Part 15

786 32 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*26/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
_Sak'on gaisuwata gareku masoyana bare tab'a yankewa ba,a kullum ina alfahari da kasancewata tare daku,addu'o'i'nku a kullum suna riskata kuma suna k'ara sani naji walwala,masu yimin sak'o ta PC,Facebook,dama jama'ar cikin groups da a kullum suke bina da addu'o'in fatan alkhairi ina matuk'ar godiya wacce baki bai isa ya k'ayyade ba,ina fatan Allah ya barni daku masoyana ubangiji yasa muna da rabon had'uwa adarus-salaam..♥_
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*73--74.*
_____
_____

°°°°°°°°Da hanzari ko su Ada dake ciki suka fito da son dubawa ko lafiya,kowannesu hannu rik'e da bindiga suna shirin kota kwana,ganin oga a wajen yasa su sauke kan bindigunsu k'asa suka matso suna salute nasa,da k'yar ya iya fitowa a motar,jajayen idanunsa yawatsa musu hak'oransa a datse ya nufo su David cikin masifa yake magana
"Uban waye yace muku ku barta ta fito...?"

"Sir. We are sorry,amma madam da kanta ta bada umarnin a bud'e mata get ta fita..?"

Mari ya d'auke shi da shi yana tambayar wanda ya bud'e mata k'ofan,Ada da yake k'ok'arin bada amsa duk da bashi ya bud'e mata ba shima yaji an d'auke shi da mari,ransa a mugun b'ace ya kallesu duka,hatta da wad'anda ke baya sunyi cirko-cirko
"Mituna biyu na baku kusa guy en can yabar k'ofar gidan nan idan kuma kuka kuskure na sake fitowa na tarar da shi..Uhmmm!."
Ya fad'a had'e da shigewa ciki ba tare daya ko waiwayo ba.
Cikin sauri dukansu suka nufi gurin da Unaysa suke itada Abbas,had'e fuska tayi ganin suna tunkarota,har suka k'araso bata d'auke kanta daga garesu ba,da zuwa David da yake hausarsa tafi ta Ada fita kuma kusan sune gaba ya fara magana
"Malam muna sanar da kai kayi saurin barin nan..."

"Akan wane dalilin kenan kuke magana..?"
Unaysa tayi hanzarin cafke zancen
"Sorry Madam oga ne yace lallai ya tafi daga nan.."
Ranta ne ya kuma b'aci cikin dakiya ta furta
"Bare yiwuba to.."

Shi dai Abbas al'amarin ya d'aure masa kai shin me Guy en yake nufi da cewar ya tafi ya bar k'ofar gidan nasu?.Tunani babu irin wanda bai yiba akan duk ya fahimci abunda ya janyo wannan amma ya kasa gano laifinsa.
Komawa Ada yayi dan ganin sunyi da ita akan ta sallami bak'on nata ita kuma ta kafe akan babu inda bak'onta za shi sai lokacin tafiyarsa yayi,hak'ura suka yi suka kyaleta kan babu yadda suka iya,waya suka danna masa suna sanar da shi abunda ya faru,ransa ko ya sake kaiwa k'ololuwa wajen b'aci take ya basu damar idan ya musu taurin kai su harbe shi,suna ajiye wayar suka koma gurin,suna masu sanar da sak'on ubangidan nasu,ganin sunyi² da Abbas akan ya tafi amma sam ya kafe kamar tsohon babur,yasa suka shiga k'ok'arin aiwatar da umarnin oga akansa tunda sunyi juyin duniya yak'i jinsu musamman ganin zai iya jefasu cikin matsala yasa suka yi amfani da damar da aka basu suka yi harbi..

K'arar harbin daya tashi a lokacin yasa kafatanin y'an aikin gidan tsurewa dan a tunaninsu ko hari aka kawowa gidan basu sani ba,ta window Ummi tayi k'ok'arin lek'owa taga abunda ke faruwa amma sai taga bata iya hango komai,saurin sakkowa tayi nan ko ta tarar da Housemaid duka a parlour sunyi cirko-cirko kamar wasu zakaru,d'an kad'a kai kawai tayi ta fice,hanyan get tayi da sauri da son dubawa taga ko lafiya,ni dai kam nace gaskiya Ummi ba dai jarumta ba,hayaniya ta fara jiyowa a waje wanda daga ji kasan rigima ce akeyi tsakanin guard ensu da wani,muryan Unaysa ta jiyo tana zubawa guard en masifa,ai bata san lokacin data k'arasa fita ba,bata ko bi ba'asi ba ta kamo hannunta suka dawo ciki,babu wanda ta kula duka cikinsu,shima Abbas ganin haka sai kawai ya shiga motarsa ya bar wajen.
Su kansu su Ada bayan tafiyarsa komawa suka yi suna maida maganganu a tsakaninsu da masifa i'junansu,wannan yana laifin wane ne wannan ma yana cewa na wancan ne,da k'yar suma suka samu suka hak'ura da musayar yawun da suke..

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now