Part 4

1.5K 76 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*6/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*______________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
_It's for u *UNAYSA (UNIIYERH)* Gaskiya naji dad'i sosai da ganin sak'onki,ya farantamin ya kuma farantawa y'an uwana,muna matuk'ar godiya sosai,tabbas kinyi amfani da zallar basira wajen tsara sak'on,ina alfahari da samunki matsayin masoyiya ta hak'ik'a,Allah saka miki da mafificin alkhairinsa..Ahabbakillahullaziiy ah'babtaniiy lahu.._
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*15--16.*
_____
_____

°°°°°°°°Ido ta zare waje ganin yadda take jikinta babu komai daga ita sai towel wanda tsayinsa ya tsaya mata iyakar cinyanta,gashi shi kuma ya riga da ya shigo ba tare da neman excuse ba kuma bayan haka ya riga da ya gama ganinta a hakan,k'ank'ame jikinta tayi guri guda kamar wata macijiya ta sunkuyar da kanta k'asa,har ya ajiye abunda ke hannunsa ya juya da niyyar ficewa bata motsaba,tambayar daya cillo mata tasa ta saurin d'agowa tana kallon bayansa jikivna kyarma
"Ina Ummi take...?"
Bata bashi amsa ba haka zalika bata daina kallonsa ba ta baya fuska cike da tsoro,shirun daya ji kuma ya tabbata da ba wai tambayan nasa ne bata jiba yasa shi yin k'wafa had'e da ficewa da sauri yana bangging k'ofar.
K'arar da Mama taji kenan yasa tayi firgigit ta dawo hayyacinta,waige-waige ta shiga yi da son tuna inda take saboda yadda ta tsunduma a wata duniyar ta daban,ganin Unaysa can saman stool tana tab'e-tab'e yasa ta saurin tashi tana nufarta,hannunta ta rik'o ta janyota suka koma can bakin bed da take zaune
"Yawwa Mamata kinga na kasa taje gashina dan Allah taimakon nan da kika saba zakimin.."
'Dan murmushi mama tayi tana fad'in
"Dama ai ba abunda kika iya kullum sai dai ayi miki,tsifama ta gagare ki bare kuma tazar kai..Ammmm..! Kin san me zan fad'a miki...?"
Da sauri Unaysa ta shiga girgiza mata kai alamun bata sani ba har sai ta sanar da ita
"Yawwa Autar Mama,abunda nake son ki sani yanzun shi ne,kinga dai nan ba gidanmu bane ko..? to abunda nake sonki da shi shine komai zaki gani bana son ki k'ara tab'awa har sai an miki izini,a matsayinmu na masu aiki dole ne mu kiyaye da duk wasu abu da basu danganci masu aiki ba,haka zalika sai mun rik'e talaucinmu,Allah shi ya k'addara mana yin wannan irin rayuwar fatana shi ne mu yi hak'uri har zuwa lokacin da Allah zai yaye mana ya kawo mana rangwame a cikin al'amuranmu,kin fahimce ni ai ko..?"
Nanma kai ta d'aga mata jikinta a sanyaye,har mama zata ci gaba da magana Unaysa ta dakatar da ita da fad'in
"Mama to wai mu me yasa da Abbana ya mutu muka zauna a nan..? Kuma da Baffa ya wulak'antamu ba sai mu tafi danginki ba.? Kinga dai duk lokacin da nai miki wannan tambayar Mama bana samun amsa daga gareki me yasa Mamana bara ki fad'amin ba..? Na sani kowane mutum yana tashi ne a tsakanin dangi biyu,dangin mahaifi da da kuma dangin mahaifiya,to amma Mama me yasa ni na kasance mai dangi d'aya duk da suma ba wani yawa gare suba,ko sau d'aya baki tab'a gwadamin danginki ba,ina danginki suke Mama...? Dan Allah Mamana ki sanar dani inda suke ko ba a k'asar nan suke ba,wata rana idan Allah ya azurtamu sai mu ziyarce su..!"
Shiru Mama tayi,cikin y'an mintuna da yi mata tambayar idanunta sun cika taf da ruwan hawaye,ganin yanayin data shiga yasa Unaysa marairaicewa hawaye har sun fara gangarowa ta rik'o hannun Mama tana sake fad'in
"Ki yafemin Mahaifiyata,ko kad'an bana son ganin abunda zai saki shiga yanayin damuwa,gashi a dalilin tambayata har kina shirin zubar da hawayenki,dan Allah ki yafemin,idan har a dalilin tambayar dana mikine in sha Allah haka bare sake faruwa ba,daga yau ban k'ara tambayar inda danginki suke in dai har bake kika so sanar dani ba na hak'ura da jin asalinki in Allah ya yarda..."
Tana fad'in haka ta mik'e zata bar kusa da mama,da sauri ta rik'o hannunta ta dawo da ita tana mayar da kanta bisa cinyarta data d'auke shi a kai
"Ko kad'an Unaysa bakimin laifin komai ba bisa tambayar da kika yi,hasalima a koda yaushe inajin kunyarki a duk lokacin da kika tambaye ni dangina ban baki amsa ba,sai dai hakan nima ba laifina bane daya zama bani da dangi.."
Sake saurin tashi tayi tana kallon mahaifiyarta idanunta a waje saboda tsoro daya kamata,cikin zuciyarta take maimaita "Kamar yaya kenan baki da dangi Mahaifiyata..?"
Kamar mama tasan abunda Unsysa ke sak'awa a ranta,bayan ta goge hawayen da suka sakko mata ta furta
"Tabbas..! abunda na fad'a babu k'arya a cikinsa,ni da kike gani ba kowa bace,haka kuma bani da kowa,na tashi ni kad'ai,haka kuma na tashi na ganni ina rayuwa a tsakanin wasu al'umma irina marasa dangi da asali.."

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDKde žijí příběhy. Začni objevovat