Part 25

978 37 0
                                    

*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_(Palace of excitation & pleasant writer's)._~
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*4/March.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/Smasher&HubbeeyNovelsGroup/369678263526212/
___________________________
_*MAMAN NOOROUL HOODAH* marubuciyar *IKLAS & EESHA* gaskiya muna farin ciki had'e da jinjina gareki na saudakarwarki garemu ~SMASHER & HUBBEEY~ basu da bakin magana ko godiya a gareki,sai dai addu'ar fatan alkhairi da a kullum muke fatan ki kasance cikin amincin ubangiji,Allah saka da alkhairi muna godiya sosai bisa mutuntawar da kika mana,fatan rabb ya k'ara miki fikira sama da wacce kike da ita.._
___________________________
_Habiibtiiy *HABIBA IDREES (HUBBEEY)* ahuwa kwana biyu ban baki page ba,dama naga har hararata kika samu damar yi,ga shi nan to the hole page is ur's ki yi yadda kika so da shi._
__________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*129--130.*
________
________

°°°°°°°°Yatsina fuska Fateema tayi tana bin Unaysa da wani irin kallon raini,a tunaninta Unaysa'r wata banza ce can bakinta cike da fad'in
"Allah sarki sannunki fa Unaysa.."
Kaf mutanen cikin parlour'n babu wanda bai fahimci a yanayin da tayi magana ba,musamman Abbas da yake kallon fuskarta tunda yaji Fadeela tana describing matsayin Unaysa a gurin ta,yasan dama dole ne a samu wannan matsalar muddin ta fahimci wace ce Unaysa'r,ita ko Unaysa jin yanayin yadda tayi furucin yasa ko d'agowa bata yiba bare ta kalleta tasan kuma da ita take,yadda tayi ya dad'a tunzura Fateema take ta shiga cika tana batsewa ita a dole kishi dan tana jin Fadeela ta ambaci sunan Unaysa ta gane wacce ake maganar akanta.
Inda take zaune ta tana yatsina fuska had'e da karkad'a k'afa tana faman harare²,ni ko dai da nake gefe nace "A banza....! Wai anyiwa dala dundu."
Sabgoginsu suka ci gaba da yi ba tare da suna sawa da ita ba,musamma ma Unaysa data watsata a dustbin,yadda ta d'auke ta tamkar ita da babu duk d'aya, sai dai ko Fadeela idan tayi magana tace
"Auntynah kinyi shiru fa kink'i magana.."
Data ji tace haka sai ta d'an yi yak'e da fad'in
"To ni me zance ne...?"
Wannan amsar da take bayarwa yasa tun daga nan babu wanda ya sake sata cikin hiran,ko da suka mata shiru suka dena sawa da ita sai abun ya sake b'ata mata rai fiyema da ganin Unaysa da tayi,har Fadeela ta gama shirinta tsaf ta fito suna zaune sai dai babu mai tankawa wani tsakaninta da Fateema,futowar Fadeela yayi dai² da lokacin da Mom ke fad'in
"Fadeela ku d'an jira kad'an na aiki driver kasuwa yanzun.."
Turus tayi a tsaye dan bata yi tsammanin jin hakan ba,a tunaninta tana fitowa wucewa kawai za suyi gurin gyaran jikin,nan saman kujera ta zauna tana tunanin hanyar da zasu bi dan kada suyi dare,ta d'an jima tana tunani kafin ta kalli Abbas da yake shirin fita
"Yaya tafiya za kayi ne..?"
Sai daya juyo ya kalleta sannan ya d'aga mata kai tare da fad'in
"Ehh! Da wani abu ne..?"

"A'a dama dai tambayarka zanyi idan hanyan da za muyi ne sai ka ajiyemu.."
Sunkuye take tana latsa waya amma jin abunda Fadeela ke fad'a tuni ya haddasa mata saurin d'agowa ta kalleta tana tsuke fuska, ga Fateema kuwa ko data ji abunda Fadeela ta fad'a nan ta fara hura hanci tana jiran taji me zai ce mata,a gefen Unaysa kuwa ba komai take ba illah addu'ar Allah yasa ba nan zai yiba,cikin rashin sa'a bud'ar bakin Abbas ko sai cewa yayi su shirya ya kaisu,wani mummunan fad'uwa gabanta yayi daya tilasta mata runtse ido,murna Fadeela ta fara dan dama ta k'agu su tafi,bedroom enta ta nufa da shirin ta d'auko abunda bata fito da shi ba.
Tunda Unaysa taji ya amsa ta fara neman nutsuwarta ta rasa,take ta fara line wayan Akmaal,ring d'aya yayi reject sannan ya kirata,can daga gefen sa jin ta d'auka bata yi magana ba yasa shu fad'in
"Baby yane..? Naji kinyi shiru.."
Ajiyan numfashi tayi sannan cikin y'ar damuwa dan ranta a b'ace yake har lolacin ta daure tana masa magana k'asa² ta yadda ba lallai ne wanda yake gurin ya jita ba
"Yayanah kana wani abu ne yanzun..?"

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDDonde viven las historias. Descúbrelo ahora