Part 7

1.2K 48 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*11/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
_Luck is not in ur hands,but work is,ur work can make ur luck Good day,Good luck habiibtiiy @ *NI'IMATULLAH MUHAMMAD USMAN.*_
__________________________
_U guys wollah har kunsa na rasa bakin magana,saboda yadda kuke nunamin k'auna ya wuce baki ya furta,har kullum ina muku fatan alkhairi *#Masoyana.*_ ♥💋
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*31--32.*
_____
_____

°°°°°°°°Kasa fita yayi ganin yanayin da take ciki,a hankali ya saki k'ofar ya dawo da baya,itanma a hankali ta bud'e lumsassun idanunta a tunaninta ko ya gaji da tsaiwar ya tafi,yunk'urawa tayi zata mik'e zaune amma sai ta kasa,kasancewar duk sa'ilin da za tayi k'wak'waran motsi sai taji kamar kanta zai fice daga jikinta tsabar azabar da take ji.Komawa tayi ta sake yin lamo ta kwanta a k'asan tana damk'e kanta da duka hannayenta biyu.
Duk abunda take yana tsaye yana kallonta cike da tsantsar mamakinta da ganin k'arfin halinta,takowa ya fara yi cikin nutsuwarsa har ya dawo dai-dai inda take kwance,baiyi mata magana ba ya shiga janye hannun long sleeve ensa,tsugunawa yayi tare da tallafota ya nufi saman bed da ita,kwantar da ita yayi sannan ya d'an jinginata da jikinsa,sai daya gyara zaman pillows en dake kan gadon sannan ya jinginata jikinsu ya kasance ita ba'a kwanceba kuma ba'a zaune ba,kallonta yayi idonta har lokacin a rufe suke ta kasa bud'ewa,a hankali ya janyo tray en abincin ya ajiye saman cinyarsa yana gyara zaman sa a kusa da ita,spoon yasa a ciki ya d'ebo yana kai mata shi dai-dai bakinta,k'in bud'ewa tayi har sai data sashi jin haushi yayi magana
"Ki bud'e bakinki ki amsa.."
Maimakon ta bud'e bakin sai yaga ta bud'e idonta a hankali tana kallonsa,fuskarta ta d'an yamutse cikin muryan masu jinya ta furta
"Baran iya ciba.."
Da sauri kuma ta nemi zamewa ta kwanta saboda maganar da tayi yanzun ji tayi kamar an k'wala mata wani abu akan,saurin ajiye cokalin yayi ya tare ta yana binta da wani mugun kallo,hak'ura tayi da kwanciyar ta zauna badon ta soba
"Kin tab'a ganin anyi jinya babu cin abinci bare shan magani.?"
Ita dai bata kula shiba haka kuma idnunta a rufe suke,bare ta kalle shi tasan da wane irin yanayi yayi maganar
"Ki amsa abincin ko yaya ne saiki sha maganin ki kwanta zai taimaka miki har maganin yayi aiki a jikinki.."
Still dai tana a yadda take,shima ganin bata motsa ba yasa shi sake d'ago spoon en,ga mamakinsa sai gani yayi ta bud'e idonta da bakin,bata abincin ya shiga yi tana karb'a,baifi spoon bakwai ba ta gimtse bakinta tak'i ci gaba da karb'a,ba yadda zai yi haka ya k'yaleta,prescription en ya b'alle ya mik'a mata,ita da kanta ta d'auka a hannunsa,sannan ya mik'a mata glass cup da ruwa a ciki,tana shanyewa ya amshe cup en ya d'ora saman tray,idanunta ta mayar ta kulle,bai sake kallonta ba ya tashi daga kusa da ita ya koma can saman sofa,wayansa dake cikin aljihun jeans ensa ya fiddo nan ya shiga latse-latse,ya shafe tsawon wasu mintuna da suka haura ashirin sannan a hankali ya d'ago ya kalleta ganin yadda kanta ya d'anyi bending yasa yayi tunanin ta samu bacci,tashi yayi ya tura wayan a aljihunsa kana ya nufeta,a hankali ya gyara mata kwanciya bayan ya janye pillows en gefe,sai guda d'aya daya bar mata wanda kanta ke kai,lullub'e mata k'afafunta yayi har zuwa dai-dai chest enta sannan ya d'auke tray ensa bayan ya kashe mata hasken d'akin ya fice had'e da nufar down stairs.
Su Ummi ya tarar zaune suna d'an tab'a hira kad'an-kad'an kuma duk akan ciwon daddy'nsa ne zancen nasu,kujera yaja ya zauna yana sauke ajiyar zuciya,kallonsa Ummi tayi da d'an murmushi ta furta
"Ya akayi ne d'an albarka..?"

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now