Part 14

972 32 0
                                    

 💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*24/Jan.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*67--68.*
_____
_____

°°°°°°°°Waya ne k'irar Ipone 7+ a ciki,juya wayan tayi ta faman yi a hannunta tana mamakin dalilin da yasa ya aikata haka,tashi tayı bayan ta tattara komai ta maida cikin kwalin kana ta nufi sama.
Cikin closet ta yiwa kwalin gurin zama,har ta juya zata bar wajen sak'on dake cikin y'ar wasik'ar ya fad'o mata,tsayawa tayi kad'an sannan ta sake fitowa da shi,wayan kad'ai ta iya fiddowa da duk wani tarkacenta sannan ta bar wajen,had'a komai tayi a lokacin sannan ta kunnata,kamar dama jira ake ko ansan da zata sa sim enta kiran ya shigo,kallon screen en ta tsaya na wucin gadi sannan tayi picking,wanda take tsammanin dai shi en ne cikin mutunci suka gaisa da shi sannan tayi shiru,shi enma shirun yayi yana tunanin ta inda zai fara janyo zaren,da k'yar yayi y'ar gyaran murya sannan ya soma da fad'in
"Ammm! Ello..!"

"Uhumm!"
Shiru yayi yana tunani wato dai kenan hakan ya nuna tana saurarensa,sake gyaran murya yayi sannan ya ci gaba da magana
"Amm! Afuwan Ma'am nasan ranki ya b'aci da abunda na aikata ba tare da neman shawaranki ba na yanke hukunci,amma dan Allah ina son kiyi min kyakykyawan fahimta,wannan abun daya faru ya riga da ya faru kuma ko kad'an banyi tunanin ranki zai b'aci ba coz a tunanina hakan ba wani abu bane da har za'a damu,beside ma banyi da nufin cin fuska gareki ba,coz nasan kinfi k'arfin haka,nd ina so ki d'auki wannan a matsayin kyauta ta farko data fito daga gare ni,shin kinsan irin yanayin dana tsinci kaina a lokacin da Fadeela take sanarmin da baki ji dad'in abunda nayi ba..? Mene amfanin soyayya idan har babu kyautatawa..? Nasan kin sani amma zan sake tunatar dake abunda addininmu ya koyar damu,kamar yadda Annabi (S.A.W) yace a hadith:-"Kuyi kyauta sai a soku,domin kuwa yin kyautar yana tafiyar da k'iyayya.." Shin dan na miki d'an wannan abun shi ne abun damuwa..? Ina so ki lissafa da kanki idan har babu kyautatawa tsakaninmu bama ace iya mu kad'ai ba ki hasaso wasu daban can,shin soyayya ko wani shak'uwa zata samu kuwa..? To kamar hakane garemu,nd kuma ni ina d'aukan duk wani namiji marowaci a matsayin baisan kansanba,ya kamata ki fahimci dalilina nayin haka bawai saina yi miki fashin bak'i ba,ina fatan kin fahimta.."
Dogon ajiyar zuciya ta saki,cikin sanyin murya ta furta
"Shi kenan na gode sosai da tunatarwa,na kuma gode da alkhairinka gareni,Allah saka da alkhairi.."

"Shhiiiii! Ma'am ya isa haka,wannan godiyar duka name ne? ina tunanin idan nayi miki wani abu nan gaba bana so kici gaba damin irin wannan godiyan,wani idan yajiki kina irin wannan ai sai yayi zaton wani gagarumin abu akayi miki,stop it pleaseeee..!"

'Dan murmushi ta saki sannan ta furta
"As u wish ur excellency..!"
Dariya sosai duka suka saki
"Wato Ma'am kin iya zolaya kemafa,amma dai shi kenan idan har ni na zama Excellency,what will u be..?"

"Ehmm! Bari muga mema zan zama ne..? Yess! Ur P.A.."

"Whatt....P.A kuma Allah rufa asiri,a time en kam ai sai dai a kiraki da.....?"
Saurin katseshi tayi ta hanyar
"Nifa da gaske matsayin P.A zan zauna.Kuma kaima nasan saika yarda dani idan ka gano abunda nake nufi.."

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDWo Geschichten leben. Entdecke jetzt