41 too 45

121 6 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Wattpad*
*HaseenahNaseer*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/Xahrah-Farooq-Novel-110638730479676/
_______________________________

*Dedicated too*

*Noorul Hannerh* *love my dear*

*Special gift too my mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

*Note Editing*🤦🏼‍♀

*Page*

*41 too 45*

..........Sosai jikin Zainabu ya kama 6ari! Sabo da tsananin tsoron abunda zai faru , gashi yau mahaifin ta mai tare matan baya gida.

Tsawa! Laitana ta sake dakawa Zainabu, "bakya jinane?" , Ko ba dake nake magana bah?".

Zainabu cikin rawan murya! tace "daman tulunne ya fashe....

"Kan uban nan ya meye ?".

"Fashewa yayi Zaibanu ta maimaita zancen .

"Kika fasa dai dan ubanki , kuma wallahi biyana zakiyi shegiya bak'ar muna fuka wanda batason ci gabana, karuwancin da kike yi ake zagina bai isheki ba sai kin had'a da bak'ar muguntan baki kin cutar dani , wallahi biya zakiyi bakya min sana'an komai dan haka bazan d'au asara ba , ki fita ki nemon kud'in siyan tulu , saboda bak'ar muguntan kije birni ki ringa yin aikatau ki samo kud'i ma kunk'i keda mahaifin ki ,dake duk muguntan ne a ranku , wai ke y'ar boko sai kici bokon ai , boko ko karuwanci ohoo! ga yawon bokon naki ai yanda ya jama gidan nan bak'in jini Kuluwa ko zuwa neman auren ta ba'ayi sanadin bokon naki ance gidan karuwai ne....

Zainabu ta bu6e baki zatayi magana , Lantana ta jifo mata wani k'aton dutsi tas kake ji ya sauk'a a fiskan Zainabu , ihu! tasa tare da ficewa a gidan , kafin kace meye wannan jini ya jik'a hijab d'in nata gaba d'aya , kid'imewa Zainabu tayi tama rasa meye zata yi Sam , rik'e gun kawai tayi tare da ci gaba da kukan ta...

Ahmed ne ya fito daga nasu gidan , ganin zainabu cikin wani yana yi yasa shi zuwa inda take cikin sauri , "subhalallahi zainab...

Dak'er ta d'aga Kai ta dubeshi sannan ta mayar  sabo da jinin da yakai zuba , hanun ta ya rik'o tare da shigar ta gidan su , ina Larai ce ta d'ibo ruba aka wankewa zainabu gun ciwon suna mata addu 'an Allah ya kawo mata k'arshen wannan lamarin dan ba sabon abune agunsu ba daman sun saba gani.

Inna Larai ne ta tanbayi Zainabu abunda ya faru , bayan ta fad'a mata ne ta bata wani tulun tare da zuba mata ruwa aciki , zainabu d'auka tayi sannan tayi godiya tabar gidan...

Asanyaye Ahmed yake bin zainabu da kallo idan sa fal gawaye , bayason ganin yarinyan cikin damuwa iya matuk'ar sonta kuma yana da niyyan auren ta insha Allah.

Inna Larai ce ta juyo ta dubi D'an nata da duk yanayin sa ya Sanja , "Ahmed ta Kira sunan sa.

Ahankali ya juyo yana dubanta , ba tare da ya amsa bah.

"Agaskiya lokaci yayi da zaka fidda yarinyan nan cikin damuwa , kaga dai ta kammala karatun nata ko.

"A'a Inna bata gamaba futu tazo saidai a wannan shekaran zata yi paper .

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now