🌹A Sanadin Auren Zumunci🌹
Story by ayshat Yusuf
Dedicated to surayyahms catty🐈
Follow@yusufayshat0
Page15
Zaune take akan wata bola sai famar tsintar ledoji take tana wasu surutai marasa ma'ana
Wata mata ce wacce a shekaru bazata fi shekara arba'in ba ta nufo bolar nan tana sharar kwalla ta Kama yarinyar tana fadin haba nuwailat ba said Dana hanaki futa ba yanzu meye anfanin zaman da kike a nan
KO daga Kai yarinyar da aka Kira da nuwailat batayi ba bare ta Nuna alamar ita akewa magana
Cigaba da tsintar ledojinta tayi ganin bazata daina abun a take ne yasa matar nan zauwa ta Kama hannunta da nufin futar da ita daga wajen
Tirjewa ta shiga yi sai dai ganin alamun Bazata samu nasarar komawa ba yasa ta nutsu suka Shiga tafiya still matar na rike da hannuntaWani dankareran gida naga sun Shiga wanda daga mutum yaga fasalin gidan gidan zai shaida cewa turawa be suka gina shi
Washe garin ranar ma hakan ce takasance a gidan ash dan tun asuba da jamila ta tashi sallah ta girka breakfast dai dai cikin ta ta sa a daki
Ranshi a bace ya futa daga gidan dan wata irin yunwa yake ji sakamakon dinner dabe ci ba jiya daddare dole ya fuce restaurant dan gudun kar ammy ta zargi wani abu
Bangaren hafsat kuma yan kwanakin nan tana cikin fargaba dan cikin satin yaya Mahmud din data cema goggo suna soyayya zai dawo dan dama wajen kwantar da tarzoma aka tura su kuma alhamdulillah sunyi nasara shiyasa aka yanke dawowar tasu cikin satin
Duk tabi ta damu dan yanzu babu abun da ta tsana kamar Kalmar aure auren ma nata a Nata tunanin babu abunda namiji zai mata Wanda yar uwarta mace bata mata ba a nata fahimtar maccen ma tafi namijin experience akan wanan harkar(wa iyazubillah)
Wani dan bq motar ta nufa da yarinyar Masha Allah duk da babu wasu kaya masu yawa a falon ya tsaru fiye da tunanin mai karatu komai na cikin falon blue ne sai ratsin white
Yayinda bedroom din shikuma yake red and white komai net babu wani alamu dazai maka cewa Mazauna wanan muhalli kazamai Ne
Kai tsaye toilet din dake cikin bedroom Wanda shima cike da tsapta matar ta kaita wanna ta mata sanan ta wanke mata gashin kanta Wanda gani daya zaka masa kasan ta hada iri da Fulani koh buzaye
Said da ta gama shiryata ta kwantar da ita a dan madaidaicin bed din dake dakin ta kashe fitila ta fuce zuwa ainayin cikin gidan tana share hawaye
Ba'a wani bata lkc ba bacci yayi gaba da ita
Kwana biyu kun jini shiru hidima ce tai min yawa yau ma kadan kuka samu
#vote
#comment
#share
YOU ARE READING
a sanadin auren zumunci
Adventurelabari mai cike da tausayi soyayya zalumci da sauransu ...