page18

491 16 0
                                    


🌹A Sanadin Auren Zumunci🌹

Story by ayshat Yusuf

Dedicated to surayyahms catty🐈

Follow@yusufayshat0

                  Page18

Haka suka cigaba da hirarsu ba Dan nuwailat ta yarda da ce ba abun da suka wa mahaifiyar tata ba dan tasan halin muguntar mutanen

Gobe Mahmud zai dawo dan haka hafsy ta rasa me ke mata dadi daga karshe dai ta yanke shawarar komawa wajen bokan daya mata aiki akan mahaifanta

Washe gari nuwailat ce ta shiga gidan dan tayi aiki dan duk lkcin da take haiyacinta bata barin saudat ta yi wani aiki na wahala

Tana Shiga ta tarar da hajiyar da mijinta a falo suna ware kayan da za'a raba cikin tsarabar da ya kawo

Kamar yanda ta zata kuma hakan ce ta faru maganun da suke sakata kokonto da zurfin tunani hajiyar ta Shiga fada mata

A da in hajiyar ta kirata da mahaukaciya sai tayi zaton saboda tsanar da ta musu ne shiyasa bata Damuwa

Sai dai yanzu abun ya fara damunta dan a ganinta daga saudat tazo aiki yau a goben in ita taje sai taji hajiyar tana tambayar ta da cewa haukan ya lafa kenan

Bata gaishe da su ba ta fuce ta shige kitchen dan a dunia babu Wanda ta tsana sama da hajiya da mijinta sai Allah ya daura ta akan su munguwar shakkarta suke dan duk irin bautar da ake saka saudat ita ba'a saka ta abun da tayi niyar yi shikenan sauran sai dai asamu wani yayi

Break ta daura ganin abunda ta daura ya kusa ya dahu yasa ta rage hutar gas din ta futo falo ta fara mopping bayan ta gama ta jere breakfast din kan dinning

Dakin alhaji ta shiga ta gyra sannan na hajiyar dan duka wannan yana daga cikin aikinta

Kitchen ta koma ta cika kula su da abinci dan haka ta saba bata wani tsayawa hajiyar ta debar mata

Ta gama duk tunanin da zatayi ganin bata da mafita yasa ta aiwatar da abunda zuciyarta ta raya mata wayarta ta dauka ta kira nusee

Sun kai minti ashirin suna magana sanan ta katse kiran ta Shiga wanka dan sai alokacin take jinta sakayau bata da wata sauran damuwa dan gani take kamar matsalarta ta kaw tunda nusee zata je mata wajan boka

Sashin su ta fice da kularta a hannu inda ta tarar da har ummu nata ta gyra gidan dan haka ta zauna suka ci abinci

Ta dauki uniform dinta na islamiya ta saka tama ummun sallama ta fice

A can dubai kuma ashraf bai wani huta ba dan gani hake ba anfanin zaman gidan tunda matar gidan ba way ta damu da shi bane dan haka washe garin ranar ya fara futa office

Hakan ba karamin dadi yai wa jamila ba dan holewarta take dan ahmed dinta inda har video call suke da juna a tsirara

Satin su daya ta fara futa hawo ita da wata da suke Katanga daya ita ma yar Nigeria ce

Samira mace wadda bata da aiki sai bin bokaye ga karya saidai kuma duk abunta tana son mijinta kuma tana mugun kishinsa

Bata dayo ba sai bayan sallar asr wanda dama haka tsarin islamiyar tasu take

Jakarta kadai ta ajiye ta fuce dan zuwa yin aikin yamma kasancewar tayi sallah a islamiya

yau kwanan Mahmud biyu da dawowa kuma yau ne hafsat da iyayenta suka je gidan gwaggo dan masa sannu da zuwa (Mahmud maraya ne dan haka yake zaune a gidan gwaggo tun yana yaro a hannunta ya taso )

Bayan a kare gaishe ne gwaggo tayi gyran murya hakan yasa kowa ya nitsu dan sun san magana ce zatayi mai mahimmanci

Ba yawa kuyi hakuri

#vote
#comment
#share

a sanadin auren zumunciWhere stories live. Discover now