Part 9

1.1K 47 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*13/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
_Alkhairin Allah ya isar muku *Safiyya Bala (Mom Hanan)* & *Khadija Salihu (Deezoh)* Allah yasa kuna cikin k'oshin lafiya._
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*37--38.*
_____
_____

°°°°°°°°Kallon k'ofan kawai ya d'an yi a hankali kuma ya sauke k'afafunsa k'asa ya mik'e,sake kallon k'ofar toilet en yayi a hankali kuma ya tab'e baki sannan ya fice a d'akin da sauri.
Kamar wata wacce tayi gamo da zaki ko damisa haka ta dafe k'irji tana haki ta lafe a jikin k'ofar toilet en,sai data tabbatar ya fice a d'akin sannan ta fito cikin sand'a tana waigawa,k'ofar d'akin ta nufa ta kulle sosai sannan ta dawo ta zauna duk sai jinta take ba a cikin nutsuwarta ba,korar shad'anin daya kawo mata ziyara tayi sannan ta mik'e ta kabbara salla'rta.
Ko bayan data idar da sallah kasa karatun tayi tunani duk ya dameta,tagumi ta buga da duka hannayenta ta zubawa guri d'aya ido a fili ta furta
"Ya Allah! wai kada dai ace duk abunda nake tunanin mafarki nayi a gaske ya faru..."
Shiru ta d'anyi na wani lokaci kafin taci gaba da fad'in
"Tabbb' idan ko haka ne ban san ya zanyi ba,yanzun fisabilillah aka ce duk wannan abun a gaske ne aiko kallonsa na daina yi bare mu had'a hanya da shi.."
Shiru tayi tana nazari a hanakali ta d'an saki murmushi
"Kaiii! duk fa wannan rud'un ni nake neman jagulama kaina lissafi duk wannan ba gaskiya bane sharrin mafarki ne kawai na sani.."
Bata k'arasa ba ta sake yin shiru
"To amma meya kawo shi d'akin nan idan har duk wancan ba gaskiya bane..?"
Tayiwa kanta tambayar,rashin samun amsa yasa ta sake cune fuska kamar za tayi kuka saboda a wannan karon kam ta gama fahimtar bafa mafarki tayi ba a zahiri komai ya faru,hawaye ta goge kana ya bishi da Allah ya isa,hannunta ta kai kan lips enta tana shafawa,a hankali ta saki wani siririn tsaki tana sake had'e fuska tana hararan gurin daya tashi kamar ance mata har lokacin yana zaune a gurin.(Ni kam dai nacewa Unaysa ayi dai mu gani,idan tusa zata hura wuta). 😄

Misalin 7:00am ya shigo parlour sanye cikin k'ananun kaya fuskarsa babu walwala,da Ummi suka fara had'uwa a yadda yake ba tare daya damu da sakin fuska ba ya gaisheta yana sauri coz baya son ta tsayar da shi,amsa masa tayi itama babu yabo bare fallasa,kafin yayi yunk'urin barin gurin ta tare shi da fad'in
"Akmaal raini ne yasa jiya ka kashe wayoyinka kuwa me kake nufi..?"
Tsayawa yayi cak a inda yake,kansa ya sunkuyar k'asa had'e da nazarin maganarta
"Wato kasan inda take shi yasa kayi ficewarka har na gama zaman jiran ganin shigowarka saboda ka rainani shi yasa daka fice ko k'yallinka ban sake ganiba sai yanzun ko..? Ni inda ka kai yarinyar mutane kawai nake son ji daga bakinka,idan ka fad'amin inda take wannan ne kawai zaisa yau na kyaleka,amma wollahi kaji na rantse idan baka sanarmin da gaskiya ba,Allah zan maka abunda tunda muke da kai ban tab'a maka ba,haba Akmaal wannan duk d'abi'un a ina ka d'ebo su..? Ko kad'an nasan wannan ba tarbiyyarmu bace,da bakai irin wannan rayuwar ba sai yanzun da kake girma,me yasa zaka aikata haka,shin kasan abunda mahaifiyarta zata ji idan ta samu wannan bak'in labarin..? Tabbas baka sani ba domin kuwa uwace kawai zata iya shiga wannan halin,ku maza baku san iya adadin rad'ad'i da damuwa da mahaifiya ke shiga ba a duk lokacin da wani abu ya samu d'an ta,har kullum maganata daku itace kada ka tab'a cutar da na k'asa da kai,dan kuwa baka san kai wane irin hukunci ubangiji zai maka ba,bisa cutar da kayiwa wanda ya fika rauni..Amma kayi tunani na baka lokaci zuwa k'arshen wannan yinin ka tabbatar ka dawomin da yarinyar nan kuma ka kawomin ita gabana cikin k'oshin lafiya,Allah ya kiyaye hanya ubangiji ya bada sa'a ya kuma tsaremin kai..."
Tana kaiwa nan a zancenta ta mik'e tabar gurin ba tare data bashi damar yin magana ba,jikinsa ne yayi sanyi jin a yanayin data masa magana,a hankali ya mik'e yabi bayanta.

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWo Geschichten leben. Entdecke jetzt