126 too 130

93 7 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Gmail*
xahrahfarooq@gmail.com

*Wattpad*
*XahrahFarooq*
https://my.w.tt/q5NpdRP3L7

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Snapchat*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

*YouTube Channel*
*AL'UMMA TV*

https://youtu.be/vRkcRYYZdtA
بسم الله الرحمن الرحيم ___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

https://www.facebook.com/groups/227620608315825/permalink/254851642259388/

*Special Gift too my Mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

     *Note Editing*🤦🏼‍♀

*Page*

*126 too 130*

......."Wannan k'arya ne , bana son zancen banza bazan d'au iskanci bah, dalla mik'e amai d'in da kika yi yana jiran ki , ko akwai bawan ki da zai kwashe miki amai d'an shege?".

Sultana dak'er ta iya d'aga Ido tana duban Ummy , k'ok'arin mik'ewa take yi amma ta kasa saboda yanda jiri yake d'iban ta.

Ummy ce ta sake daka mata tsawa , "zaki mik'e ne ko sai kinjin sauk'an mari?" , Ai wlhy wahala ta ganki tunda baki da zuciya , yaro yama sake ki amma kizo gidan su ki zauna , andai ji kunya an had'a da asara.

Sultana mik'ewa tayi tabar wajen tana zubar da hawaye, wajen aman da tayi ta nufa ta fara gyarawa , sannan ta wuce zata je d'aki ta kwanta.

Tsawan da Ummy ta sake doka mata ne ya sata saurin tsayawa, "keh ina zaki he?" , Uban wa zaiyi girki wato girkin ne baza kiyi ba shiysa ma kika kunna gas kika tafi kika barshi saboda mugun ta , ai inda ubanki ne yake refiling da baki barshi a kunne sama da 1hour bah, aikin banza.

Sultana baya ta dawo tazo gaban Ummy ta zube tana shar6an kuka,! "dan Allah Ummy kiyi hakuri wlhy idan na shiga amai zanyi...

"Amai zaki yi fa kike cemin?" , To me kike nufi?".

"Ni na yarda zan muku girkin da ice, tayi maganan tana dafe kan ta saboda tsananin ciwon da yake mata kamar zai fashe.

"Shikenan Ummy  ta furta a tak'aice, nanma ba tsananin tausayin Sultana bane yasa ta yarda , kawai dai gudun kar 'a 6ata mata kitchen da amai ne yasa ta yarda.

"Shikenan za'a fito da murhu ki fara.

Hakan kuwa akayi , murhun aka fito dashi tare da ice , Sultana takai 1hour amma wutan yak'i kamawa da abun ya isheta sai ta fara kuka , saidai ganin bbu wani mafita yasa ta goge hawayen ta .

Wajen had'a girkin ansha daga , dan bbu abunda Sultana ta iya girkawa banda tea, indomie, acikin girki kala biyar da aka sata ko d'aya batayi ba dan bata masan taya zata fara bah .

Abunda yafi mata sauk'i ta za6a wato white rice and beans , shima sam bazai yiwu bah daga waken har shinkafan jik'a yayi bazai ciwu ba ko da wasa saboda wutan sam icen baya chi...

Duk yanda taso had'a source Amma ta kasa, attaruhu ta d'iba son rai ta sai gishiri maggin ma baji yayi bah , albasa kuma gaba d'aya bata sabah gashi da tazo yi duk ya k'one yayi bak'i , ni na tabbatar duk wanda yaci girkin nan yau zaiji a jikin sah😂😂😂.

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now