26 too 30

127 6 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Wattpad*
*HaseenahNaseer*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_______________________________

*Dedicated too*

*Noorul Hannerh* *love my dear*

*Special gift too my mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

*Iyyaka na'abudu wa iyyaka nasta'in'* .
*May Allah be there at every point of our needs & continue to bless and protect you & your family. Ameeen Jum@t Mubarak*

*Page*

*26 too 30*

............Kaf d'inkin sake baki sukayi , tare da duban Sultana cikin tashin hankali ba tare da sunce komai bah.

Sultana ganin duk d'akin ita suke kallo yasa ta murmushin mugunta tare da watsa musu kallon banza!.

Daddy ne ya fara magana " shikenan ina fatan kunji hukuncin da Sultana ?" ,yanda ta fad'a hakan za'ayi domin inason ganin farin cikin d'iya ta , tunda ku bakwa sonta ni kan ta zama min dole , Allah ya miki albarka Sultana ummi nah uwa ta gari I love you Allah ya barmin keh ina alfari da ke a kullun.....

Tinin mamy kam tabar d'akin dan bazata iya ci gaba da ganin wannan 6acin ran bah.

Mommy ce ta mik'e tare da cewa "Allah yasa ayi damu.

"Ameen , inma da wata manufa kikafad'a , toh sharrin ki ya koma kanki.

Suma yaran mik'ewa su kayi jiki a sanyaye suka bar d'akin .

Ita kam Sultana zuciyar ta fari tas ,sabo da zata yi Aunty .

Kasan cewan Daddy baya wasa da lamarin Sultana cikin sati d'aya ya gama daidai tawa da matar da zai aura , har ansa lokacin biki nan da sati uku masu zuwa , Daddy yaso kai amaryan sa wani gidan daban Amma Sultana tak'i yarda wai saidai su zaina a wannan gidan sabo da tanason d'akin ta , koda daddy yace zai had'a mata Wanda yafi  wannan Sam tak'i yarya babu yanda Daddy ya iya dole ya barta ya fara gyaran gidan sosai domin sa amaryan sa.

Ita dai amaryah bata so hakan ba , amma tunda ta fahinci sai yanda Sultana tayi da uban nata shiysa ta hak'ura , za kuma taci uban yarinyan a hankali yanzun kan kaman za ta cinye ta sabo da Soo, *Hajiya Fatima* Fatima ma'aikaciyar banki ce , ayanzu ta ta6a aure  yaran ta uku, suka rabu da mijin a gidan ta take zaune bawai gidan iyayen taba , ina nufin zaman kanta takeyi a yanzu Fatima gogaggiyar yar duniya ce wanda take juya maza take abunda takeso a yanzu ,duk wasu halayen ta marasa kyau ta ta6oyewa daddy su.

Sultana kan murna ba'a magana daddy zaiyi aure har party ta shirya...

Hajiya Fatima tun kafin ta shigo gidan take ji da Sultana take kuma tarairayan ta , ga uban kud'i da take kashemata itakan Sultana abun nema ya samu , shima daddy yana jin dad'in yan da Fatima ke bawa Sultana kulawa .

A 6angaren su mommy suna shan kallo dan sun sawa Alhaji ido , ganin abun yafi k'arfin magana zadai su bishi da addu'ah.

Anyi biki amarya ta tare a gidan ta , sauk'in ta d'aya Sultana har yanzu tana 6angaren iyayen ta da zama tunda acan d'akin ta yake, tana kuma lalla6ata domin su rabu lafiya , saida aka kwashi wata guda a hakan Sultana ta tayar da daru akan dole sai mahaifin na ta yamata wani d"akin bacci a 6angaren Momy fatyma , babu yanda Daddy ya iya dole ya zuba mata kaya a wani d'akin a cikin 6angaren , d'akin ta ya zama biyu a gidan .

Ita kan fatyma bata jin dad'in hakan ba amma ba yanda ta iya dolen ta danne zuciyar ta da kuma haushin yarinyan da take ji  dan bata son tun daga yanzu ta fara nuna halin nata marar kyau.

Duk yanda momy faty take kyau ta tawa Sultana hakan bai hana Sultana ta farajin haushin taba , acewar ta Daddy na bawa mommy faty kulawa da yawa ta fara tinanin asiri akayiwa Daddyn ta , yake 6arin jiki haka.

Sultana kwana takeyi babu bacci sabo da cikin dare tana yiwa mommy Faty la6e sai da safe take yin baccin , tun Fatima bata fahinci hakan ba harta gane , ta kuma fara tinanin meye abunyi k'awar ta Hajiya Falmata ta kira domin neman shawaran ta ko data zaiyana mata abunda yake faruwa  shawaran itama ta d'auko d'iyar ta zainab tunda sa'ar Sultana ce may be asamu sauk'in hakan zata rage abunda take yi , amma yanzu lokacin fara d'aukan mataki baiyi bah....

Bayan kwana biyu kuwa zainab ta dawo gidan Sultana bataso hakan ba , saidai tayi hak'uri sabo da mommy faty na kyautata mata , tana shafar ta kamn wani man shafawa, duk yanda fatyma taso Sultana da Zainab su zauna d'aki d'aya amma San Sultana tak'i dole aka nemawa Zainab wani d'aki daban , a gidan .

Ayanzu su mamy kan sai suyi  sati basu sa Daddy a idon suba , koda ran kwanan sune, Fatima sai yanda tayi da mijin ,acikin haka auren Fariha ya tashi Alhaji musa ya rik'e bakin aljihun sa Sam yak'i bada kud'i komai na walak'anci yake yi da k'ask'anci bbu yanda suka iya dole momy da mamy sai ya Nura Wanda shima karatu yake amma yayi k'ok'arin bada wani abu , Su mamy dai sune k'arfin kud'in , tunda sun had'a Kai suka yiwa yarinyan duk abunda ya dace.

Kwance tashi bbu wuya a wajen Allah , Sultana harta zana Ssce kyaud'in ta ya k'ara fita ta cika tayi wani kyau naban mamaki duk namijin da ya ganta sai ya k'asa Masha Allah,sai dai kullun salon iskanci da raini gaba yake yi agunta baya baya , ga walakan ta muta ne ko kai waye bakafi k'arfin taci ma mutunci bah.

Sultana ce kwance akan makeken gadon ta waya take tana ta zuwa shagwa6a , ga duk kan alamu hak'uri ake bata daga cikin wayan.

Baki Sultana tasake turawa sannan tace "nidai kafad'a min yaushe ne zaka dawo wallahi hak'uri na yana shirin k'arewa ina matuk'ar buk'atarka a kusa dani ya kakeson nayi ne?" , kullun daddy yana kawo min wasu Amma naki saboda Kai nake so kaine za6i na sannan kaine rayuwa tah...

Sultan shiru yayi yana sauraron ta har takai k'arshen maganan ta , sannan yace "am sorry baby na kusa insha Allah ki k'ara hak'uri aini naki neh ke d'aya daga ke kuma na rufe k'ofa....

Sultana murmushin ta tayi mai k'ayatarwa da k'ara mata kyau tankar yana kallon ta , sannan ta share hawayen nata tare da langa6ar da Kai .

Washe gari 12:pm  Sultana ta farka daga bacci ,kasan cewan ta kwana tana waya , wanka tayi tashirya cikin riga da wanda sun bala'in kamata , bata d'aura d'ankwali ba ribbon kawai tasa ta kama gashin ta ,wayan ta tajawo ta kunna sannan ta Kira sultan sai saida taji lafiyan sa sannan ta mik'e ta nufi parlor ,zare ido tafara yi ganin duk anyiwa parlon decorations yayi kyau sosai ga kuma wani k'aton cake a tsakiyan parlon shima din yasha kwalliya, cikin mamaki ta shiga dube dube , momy faty ne ta fara fitowa tana dariya Zuwa tayi ta rungume Sultana tare da cewa " congratulations fr our ssce graduation , Sultana bata ce komai ba illa sakin baki da tayi tana bin momy faty da kallo , Daddy ne ya fito shima tare da hugging din Sultana ta baya, yana yin yanda ya rik'etan ta gane Daddyn tane wani tsalle! Sultana ta buga tare da sake rik'esa sosai , "welcome back Daddy nah sauk'an yaushe wallahi nayi missing d'in ka kullun sai nayi kuka , ka tafi ka jima ka barni , saushe ka dawo ?"  .

"Sorry my daughter , kina raina kullun da tinanin ki nake kwana nake tashi , nasa na dawo lokacin bikin gama skull din naku Allah baiyiba , shiysa na shirya miki nawa bikin yau a gida , ina miki fatan alkairi d'iya ta Allah yasa alkairi cikin karatun , maza rufe idon ki saiki mik'omin hanun ki.

"Amin Sultana ta amsa, dare da rufe idon nata kamar yanda mahaifin nata ya bata umarni.

Key d'in mota Daddy ya jefawa Sultana cikin hanun ta sannan yace maza bud'e idon.

Cikin saurin Sultana ta ware ido tana k'ok'arin yin magana , daddy ne yasa hanunsa akan bakin nata sannan ya kama hanunta suka fita waje , fatyma ya duba tare da cewa follow mie .

Momy faty cake din ta d'auka ta bisu tashi tana murmushin yak'e, saidai na ciki na ciki kan uban nan ya sayawa Sultana na mota?" Lallai anzo wajen da hak'urin ta zai kare.......

*Vote*

*Comments*
       &

*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now