Part 11

1.2K 44 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*17/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*49--50.*
_____
_____

°°°°°°°°Fad'a Mama ta shiga mata bayan dawowarta akan bata kula sosai,da rashin godiyan da bata masa ba na taimakonta da yayi d'aya barta ta dad'i ai da yanzana nan tana faman raki da kuka,kallonsa tayi ranta a b'ace ganin yadda ya daketa kuma yake k'ok'arin hanata kuka,tana tura baki ta furta
"An gode.."
Daga haka bata sake magana ba ta tattare kayanta tayi hanyar komawa sama
"A'a k'anwata tafiya kuma za kiyi,naga kina karatu kiyi zamanki mana nan abunda baki gane ba sai a sake nuna miki.."

"A'a na gode na iya kuma zanyi da kaina,kasan kan bana dak'ik'ai bane.."
Sarai ya gane magana ta fad'a masa kawai sai ya wayance da fad'in
"Haaa..! I see."

Sai data faki idon kowa ta zabga masa harara sannan tayi sama abunta da sauri,shima da harara ya rakata,dan duk wannan jantan da yake yi da maganar yana yine don kawai yayi basaja.Amma bawai don yana mata hakan don son ransa ba.

A nata b'angaren kuwa itama Unaysa bayan komawarta sama rufe kayan karatun nata tayi tana tunanin abunda zata masa ta fanshe fad'an daya janyo mata,sai dai duk iya kar k'ok'arinta ta kasa samun mafita,wanda a k'arshe kasancewar babu yadda ta iya ta hak'ura ta bar tunani,amma har cikin zuciyarta bawai don ta hak'urewa d'aukar fansarta ba.

Kwanaki uku tsakani har lokacin Unaysa sai troops take ta shirya masa na yadda zata rama abunda ya mata,haka har lokacin bata manta da komai daya mata ba.Hasalima duk lokacin data tuna haushinsa ne yake kamata,yinin ranar ko baza ta bari koda hanya ta had'asu ba dan gani take kamar zai gano irin yadda take shirya plan enta.

Fitowarsa kenan daga wanka bayan ya gama shiryawa ta shigo,da sauri ta juya masa baya hannayenta a saman idanuwanta ta rufe tana fad'in
"Ohhh! sorry.."

Tsaki ya saki yana kallonta
"Mene ne zaki wani fad'owa mutum a ka ba tare da neman izini ba..?"

"Aaa! Amm! dama..."

"Dama me...? kin wani tsaya sai kame-kame kike ki fad'i maganarki kawai ban son inda-inda wannan duk alamun zaki fad'i k'arya ne.."

Saurin bud'e idanunta tayi da fad'in
"K'arya kuma..?"

"Eheem! k'arya mana,idan ba shiba meya shigo dake d'akina yau tunda nasan baki tab'a yin hakanba..?"

"Ok.! kayi hak'uri.."

Saurin juyawa tayi zata fice ranta duk babu dad'i saboda yadda ya kirata da mak'aryaciya,saurin fizgota yayi ta dawo baya

"Kina hauka ne ina magana zaki wani nemi ficewa,ko ni sa'anki ne da zaki juyamin k'eya..?"
Bata tanka masa ba saboda tunaninta ya bata kada tayi kuskure a wannan lokacin dan komai zai iya faruwa tunda ita ta kawo kanta gareshi zai iya mata komai,dalilin da yasa bakinta mutuwa kenan,juya idonta tayi aiko sai yaga kamar ta harareshi,hankad'ata yayi daga jikinsa take ko ta fad'i k'asa k'afarta ta k'ume da gefen bed ensa,tsabar azabar data ratsata har bata san sanda ta saki wani marayan ihu ba,bai ko saurare taba cikin masifa ya furta
"Dallah malama ficemin a nan kafin kisa raina ya b'aci na k'aryaki.."

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWo Geschichten leben. Entdecke jetzt