page10

494 14 0
                                    

🌹A Sanadin Auren Zumunci🌹

Story by ayshat Yusuf

Dedicated to surayyahms catty🐈

Follow@yusufayshat0

Ina taya ki murnar kammala novel dinki Da ciwo a rayuwata Anty ramlat(mai dambu) Allah Kara baseera da karfin ido muna biye dake insha Allah a matar so
           

                Page10

Ashraf yayi shuru ne saboda ya auna hakalinta da tunanita ya kuma kawar da zargin da yake mata na bata da tarbiya tun a lkcn da ta shigo dakin

Tunuwa da tayi da maganar da sukayi da latifa na cewa kadda ta bari ko angon ya san cewa bata son auren yasa tayi sauri zamowa daga kan kujera ta furta masa ina wuni

Wani sanyi yaji a zuciyarsa ganin cewa abbu ba masa zaben tumun dare ba ganin handa take lulube kanta cikin gyle yasa shi tunanin cewa dama kunya ce tasa ta kasa magana koh a dazu

Cikin sakin fuska ya amsa mata da lfy lau sabanin lkcn da suka  shigo da ya hade fuska kamar hadri

Tambaya sa ta kuma yi da cewa anzo lfy ya gajiyar hanya amsa mata ya kuma cikin sakin fuska

Daga nan ba wanda ya Kara magana a cikin su kowa da abunda yake sakawa a zuciyarsa

Ita jamila ba'abunda take sai zaginsa a zuciyarta dan wata tsanarsa take ji duk da kyau din  taga ya mata amma soyayyar ahmed ta yana hakan tasiri a gareta dan haka ta kagu da taji ya furta zai fice sai dai shiru har kusan mintina biyar

Ashraf kuma ba abunda yake tunani sai alkawarin da ya daukarwa kansa nan cewa zai karbi duk matar da abbu ya zaba masa hannu biyu to hanzu ma bata canza zani ba dan duk da soyayyar hafsat da ya ke ya kudirta cewa zai yi korarin kyautatawa matar sa dai dai iyawarsa dan da alamu zatayi dadin sha'ani

Shi ya kashe shirun da tambayarta events din da zasuyi da kuma wanda ya kamata su halarta

Amsa ta baji na cewa saidai yayi magana da latifa dan ita bata San me suka shiryawa ba

Jin an fara kiran sallar as'r ya mike tare da fadama ta cewa zasu tafi masallaci su kokarta gama shawararsu kanfin su dawo dan yau suke son fucewa saboda muna son jin abunda ake shiryawa ta fannin matar da moctar zai aura

Sai a lkcin tasan cewa moctar din ma aure zaiyi

Da toh kaway ta amsa masa yayi gaba abunsa ta raka bayansa da harara tare da Jan wani uban tsaki kamar harshenta zai tsinke

Gurin da moctar da latifa suke tsaye ya isa ya masa magana suka fice masallacin dake kusan da gidansu jamila

Dakin latifa ta koma ta iske ta a zaune tana chatting zama tayi kusa da ita tana cewa fatan dai daki bata mana shiri ba

Tsaki tayi wanda ya zame Mata dabi'a idan ranta ya bace ta wlhy ko na kusa na shuka masa rashin mutunci kuma sai na tuna da maganarki
Kuma yace mu tsayar da abunda zamu yi a bikin kafin su dawo daga masallaci saboda suna son su koma yau dan suji abunda ake shiryawa daga bangaren amaryar moctar

Latifa bata ji dadin cewa moctar zaiyi aure ba dan ita taso ta kafa gomnatin ta dan itama ta Shiga irin daular da jamila zata shiga

Aikam gomma da baki yi ba yanzu dai in sun zo sai mu sanar dasu cewa za'ayi events kala ukwu duk da kin ce bazakiyi komai ba bayan kamu da walimar da abba da umma suka ce za'ayi

Kallonta jamila tayi tace ay dama ce musu akayi biyar dan ni wlhy so nake na talauta dan banza mutum sai ji dakai kamar wani sarki magana mafa da ker ya keyi kamar wanda na sashi dole ko nace masa Ina da bukatar jin muryarsa

Dariya latifa tasa tare da cewa ai haka ake son mutum mai aji gaskiya guy din nan yayi dan wlhy ni ya mafi burgeni akan wanan ahmed din naki mutum kamar bulala

Cikin fushi jamila ta dakatar da ita kinga malama saurara min kar ki kuma zagin ahmed dan akansa zamu iya zaba hanya da ke ta idar da maganar tata ta huci

Cike da mamaki latifa take kallonta a zuciyarta kuma cewa take ya za'ayi in harda mu raba hanya dake a hanzu banyan ban fara tatsar rabo na ba ta bude baki da niyar bata hakuri kenan suka ji sallamar su ashraf dan haka ta rufe bakinta

Zama sukayi bayan sun shugo moctar yace toh muna jinku me kuka tsayar latifa ta bashi amsa da events hudu zasuyi

Jinjina Kai moctar yayi alarmar gamsuwa ya tambayeta ko akway wanda ango zai halarya

Ashraf sai wata yake a cinkin zuciyarsa Allah sa babu wanda zasu halarta dan shi baya son kayan ciwon Kay

Cike da alamun rshin gaskiya har sun so su gane hakan latifa tayi sauri cewa babu dan duka mata kadai ne

Kudi ne latifa tace dubu dari sai ashraf ya kara musu wata darin cike da jin dadi ta karba ba tare da korafin sun yi yawa ba ko wani Abu ba  suka musu sallama sai da suka biya suka gaishe da Umma kafin su fice inda take ta rawar jiki a kansu dubu ashiri suka aje mata a Cewar su ta Kara a hiddimar biki

Har zasu jiga mota suka ga abba ya shirin Shiga gida gaisheshi suka yi inda shi kuma ya amsa cike da kulawa yana tambayar su iyayensu amsa masa sukayi da lfy lau sun dan taba hira inda abba ya musu nasiha mai ratsa jiki sallama suka masa Shiga suka aje masa dubu talatin wanda da ker suka shaho kansa ya amsa wanda yakan ya Kara ma tsohon mutunci a idanun su

Daga gidansu jamila kai tsaye airport suka nufa inda suka tarar da abokinsu mas'ud yana jiran su dan ya amshi motar da suka zo da ita in zai je wajen biki sai ya tafin musu da ita

Hira suka jiga yi ta yaushe gamo wanda duk rabin hirar tsakin mas'ud da motar ne dan ashraf sai dai yayi murmushi kaway hakan yasa suka gane yan miskilancin sun zo dan haka suka daina saka shi a maganar suka cigaba da hirarsu su biyu

Karfe biyar jirginsu ya daga daga kano zuwa birnin tarayya
Koh da suka sauka a sun tarar da dereba yana jiransu

Da suka isa gida wanda sukayi suka sawya kaya ko abinci basu tsaya ci ba suka kama hanyar gidan su rukayya

Kamar yanda suka ba su jameela dubu dari biyu a kano haka suka ba su rukayya ma sai dai su events biyu kadai zasuyi kuma duk na mata kadai

Shiryen shiryen biki ya kanka ma dan yan uwa na nesa da kusa sun soma isowa wanda yaka yaja saida su moctar suka Kama hotel dan abokansu har na waje sun fara zauwa

Bagaren jamila kam har tanzu ta kasa daukar kaddarar rabuwa da ahmed dan ko a yau da biki saura kwana biyu saida suka tara da ahmed inda ta ke Kara kara karfafa masa guwwa akan cewa ita din tashi ce kar ya damu dan za'a daura auren ne kaway amma ko gidan baza'a kaita ba da angon zai saketa

#vote
#comment
#share

a sanadin auren zumunciWhere stories live. Discover now