🌹A Sanadin Auren Zumunci🌹Story by ayshat Yusuf
Dedicated to surayyahms catty🐈
Follow@yusufayshat0
Page19
Gyran murya goggo tayi Wanda yasa kowa daga cikin su ya bada hankalinsa kanta
Kallon Mahmud tayi tace nikam wata magana naji nake son nasan ya abun yake
Amsa ya bata da Allah sa nasan da ita
Ameen duka suka amsa ita kuma goggo ta dora da maganar sayayyar ka da hafsat ne nake son nasan ina kuka kwanaSu kam mayaifan na hafsat ba karamin mamaki suka yi da jin wannan zancen ba dan ko so daya basu taba ganin ko da alamun hakan ba
Sunkuyar da kai mahmud yayi yace gaskiya goggo muyi soyayya sai dai ni yanzu bana da ra'ayin aurenta na samo wata wadda zan aura dan dama ni ba sonta nake sosai ba(aikin boka)
Salallami kowa na falon ya fara banda hafsat dake hawayen karya sai Mahmud da har lkcn bai dago kansa ba
Wani tausayin hafsat ne ya rufesu duka bare da sukaga yanda take kuka kamar ranta zai futa
Ai ko goggo ta Shiga ma Mahmud fada kamar ta ari baki sai dai ba abun da ya sa daga ra'ayinsa na kin auren hafsat daga karshe ma futa yayi ya bar musu dakin
Ganin yaka yasa hafsat tafiya zuwa plan b
Yau kimanin watansu daya a dubai sai dai ba abun daya sauya daga yanayin zamansu
Duk da yaka ash bai tauyeta ba yana kokarin sauke nauyinta da ya rataya akansa sai dai saduwar aure ne har yau baya ji zay iya yi da ita
Yau da murna meelat ta tashi dan a yau masoyinta ahmed zai ka mata ziyara tun da safe ta Shiga kitchen take girke girke kamar wadda take shirin tarbar mijinta wanda yayi tafiya ta tsawan shekara KO fiye da haka
Shi kansa ash saida yayi mamakin tashin da tayi da wuri abunda bai taba gani tayi ba duk tsawan zaman su dan ko ya tayar da ita ma ya ficewa take komawa bacci abunta
Haka ya fice office ba tare da ya tanbayeta dalilin hidmar da yaga tanayi ba dan yasan ba amsar kirki zai samu ba
Kamar da safe yanzu ma dai kitchen ta shiga ta dora abinci da ranta yake so ba tare da ta tanbayi hajiyar me za'a dafa ba
Kwanonin da ta tarar ta Shiga wankewa a ranta tana mitar kazamta irin ta mutanen gidan ace kwanonin da aka ci abinci tun wajen karfe daya na rana sai bayan la'asar za'a wanke su
Bayan ta idar ta share falon ta gyra kitchen din kasancewar a lkcin kiris take jira a mata ta tanka yasa bata share dakunan su hajiyar ba
Abincin su ta zuba daidai Wanda zai ishe su ci harma su rage ta jera musu sauran a table a manger (dinning table)
Ta fito rike da kwanon dan ficewa bangarensu ganin magrib ne neman fucewa muryar hajiya ta tsayar da ita
To isassa yau kuma sharar dakin ne bazikiyi ba a maimakon ta tanka mata sai ta koma kitchen
Fitowa tayi hannunta dauke da fresh milk guda biyu sai kuma juice daya
Hakan da tayi ne ya rufe bakin hajiya dan tasan yau in tamata ita ma sai ta rama
Ta kai second 30 tana jira taji hajiya tayi magana sai taji shiru dan haka ta dauki kayanta tare da yin tsaki ta bar falon
Sai a lkcin hajiya ta sauke ajiyar zuciya can kuma ta shiga zagin nuwailat
Ihun da tayi ne yasa hankalin su goggo zuwa gareta koda suka duba ya ta suma dan haka zuka dauketa cike da tashin hankali sukayi asibiti da ita
Kuyi yakuri sai yau na samu kaina
#vote
#comment
#share
YOU ARE READING
a sanadin auren zumunci
Adventurelabari mai cike da tausayi soyayya zalumci da sauransu ...