Part 10

1.1K 56 0
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*14/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
_Gaisuwa,jinjinar ban girma tare da fatan alkhairi gareku *Writer's* na group en *Smasher & Hubbeey 1&2,Zab'in wa zanbi Fan's,Comments Only* Allah saka muku da mafificin alkhairi,a kullum kuna aiki tuk'uru ba don komai ba sai don ku farantawa masoyanku,hak'ik'a kun cancanci girmamawa da mutuntawa,rabb yayi muku sakamako da mafificin alkhairi a nan duniya da lahira.._
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*43--44.*
_____
_____

°°°°°°°°'Dan murmushi Ummi tayi tana zaro photon daga jikin inda yake mak'ale ta mik'awa Mama,Unaysa ma kusa da Mama ta koma tana lek'awa,fuskarta da mamakin ganin wannan photon.
"Wannan da kike gani kika tsammanci ke ce,ko kad'an baki santa ba,haka itama bana jin tasan ki,kawai dai halittar Allah ce yasa kukayi tsananin kama da juna ba tare da had'a alak'a da junan kuba.
Wannan itace *RUMANA* mahaifiyarsu Akmaal..!"
Dumm! k'irjin Unaysa ya bada sautin da sai da tayi hanzarin dafewa saboda firgitar da tayi da jin sunansa haka kawai.
"Tabbas idan baki manta ba a waccan ranar da muka had'u dake idan har zaki iya tuna yanayina zaki gano mamakin da nake dana ganki,sai dai kawai na b'oye ne badon komai ba sai don idan har na bari kika gano hakan zaki iya k'in yarda dani,a lokacin maganar da kikamin ta shin ina neman y'ar aiki ne!? ita ta sake bani k'warin guiwar tahowa daku badon komai ba sai don wani tunani da nayi a lokacin game da rashin lafiyar d'an uwana,wollahi tun a lokacin naji baran iya barinki ki kufcemin ba saboda na hangi nasara acikin zaman da zamu yi daku,tabbas idan har na kawoki gidan nan,matuk'ar d'an uwana zai yi arba dake ina kyautata zaton zai iya tashi daga wannan jinyar,haka ko da kika sanar dani akwai yarinyarki da zaki d'auko zuwa gobe sai ku zo gida ku same ni ai kinga ban baki wannan damar ba ko..? to wollahi lokacin zuciya tace tak'i nutsuwa gani nake kamar idan kika tafi baran sake samun damar ganinki ba shi yasa nayi ta miki naci har kika yarda kika biyoni muka je inda kika bar Unaysa,daga nan kuma muka kamo hanyar tahowa..Nasan dai wannan ya faru kuma kema kin shaida da abunda ya faru tsakaninmu a waccan ranar,sai dai baki san dalilin da yasa na d'auko kuba,kawai dai abunda nasan zaki iya tunawa shine nace miki zaki dunga tayani jinyar d'an uwana amma bayan wannan baki san komai ba.."
Shiru duka suka yi har lokacin mama sai juya photon hannunta take,haka kuma har lokacin bata gama gasgata ba itace a jikin photon ba sai dai kawai abunda tafi yarda dashi shi ne take kuma tunawa yadda ta rayu a gidan marayu,da yadda suka iske Alhaji Abdullah a d'akinsa,tabbas lokacin daya farka sunan Rumana ya kirata da shi,wannan tunanin shi ya sake bata damar gane cewar suna tsananin kama ne kawai,dogon numfashi ta sauke kana ta mik'awa Hajiyar photon tana fad'in
"Allah ya kyauta..!"
Kallon rashin fahimta suka mata daga Ummi har Unaysa,ita ko bata wani bi takansu ba ta mik'e,ganin haka yasa duk suma suka mik'e Unaysa cikin raunin zuciya ta kalli Mama
"Mama dan girman Allah kiyi hak'uri,kada kice zaki tafi a karo na biyu bayan sanin gaskiya,kadafa ki manta ke mahaifiyata ce kin nunamin jin tausayi abune mai kyau haka taimakon wanda yake cikin tsananin buk'ata,kina da damar da zaki yi amfani da ita ki fidda wannan bawan Allah daga cikin k'angin wahalar da yake fama da ita har na tsawon lokaci,kada kiyi haka ya mahaifiyata idan har kika juya baya akan taimako bayan Allah ya baki iko to ki sani ubangiji zai iya jarrabarki da abunda bai jarrabi bawansa da shiba,shin ya kike tsammani a lokacin da kema wani da yake da ikon taimaka miki ya juya baya ba tare da tausaya miki ba..? Kwatankwacin abunda zaki ji a lokacin haka shima wannan bawan Allah'n zaiji idan har kika tafi..Kiyimin afuwa mahaifiyata idan har na fad'i wani abu daya b'ata miki,banyi da nufi ba sai don na tunatar dake abunda zuciyarki ke shirin sawa ki aikata na ba dai² ba.."
Kanta ta sauke k'asa bayan ta gama maganar hannayenta sark'e cikin juna tana murza yatsunta da jiran jin hukuncin da Mama zata yanke musu,shin zata bata umarni ne akan su tafi ko kuwa zasu tsaya ne don taimakawar...?

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWhere stories live. Discover now