🌹A Sanadin Auren Zumunci🌹
Story by ayshat Yusuf
Dedicated to surayyahms catty🐈
Follow @yusufayshat0
Jiki yayi sauki alhamdulillah ina godiya da kaunarku a gareni
Page8
Saida ya gama aiki da yake ya dago ya dubi moctar tare da fadin inka shirya tafiya sai ka tashi mu fice indan kuma anan zaka kwana kuma ruwanka ya fice daga office din bayan ya dauki jakar laptop dinsa
Ganin zai rufesa a cikin office din yasa moctar fuce da gaggawa
Gurin inda ya parking din motarsa ya nufa ya futo da wani abu kamar kusa ya nufi motar ashraf
Sai da ya leka yaga bai kai ga fitowa ba ya caka masa abun a tayarar mota
Aiko cikin dan lokaci tayar tayi kasa alamun babu iska a cikin
Wajan motarsa ya nufa ya Shiga ya rufe bai tayar da motar ba sai da ya ga ashraf din ya fito yayi wani murmushin mugunta ya Kara gyra zama dan yasan dole ashraf ya masa magana wannan Karon
Ko da ya fito motarsa ya nufa ba tare da ya kalli inda motar yayi parking ba duk da yasan jiransa yake dan duk lkcin da dayan su ya kaima dan uwansa ziyara tare suke komawa gida sai dai a bar dayar motar a office
Yaje bude kofar motar ne ya lura da tayar motarsa da aka sace babu alamun iska a ciki lips dinsa na kasa ya cije dan yasan wanan aikin moctar ne yayi dan ya masa magana
Ko da lateefa ta isa gidan umma ta iske a cakar gida tana shan shayi ya sha milo da madara wanda ta saya a cikin kudin da abbu ya ba jameela jiya
Gaisheta har ta tashi dan zuwa wajen aminiyarta tata umma ta tsaida ta da cewa ki dai jawa kawarki kunne dan jiya an kawo kudin aurenta tana ikirarin bata so to in ma bakincinkin cin arziki take min ki ja mata kunne dan aure kamar anyi an gama ehe
Insha Allah umma zan mata magana bazata kara maganar kin auren ba yanzu ma matsala kawai aka samu
To kidai fada mata ko ma neye akanta ta sauke shi dan arzikin da bata sona da shi sai nayi
tayi ta shige dakin jameelar Ba tare da tabi takan Umma dake ta maganganu ba
Tarar da ita tayi zaune akan gado ta jingina da bangon dakin da ganinta kasan tayi nisa cikin duniyar tunanin
Tabata da taji anyi ne ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi gannin latifa ce yasa ta sauke wata ajiyar zuciya
Zama latifa tayi ta dafa ta tare da cewa haba jamee irin wannan zurfafa tunanin yaka akan da karamin abu har kije ki jawa kanki wata cuta
Cike da mamaki take kallon latifa karamin abu fa kika ce soyayyar ahmed fa nake shirin rasawa amma kike kiran haka da karamin abun gaskiya ki dena bana so
Ai nake ga kamar gaski...katse ta jameela tayi da cewa ki rike gaskiyar ki inde kakan wannan lamarin ne yanzu dai wace mafita kika samo mana
To mafita dai daya ce ita kuma nasan bazaki yarda da ita ba
Ai inde akan wannan lamarin ne komai ma zan iya yi dan kadda a daura auren fadi kaway ina ji
Ko da hafsat ta baro gidan kakartata gidan anty nuseiba ta fice ta isketa a falo tana zaune gaisheta tayi cike da ladabi ta fuce dakin nuseibar
Kallo mai cike da tausayi anty halima ta bita da shi tasan cewa kanwartata tana neman mata sai dai bata iya mata magana kuma bata iya fada wa kowa tausayin hafsat take ji yarinya mai cike da kamala da kuma tarbiya tana jin tsoro karda watara na tazo Wanda itama zata lalace tunda tana kawance da nuseiba dan ita anty bata San aikin gama ha riga daya gama ba
Ta tarar da ita tana kallon wani bf a waya tana ganin hafsat ta rugumota suka cigaba da kallon tare da aka jima kuma suka shiga shafar jikin junan su har suka Kai ga aikata sabo
Bayan sun dawo nitsuwar su sunyi wanna hafsat ta shiga fada mata yanda sukayi da kakar tata shewa suka dauka nusee tace lalle kawata kina wuta
Dariya hafsat tayi tace kinga kafin Yaya Mahmud ya dawo naci kare na ba babbaka tunda shekara biyu zaiyi kuma gwaggo tace bazata sanar da shi ba bare ma asiri na ya tonu
Dariya suka kara sakawa sai kuma suka shiga hirar test din da za suyi gobe
Ganin babu yanda zai iya ya sa ya nufi motar motar hannun yasa zai bude gefen mai zama banza yaji a kulle ta window ya leka cike da rashin son magana yace malam ka bude min mota in shiga tunda ka mun barna dan ya san inba magana yayi ba zasu kwana a wajen dan moctar baze iya tafiya ya barshi ba kuma baze bude ba sai yayi magana
Ganin ya ci nasarar saka shi magana ya motar ya budemasa mota fuskar sa dauke da murmushi suka bar harabar hospital din
Haka suka isa gida ba wanda yake magana sai kira'ar sudais dake tashi hakan yasa ashraf yadan samu nitsuwa akan damuwar da yake ciki
Bayan sunyi wanka suka nufi bangaren ammy inda suka dameta da tsokana har akayi kiran sallah suka je masallaci tare da abbu saida akayi isha'i suka dawo sukayi dinner basu jima a part din su ammy ba suka je nasu part
Shirin bacci sukayi saida suka hau gado moctar ya kuma tanbayarsa akan damuwarsa
Wannan karon bay wani boye masa ba ya sanar da shi abunda yake faruwa da shi akan lamarinsa
Tausayinsa ne ya Kama moctar ganin saida lkc ya kure ma aminin nasa tunkun ya samo mace da yake so dan abbu kaifi daya ne bazai harda ba a fasa wannan auren daya hada ba saboda sai da ya basa zabi da farko
sai dai a fuska bai nuna hakan ba sai ya kwashe da dariya yana nuna ashraf yaba mana aboki ya zaka karaya da wuri bayan ka kasance mutun ne kai da bai GASKATA SO Ba(my next novel insha Allah)dan in ban manta ba zulfa ma ita ta kawo kanta gareka kai kuma kullun ikirarinka shine baka sonta saboda halayenta ne kake kulata dan a lkcin ka zaci mutumniyar kirki ce sanan baka da maganar fadi kullun sai na cewa soyayya shirme ce ya kara fashewa da wata dariya mai cin rai
Duk maganganun da moctar ya fada yasan tabasss anyi haka sai dai a hanzu dai dai lokacin da sayayyar hafsat tai masa mugun kamu yayi nadamar furta waddanan kalaman
Ganin dayayi moctar bazai fasa masa dariya ba ne ya sashi kashe gloves ya ja blanket ya rufa
Ganin yaka yasa motar shima ya kwanta
Shawarar ba wata bace face ta zuwa wajen boka mai....
Bata karasa ba jameela ta katse ta da cewa haba ya zaki kamun zancen zuwa wajen boka dan duk abuna bazanyi shirka ba dan yaka ki canza wata shawarar
Nisawa nusee tayi to in day ba wanan ba sai day ki bari har ayi auren sai ki rada mata wata magana nusee ta fada mata sai naga tana gyda Kai cike da gamsuwa da shawarar da nusee ta fada amma fah sai kin daina nuna kymar auren nan dan gudun zargi
To shikenan zan gwada in gani nan suka cigaba da tattaunawa akan batun auren
#Vote
#Comment
#Share
YOU ARE READING
a sanadin auren zumunci
Adventurelabari mai cike da tausayi soyayya zalumci da sauransu ...