66 too 70

113 5 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Gmail*
*xahrahfarooq@gmail.com*

*Wattpad*
*XahrahFarooq*

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

https://www.facebook.com/Xahrah-Farooq-Novel-110638730479676/

_______________________________

*Dedicated too*

*Noorul Hannerh* *love my dear*

*Special gift too my mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

*Page*

*66 too 70*

*Note Editing*🤦🏼‍♀

.......Cikin zumud'i Sultana ta fad'a bathroom, bata wani d'au lokaci ba , ta fito d'aure da towel tana goge jikin tah, mai ta shafa sannan ta feshe jikin ta da tirare, doguwar riga ta zira a jikin ta , jim tad'an tsaya kome ta tina ohoo,, tsaki tad'an jah, tad'au gyalen ta tare da key d'in mota ta fice daga d'akin.

Parlor ta nufa cikin sauri , Daddy ne yayi magana cikin sanyin murya , ba tare daya kira sunan taba yace" ina zakije?"

Cikin sauri! Sultana ta juya inda taji anyi maganan , dan bata masan akwai mutane a parlorn ba , ido suka had'a da Daddy , fiskan sa babu yabo babu fallasa , shiru tad'an yi na wani lakaci tana tinanin abunda zata cemar....

Tsawa Daddy ya buga mata, " bada ke nake magana bah?" .

Take idon Sultana ya ciko da hawaye! tana shirin yin kuka.

Momy Faty cikin farin ciki , tare da kirsa ta matso sosai kusa da Daddy, "haba honey banason kana d'aga hankalin ka akan abunda baikai ya kawo ba , yanzu meye abun fad'a anan?" , ta k'arisa maganan tana shafan gefen fiskan sa.

"Bakya ganin ina mata magana ta manna min hauka ne?".

"Ai hak'uri zaka yi , kasan Sultana yarinya ce, sannan y'ar soo.

Sultana wani bak'in cikine taji ya tokare mata wuya , yayin da hawayen takaici ya shiga bin kuncinta.

Ganin hakan yasa Momy faty tayi wani fari da ido sannan tace honey ka barta taje kaji..

"Shikenan gimbiya , taci albarkacin ki.

"Murmushin jin dad'i tayi , sannan tace godiya nake ranka shi dade.

Sannan ta watsawa harara sannan tace shikenan kije , amma karki jima.

Sultana dak'er ta iya jan k'afar ta tabar wajen , badan tanason taje taga farin cikin taba , tabbas data hak'ura, yanzu ita Daddy ya kema wannan cin mutun cin me tamar haka yabar sonsa , wasu hawaye masu zafine suka zubo mata! , ahankali tasa hanun ta ta shiga sharewa.

Asanyaye ta k'arisa jikin motan , tana k'ok'arin mud'ewa , wayan tane ya shiga k'ara da sauri ta d'aga danko bata dubaba tasan waye neh.

Tana d'agawa bata jira taji abunda zaice bah , asanyaye ta fara magana , "kaji  shiru ko?".

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now