36 too 40

111 5 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Wattpad*
*HaseenahNaseer*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}

https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=110640203812862&id=110638730479676

_________________________
________

*Dedicated too*

*Noorul Hannerh* *love my dear*

*Special gift too my mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

*Not editing*🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

*Page*

*36 too 40*

.........Duk abun duniya ya taru yama Daddy yawa ,  dan yanason Sultana  tafi kowa karatu a cikin yaran sa gashi kuma tak'i Sam tana neman watsamar k'asa a ido, yau ma kaman kullun daddy ne zaune a parlor tare da matar sa Fatima sai faman zubamar hira take yi shidai ba wani fahinta yake yi ba , saidai bazai iya cewa tabari ba dan yanzu kamar ma Wanda daddy yake tsoron Fatiman.

Sultana ce ta shigo d'akin babu ko sallama , jikin daddy ta zube tare da cewa "my dad kud'i nake so , zan saima friend d'ina gift yau birthday d'in ta , kuma banda data , sannan kayan make up d'ina sunyi low..

Tunda ta fara maganan momy faty take watsa mata kallon banza! har takai k'arshen maganan ta, itama y'ar ta zainab ta shiga kwad'awa kira "zainab zainab, wai kina inane?".

"Yes Mom gani nan , ina waya da uncle ne game da tafiya na India karatu yace nayi list d'in abunda nake buk'ata...

"A'a gaskiya baza ki d'oramar wahala ba , ga Alhaji shine ya dace ya miki komai tunda gaban sa kike zama....

Ai kafin ta rufe baki Sultana ta fara magana" tabd'ijam , ai wallahi bazai mata ba , dan ba shine ubanta ba saidai taje gun nata uban ya mata , aikin banza agola kawai...

"Keh Sultana karki sake ki zagine , dan naga Baki da kunya ko dake ai banyi mamaki ba ubanki da yabaki duk kan gata ya fifitaki ma kin watsamar k'asa a ido bare ni , "gaskiya swt heart kayi sake wankin hula zai kaika dare , ai tunda tace aure take soo sai ka mata kafin ta lalace tunda ta fitar da zalaman ta a fili ta nuna...

Daddy ne ya katseta da "ya isa haka Fatima , ki daina biyewa Sultana domin kuwa k'aramar yarinya ce , zainab kije kimin list na abunda kike buk'ata kizo ki fad'a min nawa ne zai isheki...

Kafin ya rufe baki Fatima tace " zai Kai 1million take buk'ata .

"Ohk ba damuwa , na miki transfer ta account d'in ki kenan?".

"Yes mijina , ta furta tare da watsawa Sultana harara .

Zainab ce ta fara zubawa Daddy godiya tare da addu'ah.

Momy faty ne ta katseta da cewa"keh dalla kimin shiru ya isa haka ,sai faman godiya kikemar ai kema ubanki ne bacin arziki kikazo ba tunda Uwar ki yake aure.

Sultana mutuwan tsaye tayi agun , kai ubannan ta furta a ranta , yau ni Sultana wasu banzaye zasu wulak'anta kuma gaban daddy na Amma baice komai bah?" .

Cikin tashin hankali ta fice daga d'akin zuwa nata kamar wata mai tashi sama , bawan da yabi ta kanta ma sukaci gaba da hiransu , Fatima sai shagwa6a take zubamar ita gamai laulayin ciki...

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now