marinta Amina tayi tas tare da fad'in har yaushe zaki ta jira?waye yazo yace yana son khairat fad'amin? Rahma tace bazan iya Sani ba amma mum koda zan mutu bazanyi aure ba har sai Khairat tayi tana fad'in haka ta fita fuuuu ganin khairat tayi ta wajan kofar d'akin da alama taji komai, rahma tace khairat, ganin Rahma zata karaso inda take yasa khairat ta ruga da gudu tana kuka ta shige d'akinta tare da rufewa, rahma buga mata kofar tai tayi tana fad'in khairat dan Allah ki bud'e jin haka yasa su Ummi dasu zarah suka zo, suna tambaya lafiya? Rahma tace mu fara fito da ita tukunna, sunyi bugun duniya amma taki bud'ewa saida Abubakar da driver suka zo suka balla kofar, a kwance suka ganta a kasa farin kumfa na fita a bakinta, da sauri suka kira Dr, ba'ayi minti biyar ba saiga Dr din, nan aka fara bata taimakon gaggawa sannan aka sata a mota ambulance akai asibiti da ita, koda suka karasa emergency akai da ita cikin ikon Allah aka ceto rayuwan ta, amma bata riga ta farka ba, sai dai duk wani guban da taci ya fita, Koda Dr tama su ummi bayanin ciwon y'ar tasu, ran Ummi ya baci Sosai akan Mai zata sha guba? Rahma kam babu abunda take sai kuka, dan tana ganin kaman saboda ita khairat take son kashe kanta, sunyi wajan awa d'aya suna jira Kafin ta tashi, dishi dishi ta Fara gani sannan ta Fara ganin kowa dakyau, ummi rungume y'ar tata tayi, lokaci d'aya kuma ta saketa tare da fad'in khairat Ashe baki da hankali? Kinsha guba so kike ki kashe kanki kin San makoman Wanda ya kashe kanshi kuwa? Cikin kuka tace ummi kiyi hakuri banda wani zabi ne, shi yasa Nayi hakan, rahma tazo da sauri ta rungume khairat tana kuka tare da fad'in kiyi hakuri khairat Wlh b.......  Khairat tace ya isa haka naso in mutu dan na baki daman yin aure rahma kika sani ko Ina cikin wanda har su mutu ba zasu tabayin aure ba, sai yasa har yanzu babu wanda yace yana sona, duk da kullum burina Nima in sami Wanda zaice yana sona amma hakan bamai faruwa bane, rahma tace ki daina fad'in haka insha Allah zaki aure nan bada dadewa ba sanna karki kara aikata wannan abunda kikayi a rayuwa, tace nayi alkawari, kara rungume junansu sukayi suma su zarah suka rungume su, suna cikin haka farida tayi kasa tare da ri'ke cikinta tana nishi, da sauri suka kira Dr, nan akace haiyuwa ne, labour room akai da ita akace suje su d'auko kayan haiyuwa, Abubakar da zarah ne suka tafi daukowa, batai wani doguwar na'kuda ba farida ta sullubo y'arta mace kyakyawa sak babanta faruk, kowa yana ta fad'in Kai yarinyar kyakyawa ita kam Amina k'in amsan yarinyar tayi, ummi ta Lura da hakan ta amshi yarinyar a hannun khairat dake zaune ta mi'ka ma Amina, Amina ja baya tayi tare da fad'in barta kawai, ummi tace jikarki cefa ,Amina tace ba jikata bace domin bazan amshi d'iya mace a matsayin jika ba, jiba halin da muka fad'a damma Allah yasa yaranmu suna da basira, bazan so hakan ta kara faruwa ba har abada, ummi tace y'ay'a mata rahma miye illar y'ay'a mata? Haba Amina baki ga abunda son d'a namiji yaja ma mijinmu ba? Jikin Amina ya fara sanyi ganin haka ummi taci gaba da fad'in kalli yaron sak kaman faruk, jin haka yasa kwallan da take makewa ya fito tare da amsan yarinyar tana murmushi, lokaci d'aya tace sak faruk Allah sarki inama yana nan, kowa shuru yayi yana kallonta, kwanan su biyu aka sallamesu, sukai gida.




Anata hidiman suna amma Amina kwata kwata taki sakewa, yau suna zaune a falo, Amina tazo ta dur'kusa wajan mama tana kuka hankalin kowa ya tashi nan mama tahau tambayan Amina lafiya kuwa? Amina tace dan Allah mama kisa baki su zarah su saka a sake faruk tunda bashi bane yayi laifin ba dan Allah, aneesa amfani dashi tayi dan Allah mama, mama cikin bacin rai tace bazai taba yihuwa ba, Amina tace mama ki taimaka bashi ya kashe mijin mu ba, ki tausaya Mai kodan darajan yarshi, mama shuru tayi can tace shikenan zarah kusa a sako shi, rahma tace mama shine f.....  Mama tace umarni na baku, duka yaran shuru sukayi amma ransu a bace, mama tace su tashi suje su ciro faruk, haka suka tashi su duka harda amina da take ta murna suka nufi station, inda aka basu faruk duk yayi ba'ki ya rame, Amina rungumeshi tayi tana kuka, matsawa yayi kusa da y'an uwanshi dan yayi musu godiya, yace nago.....  Zarah tace dakata karka d'auka danka fito kasha ko mun manta abunda kayi sam ko d'aya bamu manta ba sannan sai munsa kaima an hukunta ka, daka yau babu mu babu kai ka d'auka baka sammu ba a rayuwa, Amina ta kamo hannun faruk dake hawaye tace muje, rahma tayi tsaki sannan Suma suka wuce, koda suka je gida faruk hakuri yaita bama mama tace babu komai ya  gefen ummi ma babu yabo babu fallasa, sai dai yaransu da sukeji kaman su tsige faruk, farida kam ko kallanshi batayi ba yaga yarinyar shi ba karamin dad'i yaji ba tare da son yarinyar Sosai duk da yana son yima farida magana amma bata bashi fuska ba dan tana tare dasu Rahma.Anyi suna yarinya taci suna Amina, yayi ma Amina takwara suna kiran yarinyar da suna Afra.

   *BAYAN WATA UKU*

Har yanzu Anata case dinsu Aneesah a kotu, inda a zama na karshe ake sa ran yanke hukunci, abubuwa da dama sun faru ciki harda komawan aysha d'akinta domin Maman mijinta tazo da kanta ta bada hakuri tare da fad'in shairin shaidan ne, zainab kuma an raba gado an bata nata kason ita da y'arta, sannan akwai wani guy Da yake Sonta Mai suna Muhammad, abokin alh Mahmud ne da suka zo tare yaga zainab ya mutu a kanta da farko bata amince ba saida kyar ta amince domin irin kyautata mata da yakeyi da nuna yana son y'arta, shine yasa ta yarda gasu ummi da zarah dake ta bata shawara, ta gefen faruk kam har yanzu y'an uwanshi mata basu sake Mai ba domin Sun tsaneshi Sosai,  khairat ita kuma ta sami aiki a wani babban company inda kwazonta yasa kowa ke yabanta, oganta a office sunanshi Muktar yana da son Mata Sosai gashi yaro Muktar shine d'a d'aya wajan mum dinshi, sai yasa yake she'ke ayarsa babu ruwanshi tunda yaga mum dinshi na sonshi tun yana dan shekara Goma sha biyu dad dinshi ya rasu mum dinshi ita ta ri'ke Business dinsu har Mukhtar ya girma ya kammala karatu ya amsheta, Muktar kyakyawa ne ajin Farko, Mata na sonshi Sosai dan yana da kyauta, akwai wata yarinya mai suna hauwa da yaso ya aura mum dinshi ta gano y'ar iska ce ta hana auran, duk da burinta kullum shine d'anta yayi aure, akwai sanda khairat takai mai wasu takardu office taga yana kissing din wata yarinya, tace mishi kaji tsoran Allah komai kakeyi Allah yana kallonka mum dinka mutuniyar kirki ce Banyi zaton jininta zaiyi haka ba, tana gama fad'in haka ta fita, tun daka ranan yake ta neman hanyar da zaiyi maganin khairat, yau yana office yana duba file ya tashi tsaye cikin fad'a ya nufi waje wajan staff bai tsaya wajan kowa ba sai wajan khairat yace no wander sai yasa har yanzu kika kasa samun mijin aure saboda wannan idon naki Mai ido hudu ke wace irin wawiya ce haka nace kiyi watsa mata yayi a fuska yace maza ki gyara yana fad'in haka ya koma ciki, khairat kuka tasa Mai taba zuciya, lallai itama rashin jin magananta yaja mata suda  suke da nasu company din amma tazo wani waje tana aiki ai dole taga ba dai dai ba  amma daka yau zan ajiye aikin, rubuta resignation letter tayi takardan barin aiki, yana zaune a office sai gata ta shigo kallonta yayi cikin fad'a kin gyara? Jefa Mai takardan tayi a fuska tace gashi takardan barin aiki, bazanci gaba da aiki a karkashin dabba irinka ba, tana fad'in haka ta fita gashi da karfi take maganan duk staff suna ji, Muktar tunda yake yau itace rana ta farko da akaci zarafin shi, iska Mai zafi ya furzar tare da fad'in saina aureki nasa kinyi dana sanin wannan abunda kikayi saina lalata miki rayuwa nayi alkawari.








     *vote*
*comment nd share*

*Maryam Obam*

MIYE ILLAR Y'AY'A MATAWhere stories live. Discover now