Part 18

994 53 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*9/Feb.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*91--92.*
_____
_____

°°°°°°°°Fitowarsa tayi dai² da shigowarta a corridor en ranta a b'ace tana mita,karo suka yi da juna tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota,kwanciya tayi saman hannunsa idanunta a rufe,kallonta yake da mamaki a fuskarsa,jin an tareta gashi bata san ko waye ne yayi hakanba,ta shiga bud'e idanunta a hankali,k'ok'arin mik'ewa ta shiga yi daga jikinsa tana tsuke fuska,amma duk da haka ya k'i sakinta,ganin haka yasa ta furta
"Malam wai mene hakan zaka wani rik'e ni..?"

Bai kulata ba illa kawai mik'ar da ita tsaye da yayi ya kuma juya da niyyar barin wajen,yamutsa fuska tayi ta saki d'an siririn tsaki ai kafin tayi k'wak'wk'waran motsi tuni ya juyo a fusace ya dank'ota,yana huci yake tambayarta
"Mene kika yi yanzun...?"
Idanu ta shiga juyawa da mamakin tambayarsa
"Tambayarki nake me kika yi..?"
Ganin yadda yake mata tsawa gashi gidan da alamun su kad'aine a ciki yasa ta rarrashi ranta duk sonta data masa tsiwa,marairaicewa tayi tana kad'a masa kai,yatsansa ya shiga karkad'awa a dai-dai saitin fuskarta,ba tare da yace komai ba ya saketa had'e da shigewa bed room en daya fito.
Itanma jiki babu kwari taja k'afafunta ta koma nata bedroom en,can k'arshen bed ta koma tana tuna irin rik'on daya mata,a fili ta furta
"Waii Allah yaso ni,nasan yadda muke mu kad'ai ennan wollahi bai k'i ya lallasa niba yadda dama yake yawan min warning bana ji yau kam Dana fad'ama y'an garinmu,jifa yadda yamin tsawa amma duk na wani firgita,ko yaushema na fara tsoronsa ohoo.."
Wani tsakin ta sake yunk'urin yi,kome ta tuna kuma tayi saurin dank'e bakinta tana kallon k'ofar shigowa.

Shi kansa Akmaal lokacin daya koma bed room zama yayi a gefen bed ensa da tunanin wai shin itace matar da Dad yake fad'a ko kuwa wata ce daban..? wata zuciyarce ta tambayeshi "Idan har wata ce daban,to ita kuma wannan me take yi a irin wannan lokacin da wasu gidajenma bara a rasa wanda ko fita sallar asuba basu yi ba.." Shiru yayi lokacin da zuciyarsa ta tabbatar masa da yak'inin lallaifa dolensa ya yarda itance dai wacce yake tsammanin.
Ko ita kanta Unaysa a nata b'angaren tunanin dalilin zamansa a gidan da aka ce gidan mijinta ne take,da dalilin da yasa zata ganshi a irin wannan lokacin,idan har gidan abokinsa ne yazo to me yasa zata ganshi da irin wannan shigan? Tambayoyin da tayi ta yiwa kanta kenan wanda ta rasa wanda zai bata amsansu,daga k'arshe kuma yak'ininta ya tsaya akan lallai ko tantama babu shi ne wanda aka aura mata.

Kimanin kwanaki biyu a tsakani tun daga ranar da suka had'u a corridor basu ko sake had'uwa da junaba.Yau kam tunda ta tashi take fama da wani irin amai a sanadiyyar ciwon ciki daya murd'eta a dalilin zama da yunwan da tayi ta fama da shi a kwana kin da suka gabata,tana kwance a d'aki ita d'aya gashi ko abincin data had'ama kanta a ranar da sunan zata ci ta kasa,murk'ususun ciwo kawai take har ta kaiga ta gangaro daga saman bed en da take kwance,fad'owarta daga kan bed yayi dai² da lokacin daya shigo yana sauri zai wuce bedroom,jin k'aran fad'uwar abu yasa shi dakatawa,bakin k'ofar ya nufa ya murd'a,amma k'ofar sai ya zama a rufe yake ta ciki,d'an saurarawa yayi a bakin gurin da mamakin me yasa k'ofa a kulle kuma baya jin motsin kowa a ciki,shin mene ne ya fad'o haka? rashin amsa da kuma wanda zai tambaya yasa shi juyawa da niyyar wucewa yabar wajen,nan sheshshek'ar kukanta ya sake dakatar da shi,mamakin dalilin kukan da take ya sashi yamutsa fuska can kuma sai ya jiyota cikin murya k'asa² tana fad'in
"Wayyoo..! Allah Mamana dan Allah ki taimakeni mutuwa zanyi,ki yafemin Mamata....Ki yafemin²...!"
Salati ta k'arsasa maganar tata da shi wanda ba k'aramin tsoro ya bawa Akmaal ba,a fili ya furta
"Me kuma ya kawo zancen mutuwa haka..?" tuni wata zuciyar ta bashi amsa da "Ka sani ko bata da lafiya ne yasa take fad'in haka.." da sauri ya shiga knocking k'ofar ni duk a zatonama bai ko san sunanta ba 😢,amma sai ji nayi yana fad'in
"Unaysa..! maza ki bud'e k'ofar nan.."
Shiru ya jiyo babu magana babu kuma motsinta,hakan ya sake tabbarar masa da zatonsa akan lallaifa ba lafiya,sake bubbuga k'ofar yayi yana kiranta amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa,da sauri ya juya ya shige bed room ensa,kusa da bed side drawer ya durk'usa ya shiga janyowa yana dube-dube,can daga k'asa ya hango spare keys en gidan,da sauri ya fizgosu har ya mantama ya maida sauran kayan daya fito dasu ya fice,gwadawa kawai yake da duk wanda yazo hannunsa har Allah ya taimakeshi yazo kan na kusa da k'arshe,yana murd'awa k'ofan na bud'ewa,da sauri ya kunna kansa ciki yana hangen inda zai ganota,bata saman bed haka kuma bai ko ganta a cikin d'akin ba,kiranta ya shiga yi yana kuma sake duddubawa,har toilet ya shiga ya duba amma bata ciki,har ya juya da niyyan ficewa ya hangota can daga space en gado ta d'ago idanunta a kulle ta d'ora kanta a gefen bed en tana maida numfashi a hankali cikin wahala.Saurin nufarta yayi ya d'agota a gurin,sai daya zaunar da ita a gefen bed tukun ya fara jero mata tambayoyin me yake damunta,zamewa tayi zata kwanta yayi saurin rik'eta yana sake maimaita mata tambayar
"Mene ne kuma..?"
Cikinta kawai take iya nuna masa tana runtse idonta ba tare data iya magana ba,baibi ta kanta ba ganin yadda take juyi da halin da take ciki yasa shi saurin kinkimarta yayi waje,a mota ya sata sannan ya shiga ya daidaita zamansa had'e da yiwa motan key suka d'auki hanyan hospital...

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz