🌹A Sanadin Auren Zumunci🌹
Story by ayshat Yusuf
Dedicated to surayyahms catty🐈
Follow@yusufayshat0
Page11
Ana gobe dauri aure aka yi kamun jameela inda umma tayi bajinta sosai dan a cewarta tana son ta nuna ma wanda ke mata bakinciki cewa ita ma ta shiga sahun mayan mata tunda tilon yarta zata auri mai kudi
Bangaren jamila kuma bata gayyaci kowa ba dan acewarta auren na iya ranar da aka daura shi ne kaway sai latifa ce ta gayyato mutane dan tsabar iyayi ashe har anko ta fitar kuma ta sayawa mutum goma cikin kudin da suka amsa wajen su ashraf
Ran jamila ya bace jin wannan abun dan ita gani take in ahmed yaji lbr zai iya cewa tana son auren har ranshi ya bace ita kuma in akway abun da ta tsana sama da mutuwarta bai huce bacin ran masoyin nata ba
Bayan an gama kamu akayi walima Wanda ta samu halartar malum da dama anyi lecture akan zama auren wanda ya saka zuciyar mutane dama yin sanyi sai dai banda amarya dan zancen maluman ta kunen ta na hagu hake Shiga yana futa ta dama
Washe gari da wuri suka tashi suka tafi gidan su moctar dan shiryawa kasancewar anan kayansu suke
Shiri suka yi cikin wata shadda fara tas da ita wadda kana ganinta kasan sai wane da wane zasu iya mallakar ta
Dinki aka musu iri daya wanda aka musu harda babbar riga wadda akama aiki da zare black haka yasa suka sa takalmi da hula suma black sai agogo da suka daura mai matukar tsada
Cikin gida suka fice dan neman albarkar mami sai tsokanarsu ake inda moctar kadai ke maida martani dan ashraf sai dai yayi murmushi kaway
Bayan sun fito daga gurin mami gidansu asharaf suka nufa inda anan ma bata sauya zane ba dan sai faman tsokanar su akeyi
Bayan ammy ta musu fatan alheri suka nufi dakin da inna take dan itama tun jiya ta iso da tawagarta
itama tsiyar ta shiga musu inda sai lkcn ashraf ya bude baki ya shiga maida martani
Ganin lkc yana kurewa yasa suka koma hotel din da suka kwana tare da abokansu
Sun tarar sun shirya dan haka basu wani bata lkc ba suka nufi wajan daurin auren
Da misalin karfe takwas da rabi aka daura auren moctar da rukayya akan sadaki dubu dari dan cewar s dadyn rukayya albarkar aure ake so baway yawan sadaki ba
Bayan daurin auren koh minti arba'in basu kara ba suka nufi airport karfe tara da minti ashirin shirginsu ya sauka a kanon dabo
Karfe goma dai dai aka daura auren ashraf da jameela akan sadaki dubu dari kamar na moctar
Da ka kalli fuskar moctar zaka tabbatar da cewa yau Rana ce wadda ta zamo ta farin ciki a garesa sai dai ta fannin ashraf zancen ya sha banbam dan shi mutun ne wanda ba'a gane yanayin yake ciki a fuskar sa
A cikin gida ko an shirya amarya jamila cikin jiga ta alfarma tayi kyau ba laifi sai dai fuskar nan a daure take tamau kamar Wanda aka aikowa da sakon mutuwar umma
Wata mata ce mai zakin murya ta shigo gidan tana guda tare da shelar cewa an daura aure aiko ba kunya umma ta Shiga yin gudar ita ma tana ma jama'a habaici
Aiko kamar kar jamila taji wanan maganar ta kwala ihu mai uban razanarwa wanda ko su ashraf da suke kofar gida suna jiran amarya da masu rakiyarta su fito su fice dan a lkcn za'a fice da ita saboda dinner da su ammy suka shirya saida suka ji karar tata
Cike da rikicewa aka shiga dakin inda aka tarar da jamila sai bori take kamar wadda keda iska gashi sai surutai takeyi
kuma da muryar maza ake magana cewa kar a yadda a futa daga gidan da sunan kaita wanin gidan dan sai ya zamewa wanda ya akaita hakan masifa da bala'i a rayuwarsa kuma a gaggawata sanar da ango cewa ya sakar masa matarsa inba haka ba kuma zai gani
Mamaki ne ya Kama mutane ganin da gaske dai aljani ne ke magana ba mutum ba
Ana haka sai ga abba ya shigo dan ya ga me ya tsayar dasu da ba'a fito da amaryar ba aiko ya tarar da wanan abun na faruwaDaukata yayi ya sata dakin sa ya fita waje ya kira ashraf da moctar suka jiga dakin da sauri umma tabi bayan su
Alkur'ani abba ya dauko ya fara karatu
su dai su ashraf mamaki ne ya kamasu ganin abunda me faruwa amma haka suka daure suna jiran a musu bayanin abunda ke faruwa
Can tasa kara aka kara maimaita abunda aka fada da wari sai a lkcn su moctar suka gano cewa iska gareta
Shi ashraf dariya ma abun ya bashi way ko yaga masifa lallai ma aiko aljanin yana da aiki dan hanzu ya fara zaman aure da jamila
Kimanin mminti ashirin da biyar abba yana karatu kafin ta daina ihun da take ko da suka diba tana bacci Wanda hakan ya faru ne da taimakon maganin baccin da latifa ta bata
Umma ce ta kawo shawarar abar tariyar sai zuwa lkcin da ta samu sauki amma Abba ya ki a cewarsa ko mutuwa zatai yau a gidan mijinta zata kwana
Turare na masu iska abba ya ba ashraf dan in irin haka ta kuma faruwa
Tana baccin aka sakata a motar(a motar su ashraf din zasu koma dan run jiya suka sa aka kawo musu motocin su kano dan daukar amarya da tan rakiyarta) da zata sadata da gidan uwar mijinta dake birnin tarayya da igiyar aure guda ukwu a kant Wanda take ikrarin cewa a ranar da aka darasu a ranar aza'a sincesu
Karfe daya suka gudanar da reception wanda shi kaday ne event din da sukayi a bikin sai kuma dinner da za'ayi da daddare wanda su ammy ne suka shiryata
Ba ita ta tashi sai karfe biyar na yamma inda ta ganta a wani daki wannan ya matukar haduwa kuka tasa dan ta tabbatar da cewa ta iso garin abuja a igiyaryar auren wani da ba ahmed ba akanta
Bata ji shigowar mutum ba sai ji tayi an daga kafadarta juwa tayi taga wata mata wadda suke kama ashraf din wanda hakan ya tabbatar Mata da mahaifitarsa ce
Hakuri ammy ta Shiga bata tare da fada mata ay nan din ma kamar gidansu ne dan haka ta Saki jikinta
Har ta budi baki da sunan mata rashin kunya sai ta tuna da shirinsu na biyu tunda na farko bayi aiki ba sai tayi shuru ba tare da ta futa komay ba
Futa ammy tayi dan sawa a kawo mata abinci ita kuma ta Shige bayi wiki wanke fuskarta
YOU ARE READING
a sanadin auren zumunci
Adventurelabari mai cike da tausayi soyayya zalumci da sauransu ...