81 too 85

117 8 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Gmail*
*xahrahfarooq@gmail.com*

*Wattpad*
*XahrahFarooq*

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Snapchat*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

https://www.facebook.com/Xahrah-Farooq-Novel-110638730479676/

*Special Gift too my Mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

     *Note Editing*🤦🏼‍♀

*Page*

*81 too 85*

........... Ahmad a nashi 6angaren ,tun bayan zuwan sa garin kaduna kwanan sa biyu ya gamu da tsautsayi , yazo tsallaka titi mota ta bugeshi , yanzu haka yana asibiti cikin mawuya cin hali....

Gidan su Ashwan shirye shirye akeyi sosai , duk da cewa itadai mahaifiyar sa ba wani damuwa da lamarin auren nasa tayi ba tunda bawai tanason ya auri yarinyan bane, saidai a yanzu dole ta saki jiki ba yanda ta iya , dan mahaifin Ashwan yafi k'arfin gidan sa.

Tsakanin Sultana da Ashwan babu maganan kirki sai zagi ne kawai ke shiga tsakanin su , saidai hakan baya damun Ashwan tarata yakeyi duk sanda ya aureta zai shayar da ita ruwan azaba.

Tun bayan da Daddy ya gama jiggan Sultana yaja matar sa sukayi d'aki cikin so da kulawa ba tare da ya k'ara bi takan Sultana bah.

Sultana saida taci kukan ta mai isanta sannan taja k'afa tayi d'akinta , ga kuma zazza6i mai zafi daya rufeta , kan gado ta fad'a tana wani irin shashshek'an kuka , tabbas wannan rana tazo mata da wani irin yanayi , abu biyu ne ya sameta farin cikin saduwan ta da Sultan , sai kuma bak'in cikin dukan da mahaifin ta yayi mata, nan take ta fara murmushin farin ciki , tare da runtse ido tana tino abunda ya faru a wunin yau , pillow ta jawo ta rungume k'an a jikin ta , can tad'an yi shiru kamar me tinani , a hankali ta bud'e baki ta furta "wai yau ni Daddy ya mawa duka a kan matar sa ?"  bayan niceh nasa a auro ta , gaskiya ne daman hausawa sunce d'an Adam butulu, ita daddy ya daka yau ?" Ni Sultana meyake shirin faruwa dani?" Badai rayuwa ce zata juyamin baya ba?" , lallai wannan shi ake kira *Juyin Rayuwa* , da sauri! tace Kai kai Kai never wallahi nafi k'arfin hakan , nasa akayiwa Uwar da ta haifeni ma kishiya bare wata banza , bati dai na barsu nad'an lokaci amma zangyara mata zama nan kusa , shima Daddy na fahinci giyar soce take damun sa , da kuma jiki da take sakanmar  yake murza banza shiysa yake ta 6ari tsoho dashi baya kunya , ni kuma yana shirin rabani da Wanda nake so saidai wallahi bazan yarda ba domin kuwa Sultan shine rayuwata , farin ciki na , kuma abun alfahari na , inason shi sama da daddy kuma inason shi sama da kaina banida kamarsa , shine bugun zuciyata....

Washe garin ranan kuma iyayen Sultan sukazo neman auren Sultana, anan Daddy ya shaida musu kwana uku ya rage a daura mata aure da wani, duk yanda mahaifin Sultan yaso nusar da daddy abun yaci tira daga k'arshe Daddy rashin mutunci ya fara gurza musu kan cewa Sultan shi yake furewa Sultana kunne, ananfa Abu. Yaso kwabewa dan shima mahaifin Sultan bai yarda anci zarafin dansa bah, ahaka sukabar gidan ba wata jituwa sai bacin rai..

Bayan komawan Abban Sultan gida , sam yak'i fadawa D'an nasa abunda yake faruwa yadaice sunce a basu lokaci.

Badan komai Abban yayi hakan ba saidai gujewa D'an nasa shiga wani yanayi tunda ba lafiyane da shiba, ciwon zuciya yana da babban had'ari....

Mu sanman su Ummul'kairi , Farihat, Nura, Nasir, Husna , sukazo gidan kai tsaye suka tinkari daddy akan case d'in momy , suka nunamar rashinjin dad'in su akan abunda ya aikata...

Daddy tsumewa yayi yaringa sauk'emusu buhun rashin mutunci , ta inda ya shiga batanan yake fita ba , aranan cewa yayi momy da mamy sune suka 6atamar Sultana har take shirin fin k'arfin sa yanzu...

Bayan da suka iya haka sukabar gidan jiki a sanyaye , da kuma tarin bak'in cikin Sultana ga kuma tsanar yarinyan daya dasu a cikin ransu...

Sultana duk yanda taso fita zuwa gun Sultan abun ya gagara , domin Daddy yasa ido sosai a kanta.

Ashwan yayi bugun duniya amma sam Sultana tak'i amsan ko naira a gunsa tace bata buk'ata yanemi mabuk'ata ya basu , hakama tak'i raba katin bikin , bawan da ta gaiyata sai k'awarta Zahra da tazama dole , saidai momy faty tayi gaiya ba kadan bah , danko jere ma dangintane sukayi...

Yau dai Zahra tasa Sultana a gaba akan dole ne suje koda Saloon ayiwa Sultana gyaran gashi da kuma sauran abunda ba a rasaba , a matsayin tana amarya  , amma Sam tak'i saida Zahra ta nuna 6acin ranta sannan Sultana ta yarda zatayi.

Gun Daddy taje ta shaidamar akan zataje Saloon ya bata kud'i, Amma daddy ya 6ata rai yace taje gun mijin ta ya bata , sannan baiyarda taje ko inaba sai tare da mijin tah...

Sultana komawa d'aki tayi ta shaidawa Zahra akan tafasa zuwa , cikin kulawa Zahra ta ringa bata shawara akan tayi hak'uri ta Kira Ashwan ya kaisu.

Da farko taso taki Amma sai tayi wani tinani akan gara taje , daganan tasan yanda zatayi taje gun Sultan .

Nanda nan taciro phone dinta ta fara binciken number din Ashwan a cikin sharan da ta zuba shi , ta koci sa'a ta gane number d'in bata 6ata lokaci ba ta danna kira , saidai harta tsinke bai daga bah....

Bayan kaman 20minutes , Ashwan ya kira , anan Sultana ta shaida masa abunda take buk'ata , kamar bazai amsa ba sai kuma yace

"Ohk gani nan zuwa....

Ba jimawa Ashwan ya iso gidan harda K'anwarsa Safna, koda wasa Sultana bata kalli inda Safna take ba saima kallon banza da take watsawa Safna duk sanda suka had'a idoo.

Koda suka isa gun cewa tayi Ashwan yaje ya dawo kafinnan an gama musu.

Ashwan fita yayi daga gefe ya samu waje yayi zaman sa , yana jiran a gama su wuce...

Sultana cikin dabara ta turawa Sultan text , kwatancen inda take tayimar akan yazo ya sameta .

Cikin 30 minutes Sultan ya iso wajen , koda ya kirata yace gashi yazo .

"Ohk... Kawai ta furta , suma su Zahra basusan me hakan yake nufiba , saidai gani sukayi tace a sake mata kanta tana zuwa tayi bak'o a waje...

Babu musu mai gyaran kan ta sake tah, Sultana tana fita da sauri ta shiga motan Sultan suka wuce, daidai lokacin Ashwan yakai idon gun ita kuma ta shiga tana k'ok'arin rufewa .

Itama Safna fitowa tayi domin ganin ko waye yake k'iran Sultanan , ganin tashiga mota sun tafi ya sata zare ido , Ashwan ne ya mata nuni da tazo su bi Sultanan, da sauri Safna tazo sukabi bayan motan da Sultana take ciki....


https://www.facebook.com/groups/1045601149137505/

*My Facebook Group*
🖕🏼

*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now