131 too 135

83 7 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Gmail*
xahrahfarooq@gmail.com

*Wattpad*
*XahrahFarooq*
https://my.w.tt/q5NpdRP3L7

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Snapchat*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

*YouTube Channel*
*AL'UMMA TV*

https://youtu.be/vRkcRYYZdtA
بسم الله الرحمن الرحيم ___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

https://www.facebook.com/groups/227620608315825/permalink/254851642259388/

*Special Gift too my Mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

     *Note Editing*🤦🏼‍♀

*Page*

*131 too 135*

.......Acan asibiti kuwa Zainab ce kwance kaman gawa , dak'er doctors suka yi nasarar ceto ranta , tasha wuya sosai Safna k'anwar Ashwan ita ke jinyan Zainab , dan duk cikin dangin Zainab bbu wanda yazo asibitin mahaifiyar Ashwan kullun tana zuwa duba ta , Zainab ko da wasa bata yi gigin sanar da iyayen Ashwan abunda ya faru ba dan tana mugun tsoron sa , haka shima Ashwan ce musu yayi wai fad'uwa tayi saidai duk mai hankali yasa ba hakan bane tunda duk jikin tah shatin duka ne .

Kwanan ta hud'u aka sallamesa daga asibitin , ta dawo gida , abar mata Safna akan ta tayata zama zuwa wani lokaci dan daman Ashwan zaiyi tafiya ya dai cewa iyayen nasa zaije k'aro ilimi ne agun aikin sa an tura sa wani course .

Ita kam Zainab taji dad'in hakan sosai zata futa nadan lokaci, murna ta shiga yi sosai dan har abun ya bawa Safna mamaki tayi magana ,"haba Aunty Zainab mijin ki zaiyi tafiya amma sai murna kike yi , ni dai idan nayi aure mijina zaiga kula zaiga tarairaya dasoo ba wlhy.

Dariyan kafin kuka ciwo Zainab tayi , tare da wayen cewa ta sanja zancen zuwa wani hiran daban .

Washe gari Ashwan yabar k'asan .

Ita ma Sultana a nata 6angaren bayan ta gama had'a komai da ya shafi girkin da tayi , kai tsaye daining table ta kai ta jere su , sannan ta kama gaban ta tunda daman baci takeyi bah .

Saidai matar gidan da yaran gidan suka fito cin abinci ne suka fara kallon kallo , dan a kullun ana musu girki ababu kala uku kowa ya ci wanda ya ke so , amma yau kula kala d'aya ne bbu k'ari.

Amir ne ya bangaji Mufida , "ni kam batsa min yunwa nake ji nawa aka gama sauran naku.

Mufida hanu ta d'aga za ta kai masa duka! , da sauri ya matsa yana sosa k'eya ta da cewa "haba Aunty ni ne fa.

K'wafa tayi tare da jan zaki , ta ce "to sai meye ?".

Amir ya ce "sai kiyi hak'uri nake nufi ai.

Hmm! kawai ta ce suka k'arisa gaban table d'in.

Ummy kam tinin daman taje gun ta bud'e flast dan ganewa idon ta ko me aka girka , abun da ta gani yasa ta yin shiru kamar me tinanin wani Abu.

Bayan isowan su Amir ne tayi magana , " ni fa bnga food d'in bah , anya wannan yarinyan tana da hankali?" , Ko ni sa'arta ne?".

Da sauri Mufy ta ce "Ummy me ya faru?".

"Meye kuwa idan banda wannan shegiyar yarinyan , abunda tayi takai k'arshen maganan tana nuna kulan abinci.

Mufida bud'ewa tayi dan ganin meye a ciki , a fili ta furta "kan ubannan wannan girkin ta mana amma ta raina mana wayoo.

Ummy ta ce "kai Amir maza je ka kira min ita kaji ko.

"To ya amsa , sannan ya ruga da gudu ya nufi 6angaren da take.

Ba'a d'au lokaci ba suka shigo tare .

"Gani Ummy tayi maganan tana dafe kanta wanda yake ciwo kamar zai fad'i.

Harara Ummy ta watsa mata sannan ta ce "ina girkin?".

"Shi ne wannan Sultana tayi magana cikin k'arfin hali .

"Abunda na saki kenan?", Ummy ta jefa mata tanbaya.

"A'a kiyi hakuri dan Allah , Ummy wlhy shima dak'er na yi shi , take k'arshen maganan tana mai rushewa da kuka!....

Ummy taso tayi masifa sosai amma kawai sai taji tausayin yarinyan yazo mata , shiru tayi bata sake cewa komai bah.

Sultana taci gaba da tsayuwa agun , sai da Mufy ta daka mata tsawa sannan ta fice a d'akin ta kama gaban tah.

Mufy tsaki taja! , Sannan ta bud'e food d'in ta fara d'i ba , dan mugun yunwa take ji , haka shima amir.

Ai kuwa loman farko abinci ya kasa had'iyuwa Mufida sai amai , shima Amir zubar da na bakin sa yayi sannan ya ringa wanke bakin.

"Tab lallai matsaln babbane Ummy ta furta a fili cikin 6acin rai , abincin ta d'and'ana ai kuwa da sauri ta zubar agun .

Waya ta ciro ta Kira masu aikin da tace suje gida dan ta gane ba abunda Sultana ta iya.

A ranan da kanta ta shiga kitchen ta had'a musu abinci , washe gari yan aikin gidan suka dawo , yanzu ta sake juya aikin Sultana shara da wanke wanke wankin band'aki , sharan d'akunan gidan .

Sultana tana mugun Shan wuya saidai bbu yanda ta iya dole tayi , ta rame tayi bak'i duk ta fita a haiyacin ta idan ba wanda ya santa sosai ba bazai gane taba , cikin yana mugun bata wuya ba komai take iya ciba kuma bbu wanda zai bata abunda take so a gidan saidai ta saya da kud'in ta , toh yanzu duk yan kud'in ma sun k'are hatta wayan hanunta ta siyar bata da wani madogara a yanzu , kullun tana cikin kuka wai yau ita Sultana na ce ta dawo hakan ?" , Lallai wannan shi ake kira da *Juyin Rayuwa*, anya mahaifin ta bashi ne ya zalunceta bah , tanbaya da yawa take yiwa kanta amma bbu amsa dole tayi shiru, aiki kuma basai anyi magana ba tun asuba take farawa ba yanda ta iya , lallai dangi suna da amfani a yau inda ta sansu da taje gunsu Amma bata sansu ba.

Abu kaman wasa cikin ta sai k'ara girma yake yi , Abban Sultan baya kula da yanda duk ta sanja kala a tinanin sa cikin ne yake bata wuya , kuma duk ganin da zai mata da himar a jikin ta , kuma har cikin ransa ya d'auka Ummy na bawa Sultana kulawa , dan shi tunda yaga bata sake mar zancen ba sai kawai yace ta saki ranta ne zuwa suga me Allah zaiyi besan ba hakan bane....

*Vote*
*Comments*
*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now