Part 24

1.3K 42 0
                                    

*AWESOME WRITER'S ASSO🏮*
~_(Palace of excitation & pleasant writer's)_~
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*1/March.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/Smasher&HubbeeyNovelsGroup/369678263526212/
___________________________
_The hole page is ur's Asma'u Sanee (Asmerhluv) marubuciyar *NA TSANE SHI..!!* ('DAN ISKA NE) ke in ta daban ce a gurina dama zuciyata,ina godiya tare da jinjina gare ki,fatan Allah ya bar zumunci da k'auna._
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*123--124.*
________
________

°°°°°°°°Kallonsa taci gaba da yi tana nazarin abunda yake shirin yi,a hankali cikin nutsuwarta ta dawo ta tsaya a gefensa tana fad'in
"Me kake nufi ne wai Yaya..?"

"Oho!! Nima ban sani ba amma ki tambayi kanki.."

"Uhmmm! Wato tunanin kafa wai ciki ne dani ko??"
Kai ya girgiza mata cikin dariyar mugunta
"A'a ni ban fad'a miki haka ba amma dai ki tambayi kanki koma mene dake.."

"To idan ba haka kake nufi ba mene nufinka da kake latsamin ciki d'azun..? Ai ni dama tunda naga kana yawan kallona nasan abunda zaka ce kenan,amma tunda baka yarda ba bani da komai zaka iya aunawa sai ka tabbatar.."
Ta k'arshe maganar tana murgud'a masa baki,juyawa tayi tana niyyan guduwa ganin ya mik'e tsaye,ko me ta tuna kuma tayi saurin tsayawa tana dakatar da shi fuska a tsuke
"Allah Yaya baraka sani inata binka akan kaci abinci kana guduwa ba,ni ban san me yasa yau duk ka kasa nutsuwa ba,ko akwai wani matsalan da baka sanar minba..?"
Kasak'e yayi yana kallon ta har ta dasa aya,cikin sigar lallashi ya kalleta yana fad'in
"Afuwan uwar gidanah..!"
Wata uwar harara data maka masa yasa shi saurin rufe baki
"Kana da wata matar ne bayan ni da kake kirana uwar gida..?"

"Kika sani ko zanyi nan gaba.."

"Allah koh..?"

"Sosai ma,ko bakya so nayi ne..?"

"A'a ni na isa na hanaka bayan dama ka samu da zaka iya auran fiye da d'ayan,idan kaga kana da halin yin k'wark'wara ma duk kayi kud'inka..!"
Yadda take magana tana basarwa yasa shi yin murmushi
"Shi kenan ma kinga kin kawo shawara,amma dai k'wark'warar a barta,nayi hud'un ma sun isa.."

"Ni kuwa baka burgeni ba in dai har baka k'ara da k'wark'wara ba.."
Tsar ya fahimci abunda yake damunta,maimakon yayi shiru haka sai cewa yayi
"Da gaske kike..?"

"Sosai ma kuwa.."

"Uhmmm! Bari to na gani ko da gaske kike zaki iya barina na k'ara auren ma,kafin a kaiga maganar k'wark'warar."
Tsare shi tayi da idanunta kafin ya k'araso ta juya da sauri zata bar wajen,saurin rik'o ta yayi yana jifanta da wani birkitaccen kallo
"Kina son kiyi mana asara ne kike niyyan yin gudu..?"

"Nifa Yaya ban ce maka ina da.."
Yatsansa ya d'ora akan lips enta yana girgiza mata kai
"Na yarda baki da shi,shi kenan maganar ta wuce..?"

"Ehhh!"

"Muje to ki bani abincin yanzun ina jin yunwa sosai.."
Fuskarsa ta shafa tana lumshe ido
"Ai duk laifinka ne dama tun d'azun sai fama nake dakai kaci kana k'i kamar wani k'aramin Yaro.."
Y'ar dariya yayi yana sumbatar forehead enta
"Ni yaro ne mana amma a gurin ki.."

"Uhmmm! Jariri nema kai.."

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now