56 too 60

115 5 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Wattpad*
*HaseenahNaseer*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.facebook.com/Xahrah-Farooq-Novel-110638730479676/

_______________________________

*Dedicated too*

*Noorul Hannerh* *love my dear*

*Special gift too my mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

*Note Editing*🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

*Page*

*55 too 60*


..........."Haba Daddy ai wasa ma kakeyi nasan bazakayi hakan ba , saidai in so kake mu k'ona gidan nida wannan wawan yaron , tab nice zan auri wannan jakin?" , Kawai saita kwashe da dariya.

Alhaji Musa wanda tinin ransa ya gama 6aci game da furucin Sultana , tsawa ya daka mata "keh....agabana kike fad'in wannan zancen saboda baki da kunya?", Sam ni ba sa'an ki bane kuma dole ki auri Ashwan domin shine za6ina , badai kince bazakiyi karatu ba aure zakiyi toh ga miji na samo , kuma nan ba  jimawa zan aura mar tunda yana so , banason shashanci ai nina haifeki ba kece kika haifeni ba suna kikaci kawai....

Duk wannan abunda Daddy yake yi d'in ba har cikin ransa bane , yayi hakan ne dan ya samu Sultana ta yarta ta auri Ashwan domin yana hango mata hutu acan yasan yaron zai rik'e ta amana, kuma daga ni yana da hankali, uwa uba zumuncin su zai k'ara k'arfi da Alhaji Hussain , kuma ta hakan ne zai samun daman sake shiga jikin sa har yakai ga samun kwangilan da yake nema agunsa na mak'udan kud'i...

Ni kuma araina nace Daddy ai wannan shirme ne , son da ka nunawa Sultana ya zama na banza tunda naiman kud'i zakayi da ita , shiysa idon ka ya rufe kake shirin aurar ta babu bincike...

Sultana ganin Daddyn ta cikin matsanan cin fishi yasa ta tsorita tare da sakin ihu!, Wajen momy faty ta nufa da gudu!, "Momy faty ki taimaka min please Daddy auren dole zaimin wallahi banaso Dan Allah ki bashi hak'uri , wallahi ni na tsani wannan wawan bazan iya zama dashi matsayin miji ba , Daddy yabar Sona , shikenan na shiga uku wayyoo Allah nah please please help me out...ta Kai k'arshen maganan tana shashshek'an kuka!..

Momy faty zuciyan ta a wanke tas , sa boda tsananin farin ciki na abunda idonta yake ganin , ta kuma ji dad'in hakan sosai sannan wannan wata dama ne ta samu na zuga Sultana akan ta bujirewa Daddy , kuma ta shirya tsaf domin bawa Sultana duk wani gudun mawa na yanda zata shiga tsakanin ta da mahaifin nata, "haba Sultana kibar kuka insha Allah komai zaizo da sauk'i mahaifin ki bazai cutar dake ba yana tsananin sonki ki daina kuka zanyi magana tashi kinji Koo , maza tashi kije d'aki gashi har jikin ki yayi zafi bari na samo magani shiga , momy faty cikin ranta cewa tayi shegiya wama zai baki Ashwan d'in har kike wani kuka akansa , ai saidai ki hangosa a nesa....

Daddy parlon ya bari ya nufi d'akin sa domin kuwa idan akwai abunda yafi d'agamar hankali to bai wuce kukan Sultana bah .

Itama Sultana nata d'akin ta nufa cikin kuka da tashin hankali marar misaltuwa.

Momy faty cikin farin cikin ta Kira Zainab domin su tattauna akan lamarin , dole kuma su koma gun malam da wuri tunda ya fara cewa auren da wuri za'a yisa....

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now