Part 26

2K 54 3
                                    

*AWESOME WRITER'S ASSO..🏮*
~_(Palace of excitation & pleasant writer's)._~
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*6/March.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/Smasher&HubbeeyNovelsGroup/369678263526212/
___________________________
_*HUSSAINA B ABUBAKAR (MR'S ABUBAKAR) ina tayaki murna da farin cikin kammala wannan littafi naki lafiya na *HA'DIN ALLAH NE*,ubangiji yasa yadda kika gama ya amfani al'ummah..Ameen._
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*133--134.*
________
________

°°°°°°°°Yauma tun da wuri suka shirya sai dai basu fito a lokacin ba sai da suka gama duk abunda zasu yi,sannan suka d'auki hanyar gida dan dama yau can ne za suyi taron ranar,gidan cike yake da mutane,dangi guda ne amma duk wanda ya kallesu zai iya gano hakan musamma yadda suke kama da juna,ko Mama da Unaysa da suke bare a cikin wannan family,duk iya son gano hakan a gurin mutum bare tab'a ganewa ba,saboda yadda suka saje da ahalin,taro ake sosai ko ina gidan ka duba jama'ac,wacce lissafasu zai zamewa mutum aiki.
K'arfe 4:00pm al'ummah y'an biki suka fara isowa,tun daga bakin get mutum yana zuwa zai tabbatarwa kansa shagalin da ake ba k'arami bane,an k'awata harabar gidan da ado sosai,a haka taron ya soma,su Unaysa kam an nausa cikin taro dan ko hangota ma banba bare na bada shaidar abunda idanuna basu gani ba a wannan rana daga ita kuwa har Oga Akmaal.
Can daga bakin get kuwa dai² wannan lokaci da shagali ya fara tafiya,tuni k'ugin k'arasowar motoci ya fara tashi,gaba d'aya a waje suka fara parking mutane na shigowa da k'afafunsu,sai wata mota guda d'aya da aka k'awata da adon furanni,yadda motar ke shek'in sabunta yasa kana kallo ba sai an maka dogon bayanin sabuwa bace,ita kad'ai ce motar da aka bari ta ratso cikin harabar gidan,ba ita ta tsaya ba sai a dai² gurin da aka baje manyan carpet en da amarya da hango zasu zauna wanda aka k'awata da wasu had'ad'd'un tumtum,cikin nutsuwa aka bud'e k'ofar motar d'aya,k'afarsa ya fara zurowa sannan ya fito fuskar nan d'auke da annuri,sky blue en shadda ne data amsa sunan ta,sai aiki da aka yi da zare mai duhu wato royal blue,kansa sanye da hular nan da akewa lak'abi da minister,sai bakin cover shoe da yake sanye a k'afarsa,yayi kyau sosai a matsayinsa na namiji da dama su ba'a sansu da wani kyale² ko kwalliya ba,a hankali ya kalli k'ofan yana murmushi da fad'in
"Hayatiiy..! Fito mana kin sanfa mu ake jira.."
Murmushi tayi itama kafin ta tako k'afarta waje tana sauke idanunta a k'asa,shigansu irin d'aya ne da shi sai dai ita complete royal blue tasa,kasancewar ta fara sai colour en ya karb'e ta sosai,fuskar nan taci uban ado da duk wanda ya kalleta dole ne ya k'ara kallonta,ko data fito ta dai²ta tsaiwarta sai suka jera suna tafiya tare yayin da dangi suke binsu da ruwan flashes,a haka har aka rakasu zuwa mazauninsu,ko da MC yaga amarya da ango sun zauna,nan ya busa loudspeaker ensa yana sake jaddada isowarsu ga wad'anda basa kusa,kafin kace wani abu tuni har filin ya sake d'inkewa da al'ummah,y'an gayyar sod'i ne da sauran al'ummah duk babu wanda babu,a haka taro ya fara inda dangi suka shiga nuna bajintarsu,kowa ya shiga ware bakin aljihu da jaka yana zazzaga musu iya abunda zai iya.
Shigowar wata sabuwa fil en mota data so tafi ko wacce kyau da tsari cikin harabar gidan,ta matuk'ar d'aukan hankalin jama'a,an d'auki lokaci tsakanin parking en motar sannan aka bud'e side en driver aka zuro k'afa d'aya,kad'ata ake tana d'an bugun k'asa a hankali har kusan fiye da mintuna biyar sannan aka k'arasa bud'e motan aka fito,Akmaal ne ya bayyana cikin shigarsa tamkar ta Ajmaal,abunda ya so rud'ar da al'mmar gurin kenan,suka rasa gane shin wanne ne angon na gaskiya,wani killer smile ya saki ta gefe yana shafa fuskarsa kafin ya maida murfin motan ya rufe ya zagaya d'ayan side en,sai daya fara knocking glass en kafin ya bud'e k'ofan,k'afafunta ta zuro waje duka biyu kana ya mik'a mata hannunsa na dama,sai data kama tukun ta mik'e tsaye suka jero cikin takun k'asaita,suna tafe suna hira abunsu gwanin sha'awa,sosai abun nasu ya burgeni d'aukacin jama'ar wajen,kafin kace me tuni mutane sunyi zuga sun nufesu,sai hasken flash kawai suka fara gani akansu,tun daga bakin motan su har zuwa inda su Ajmaal suke,dai² inda suke zaune suka ci burki,nan aka fara kallon kallo tsananin Akmaal da Unaysa,Jakarta ta shiga shirin bud'ewa yayi saurin rik'ewa ya karb'eta daga hannunta,sai daya bud'e jakar ya d'an lek'a kafin ya d'ago ya kalleta yana sakin murmushi dayi mata winking,gani kawai mutane sukai yasa hannu cikin aljihun babbar rigansa,amma babu wanda ya kula da me ya ciro yasa a jakar tata,sannan ya mik'a mata yana mata rad'a a kunne,kawai dai anga sunyi dariya,a tare kuma suka fito da rapper na 500# suka balle,a jaka Unaysa ta sawa Fadeela tana mata murmushi,shima ya sawa d'an uwansa a aljihunsa,koda ta juya kan Ajmaal kuwa dariyar yak'e ta masa kana ta sake zura hannunta a jakanta,wata tsohuwar naira biyar ta ciro a nannad'e ta mak'ale jakarta sannan ta manna masa ita a goshi,gaba d'aya aka sa musu ihu a gurin,shi kuwa Ajmaal ko da yaga ta ciro tsohuwar naira biyar ennan kuma ta nufo shi da ita,tuni ya gimtse dariyar da yake yana binta da kallon tama raina masa hankali,sai daya bari ta lik'a masa ita a goshi ya d'ago ya kalleta yayi murmushin yak'e yana cewa
"Lallaima yarinyar nan...amma fa kin latsani da yawa,banda raini ni zaki bawa #5..?"
Dariya tayi kafin ta ce
"Yo biyar enma daka ci sa'a har ka ganta,kuma fama ba bar maka ita zanba danma ka sani.."

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDDonde viven las historias. Descúbrelo ahora