page9

429 16 0
                                    

🌹A Sanadin Auren Zumunci🌹

Story by ayshat Yusuf

Dedicated to surayyahms catty🐈

Follow@yusufayshat0

Allah ubangiji ya kawo sauki surayyahms ya sa kafara ce

Ina bukatar addu'ar ku dan cuta ta kuma dawo sabuwa

Yau page din karami ne dan jikin ya kiya ku biyoni bashi gobe insha Ar-rahman
             
                 Page9

Haka dai abubuwa suka cigaba da faruwa inda yau saura sati daya biki kuma a yau ne za akai lefe gidajen amare

Bagaren jameela tun maganar da sukayi da lateefa bata kuma nuna kin auren a fili ba sai dai ta ciki na ciki hankan da tayi yama su abba dadi dan su a zantansu ta hakura ne

Koda ahmed yaji zancen auren kiranta yayi ya gaya mata maganganu masu zafi way ta ci amanar sa

Hakuri ta rika bashi tare da shedamasa auren na dan lkc ne dan zuciyarta ba wanda take so sai shi
Da haka dai ta shawo kansa suka cigaba da sayayyar su mai cike da sabawa mahaliccin su

Ta bangaren ashraf ma batun ba sauki dan har yanzu ya rasa yanda zaiyi da sayayyar hafsat dake faman kaisa rami ga kuma auren da'ake shirin daura masa ba tare da yasan halin matar ba

Ya rame yayi baki dan tun moctar na masa tsiya har ya koma yana lallashin shi

An kawo lefe kaya ne nan gani na fada dan ko wace amarya lefe seet biyu ta samu ga na ammy ga kuma na mami moctar

Aiko kuri ya karu wajen Umma gani wanan lefe dan harda makullin mota abbu ya hada  ma ko wacce a cikinsu

Ko jameela da taga lefe sai da ta girgiza duban lateefa tayi tare da cewa way besty harda mota naji an kawo fah

Gyda kay latee cike da alamun tabbatarwa ta ce kwarai koh kinga yanzu muma mun faso gari sai dai da yanzu kin mana bakin cikin samun wannan daular ga zaman Abuja ga kuma mota

Jameela ta amshe da cewa sai dai ba soyayya ba dariya suka sa tare da tabawa kamar Wanda aka ce da su an yafe musu zunuban su

Washe gari yau ne ammy tace da su su zo kanon dan jin events din da amarya zata yi da yawan kudin da take bukata

Bada son ran ashraf ba suka kamo hanya dan dai ba yanda zai iya ne kaway

Bayan sun isa hotel suka kama dan lkc dare ya fara yi sai washe garin ranar da misalin karfe biyar na yamma suka je gidan

An riga da an san da zuwansu dan yaka an shirya musu abinci da su juice wanda duk shawarar lateefa dan jameela cewa tayi ba ruwanta dan lkcn da latee ke girki ita tana daki tana waya da habibynta ahmed

Yaro suka samu yayi musu iso cikin gidan
A falon abba suka zauna inda ashraf yake danna wayar sa ko kallon ruwa da juice da ke ajiye be yi ba sai moctar ne ya sha

Ba abinda ya ke so ya gani sai yarinyar da abbu ya zaba masa a matsayin matar auren sa dan yana son yasan wasu abubuwa ne tattare da ita har abbu ya ke so ta zama daya daga cikin zuri'arsa

Sai da sukayi kamar minti goma a zaune kafin suji sallamar lateefa don jameela kam KO arzikin sallama basu samu daga gareta ba

Jin kamashin turaren da aka ma sawar haramun a matsayinsu na mata yasa shi dagowa dan ganin su waye da wannan aikin

Ganin su yayi zaune sun wani hakimce kamar wasu matan shugaban kasa ido ya kawar daga kallon su ya cigaba da danna wayarsa

Lateefa ce suka shiga gaisawa da moctar har yana tambaya Ina amaryarsu jibmn haka yasa jamila ta gane cewa bashi bane ango dan yaka ta gaishe shi
Tsokanarta ya shiga yi ita kuma tana basarwa

Ganin cewa ba Wanda yake da niyar wa dan uwansa magana yasa motar yaja latifa sukayi wake tana ad'du'ar Allah yasa itama moctar ya ce yana sonta dan taya alamun shima dukiya ne

#vote
#comment
#share




a sanadin auren zumunciWhere stories live. Discover now