🌹 a sanadin auren zumunci🌹
Story and writen by ayshat yusuf
Dedicated to surayyamhs catty🐈
#Follow yusufayshat0
Page2
Tun daga lkc bata kara ba sanin inda kanta yake sai dazu data farka ta ganta cikin wani daki tana fitowa taga mutane a kwance ga kolabe a kusansu Wanda hakan zai nunama shaye shaye sukayi
Anfani tayi da wannan damar ta futa daga gidan ahanya ne ta gamu da wani hawan Allah ya kawota gida
Abba ne ya nufasa tun da ta fara koro musu bayani yace Allah Kyauta Amma Wace unguwa aka kayki
Shiru tayi dan batayi tsammanin irin wannan tambayar ba sai can dubara ta fado mata tayi Saurin cewa basan ina ne ba kasancewar bana cikin nitsuwata Amma naji kamar Wanda ya dawkoni yana cewa wani kauye ne
Baki Umma ta tabe tana cewa yanzu dan Allah meye anfanin tisa yarinya gaba kana mata tanbayoyi in ta gaya maka unguwar wani arziki gareka Wanda zaka iya koto mata yancin ta KO me
Bai tanka mata ba ya cigaba da cewa daga ya'u na soke fita zance kofar gida duk Wanda yazo ya shigo ciki tunda ga fili
Wa ya taba jin zance a cikin gida in dama irin kamar gidan wani attajiri ne ma wannan sai ayi Amma wanan akurki gidan ay yayi kadan da yin zance
Bai kara wata magana ba ya fice yana mai tir da halin matarsa a cikin zuciyarsa
Yau agidan abba sun tashi da shirye shiryen dawowar Abu daga japan Wanda shi ambassador na Nigeria a can
Karfe daya suka je tarben shi jirginsu na sauka sukayi murnar gani juna suka tarkato zuwa gida
Bayan yayi wanka suka hallara a dinning dan cin abinci
Abu yana fara santi ashraf ya hau bubudewa ai shi yayi abincin alhalin KO tsokali bai taba ba yana can yana kallo wani filmGaskiya abu sai ka biyani tunda na zage damce nayi ma abinci harda su santi
Dariya abu yasa yana cewa Anya koh wannan kamar dandanon girki matata ne yana kallon ammi da ta hade rai
Tab ai abu in gaya maka matar taka cewa tayi bazata maka girki ba yanzu ka tsufa ta daina yayinka
Lalube ammi tashiga yi KO zata samu wani abu ta kwala masa gane hakan ke da wuya ashraf ya tashi ya nufi falon yana mai kunshe dariya dan yasan yau ya tabo ma kansa
Yana jin abu na fadin ina kuma zaka bayan kasa min mata fushi bai tanka ba ya idasa falon ya fara aikin na sabo wato kallon
Koh da ya bar gidan ma bata fasa fadin ba sai ta cigaba da fadin in ka korar mata manema sai ka aureta ai
Ke kuma tashi muje ki gasa jikinki o ni yau ina ganin abubuwa diyar tawa daya da Allah ya bani ake min bakin ciki dan ana ganin GABA zata auri mai kudi shine harda saceta dan a lalata mata rayuwa to Allah ba ta mutun ba
Haka dai ta cigaba da jaraba yar jameela ta fito daga daki sanye da hijab din ta na islamiya
Haba ta rike tana cewa inda ranka zaka ga kallo yanzu ke jameela ba dai islamiyar ce zaki ba duba kiga yanda idanunki suka kubura ba
Karya ta mata cewa harda zata bayar shiyasa kuma tun da tayi wanka ta jita dai dai Sauri fucewa tayi dan tasan ba karamin aikin Umma bane ta tsayar da ita
Bayan sun ida cin abinci masalaci ashraf da abu suka fice ita kuma ammi ta shige dakin ta dan gabatar da sallar zuhr
Bayan sun dawo kowa ya shige dakin baccin sa dan huta gajiya basu su tashi sai ana Kiran sallar asr suka je masallaci suka dawo suka tarar da ammi a falon zama. sukayi suka fara hira yar suka kai kan zancen bikin bude asibitin ashraf din da za'ayi gobe sunday Suna cikin magana akan yanda bikin zai basan ce suka ji sallamar moctar aminin ashraf kuma dan aminin abu
YOU ARE READING
a sanadin auren zumunci
Pertualanganlabari mai cike da tausayi soyayya zalumci da sauransu ...