Part 12

1K 45 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*19/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*53--54.*
_____
_____

°°°°°°°°Jiki babu k'wari ya fice daga parlour'n,tsabar k'i fad'i irin nasa ko kad'an baiyi tunanin tambayar kowaba a cikin gidan,a nasa tunanin yadda suka koma suka jone da ita babu fad'a sai dai suyi abunsu a b'oye ai sai ayi masa dariya a gidan idan yace bai sani ba.
Tafiya kawai yake ba tare daya sanma ina zai fara nufaba,lokaci² yakan kalli gefe da gefensa idan yaga guri kamar makaranta sai ya d'an tsaya yana tunani,haka idan yaga gurin bai masa kama da makarantar da za'a iya sata ba saiya wuce abunsa,haka yayita garari a kan kwalta ba tare d'aya samu inda yake nema ba.

Agogon hannunsa ya kalla kimanin awa biyu kenan da fitowarsa kuma duk akan neman makarantar da bashi da sanin takamaiman wacce ce,tsaki ya saki lokacin da yayi parking a gefen wata makaranta yana tunanin anya kuwa bare kira Dad ya tambayeshi skul enba,zuciyarsa ce ta bashi shawara akan kada ya kuskura ya kira,idan kuma har ya bijire ya kira en tofa lallai ne abunda bai so dole sai anyi masa shi wato fad'a,sabon tsaki ya saki,can kuma ya sake fad'in
"To ko Mama zan kira ne..? Kaii a'a da kunya ai na tambayeta makarantar da y'arta ke zuwa bayan tana kallon yadda muke da y'arta a gaban idonta..."

Shiru ya d'anyi yana tunanin to ko dai na kira Ummi ne? itanma dai zuciyarsa bata bashi shawaran kiranta ba,haka yayi ta tsaiwa a wajen ba tare daya samu abunda yake nema ba..

^^^^^
Cikin 1 hour 10 minutes ta kammala rubuta paper enta,had'a takardunta tayi tana gyara zamansu da niyyan tashi ta fice idanunta ya kai mata kan paper partner enta,babu abunda ta rubuta a paper yadda aka bata ita haka take plain,kallon mamaki tayi mata ganin duk exam ensu na baya ba haka take yiba,sosai ta tsaya nazartarta,yanayinta yau yasha bamban da sauran ranaku especially ma data santa mai kazar-kazar ce amma yau duk sai taga ba haka bane dan ita sai lokacinma ta k'ara karantar yanayin da take ciki,gyara zamanta kawai tayi ta tsaya tana nazartar gilmawar invigilators en duk kuwa da yadda take a tsorace,fakar idon na kusa dasu tayi da yake shawagi akansu,ta janyo booklet en nata ta tura mata nata,fuska ta d'aure sannan ta shiga rubutu da sauri-sauri kasancewar abunda ya rage musu bai kai 1 hour su fita ba,dan a lokacinma wasu sun fara haramar fita,cikin 45 minutes ta rubuta abunda ya sauwak'a sannan ta sake maida mata da booklet enta tana fad'in
"Ki rubuta sauran detail's enki ki kai.."

Da kai ta amsa mata tana mata murmushin k'arfin hali,jan tata takardar tayi ta tattara y'an kayanta ta fice daga cikin hall en,zuciyarta cike da farin cikin zuwan wannan rana mai cike da tarihi,k'walla ne ya tarun mata a gefen ido a hankali tasa hannu ta gogesu tana murmushi,can gefe ta samu seat ta zauna k'arkashin wata bishiya tana jiran taga ta inda driver zai b'illo ya d'auketa.
A hankali take tafiya cike da dauriya har ta k'araso kusa da ita tayi mata sallama,amsa mata tayi tana d'an sakin murmushi
"Sannu da hutawa y'ar uwa..Gaskiya kin taimakamin wollahi har nama rasa ta ina zan fara miki godiya,don ba daban keba da yau kam na tabbata haka nan zan bada paper'na plain ba tare dana rubuta komai ba,na gode sosai Allah saka miki da alkhairi.."

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWo Geschichten leben. Entdecke jetzt