page6

522 22 0
                                    

🌹A Sanadin Auren zumunci🌹

Story and written by ayshat Yusuf

Dedicated to surayyahms catty🐈

Wattpad @yusufayshat0

INA mai taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki Allah swt ya karo shekaru masu albarka

Happy birthday my besty fareeat

Joyeux aniversaire riamed

Sorry for the late wishes
             
           Page6

Ai koh dai tsafi gaskiyar mai shi dan asirin da hafsy taiwa ummi ya Kama Dan tu ranar da suka dawo daga gidan malam bata sake yi mata maganar aure ba Dan haka ta Kara shagala da duniya ta ke cin karenta ba babbaka

Tundaga wannan ranar ahmed ya mayar da jameela tamkar matarsa ta sunna kullun takan fake da lkcin islamiya suje su sha bidirinsu kyauta kuma ba irin wadda baya mata dan ita kanta abun yana bata tsoro wasu lokuttan

Shikuma ahmed ba komai yasa ya nace mata ba sai dan soboda ni'imar da Allah ya mata ga kuma tsumata da latifa keyi tunda taji ta shiga sahun su a tarihinsa ita ce mace ta farko daya raba da budurcinta kuma ya cigaba da tarayya da ita

Bayan sun dawo daga Yola ashraf ya cigaba da rayuwarsa cikin kwanciyar hankali da aminci sai dai abu daya ya hanasa sakat shine tunanin hafsat  da yake fama da shi tun ranar da ya kaita gidansu

A cikin satinan ne aka je neman aure gidansu rukayya inda komai yayi dai dai an saka rana two months kuma za'a Kai lefe aure saura three weeks

Sati me kamawa suke tunanin zuwa kano dan maganar auren dayan gogan wanda bai san ba ma wainar da suke toyawa a tunaninsa an bar maganarsa ne tunda har anje neman aure moctar amma abbu bai masa maganar aure ba shiyasa ya saki jikinsa yake harkokinsa ba tare da fargaba ba

Yau su abbu suka sauka a kano Kai tsaye gidan malam aliyu suka sauka sun samu tarba me kyau dan ansan da zuwansu sai dai banda malam da limamin unguwar wanda ya Kira dan ya tayashi bada auren da wanda ya san me ya kawosu gidan

Su umma sai washe baki ake anyi  baki masu kudi

lkc da aka basu a gidansu rukayya shi suka tsayar anan din ma dan abun ya tafi cikin tsari

An bada komai wanda yake dukiyar aure banda lefe Wanda za'a kawo daga baya

Tayi nasarar rufe bakin ummi dan haka da taga alhaji ma'aruf zai dawo kasar shima taje aka rufe me baki ko daya dawo bashida yancin mata magana Dan haka duniya ta dawo Mata sabuwa shashanci kuma sai abunda yayi gaba amma har yau tana nan da halinta na tausayi da rashin kymar na kasa da ita

Wannan halayen nata su suke lulube wancan dayan halinta Wanda daga kawayen shashancin ta sai mahaliccin ta suka San da shi sai dai kuma may be may  a gaba wani ko wata su sani dan ance rana dubu ta barawo rana daya ta mai Kaya

Yanzu kam basu da wata matsala a rayuwarsu sai ta saduwa da ya ke son yi da ita ta baya sai dai taki amince masa wannan shine kaway abun da ya ke gama su rigima na yan awanni dan daga anjima inya ji sha'awar shi ta motsa ya nemeta dan yaka fadan nasu baya dadewa

Da zasu tafi abbu ya sa aka kiramasa jameela ya yaba da nitsuwarta gaskiya dan kudin daya bata ma kin karba tayi saida ya matsa mata
Hakan yasa abbu ya koma gida cike da yakinin cewa ya zabo ma danshi matar aure ta nuna ma sa'a

Bayan sun tafi ne abba ya kirasu ya sanar dasu makasudin zauwarsu

Cikin tashin hankali jameela ta mike daga tsugunawar da tayi ta fasa kara wlhy ni  Abba bana son shi ko shi waye ni Ahmed zan aura ta fashe da kuka kamar  wadda ake  yankawa

Cike da takaici suke kallon ta tun bama Umma ba datake ganin zata mata sanadiyar rashin arziki dan tunda Abba ya sanar da su cewa ambassador ne taji ina ma yace yana san jameelar gashi kuma Allah ya amshi rokonta tunda danshi yazo nemawa sure

Abba ne ya kalleta cike da bacin rai to baki isa ba ki sani jin kunya ba a ce yar dana haifa ta kasa mun biyya don haka aure ashraf ya zame miki dole kuma ke kika San wani Ahmed ni ban San shi ba dan haka ko sunan sa karki sake ambata min a gida

Wani kuka ta kara fashewa da shi ta mike ta Shiga daki

Tsaki abba yayi ya fice ya bar gidan dan bazai iya kallon wannan kayan takaicin ba

Umma ce ta Shiga balbale ta da masifa to uwar yan bakin ciki daga maganar arziki kuma sai ki hau kuka yarinya Allah ya yanke  ya baki miji mai arziki amma ki tsaya kina kuka to dan ubanki aleeyu aure nan ba fashi sai kin aure sa muma mu ci arziki shashasha kawai

Shi kuma ashraf bayan sun dawo ne abbu yake sanar dashi batun auren yaji Dan shock saboda abun yazo masa a bazata Dan shi a zatonsa an rufe wannan babin sai dai ya ma kansa alkawari karbar wannan auren da hannu biyu dan ya san hakan na daga cikin abun da Allah ya tsara masa

Ammy ma ko da taji wannan maganar tayi matukar farin ciki ashraf zaiyi aure kuma matar ta fito ne daga gidan nagartaccen mutum irin malam aleeyu dan haka ta Shiga hada musu lefe da shi da moctar wadda duk rabin kayan a online ta siyesu

Gaskiya amare sun zama yan gata dan a gidan su moctar ma momynsa ta yada musu lefe na gani na fa komai ya ji abun kam sai dai ace masha Allah ....

Kuyi hakuri da wannan

Kuyi hakuri da yanda littafin yake tafiya wannan karon abubuwa ne sukay min yawa

#vote
#comment
#share

a sanadin auren zumunciWhere stories live. Discover now