21 too 25

132 4 1
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Wattpad*
*HaseenahNaseer*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_____________________________

*Dedicated too*

*REAL MARYAMA*

*Ina tayaki murnan kammala book d'inki mai suna*
*K'WAD'AYI NE SILA!💔💔💔💔💔💔💔* *Sai mun jiki a sabon book Allah ya k'ara basira*

*Special gift too my mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

*Page*

*21 too 25*

..........Kuluwa taja ta tsaya tana kwasar dariya agun , tsananin dariya saida ta zube har k'asa tana k'arewa tsofin nan kallo sannan taja tsaki tace "shegu maganin ku kenan ai , baku da aikin sai zaman majalisa kuna k'arewa muta ne kallo , tsofin banza kawai bice maganin ku a wannan k'auye , dariya tasa sannan ta d'ibi zugarta suka k'ara gaba.

Daga nan kai tsaye gonar malam iro sukaje tsinkan kashu , suka sha na sha suka zubar da sauran agun, sannan masaran cikin gonan suka ringa tsinkewa suna zubarwa ,acewar ita Uwar gaiya Kulawa suna rage mar aiki ne, ni kuma nace rage aikin ko 6arna🤔🤔, masaran da bata ko nuna bah...

Washe gari malam Iro ya shigo gona ya tararda mummunan aikin da akamar ko ba'a fad'a mar ba yasan wannan shaid'aniyar yarinyan ce tamar,kuma bazai yarda ba yanzu ba sai anjima ba zaije gun ubanta , abiya sa duk 6arnan da akamar bazai d'au asara ba , domin bai gaje tabah...

Gidan su kulawa yaje Kai tsaye , yana isa ya ringa doka sallama daga soron gidan , malam Garba ne ya fito da sauri yana magana kasancewan ya gane muryan abokin sa"haba malam Iro me yayi zafi haka ?" , Kana ta faman kwad'a min shegen kiran naka kamar wani makahoo.

Hmm! "barni kawai , wallahi y'ar wajen kane takwashi yara suka je gonan suka min 6arna ba ta wasa ba , baka ganni duk a birkice bah?".

"Subhalallahi kulu kake nufi Wai?" .

Ita dai kasan ai d'ayar kan baza tayi hakan ba , ita dai wannan itace shaid'aniya.

Kafin ya rufe bakin saiga Baba Lantana a cikin soron , yatsa take nunawa kamar zata tsolewa malam Iro ido , " kaganka wallahi kar ka sake ka aibata Kuluwa dan wallahi bazan yarda bah , kayi abun gaban ka banason sa ido duk kun hana yarinya k'iba to ta Allah ba taku ba....

Malam Garba dai kunya kamar zai ni tse cikin k'asa ,duk da cewa wannan ba sabon abu bane agun sa , kama hanun abokin nasa yayi suka bar gidan ba tare da ya sake cewa komai ba....

Duk abunda suke yinnan Kuluwa na jinsu , ta kuma sake shirin abunda zata yiwa malam Iro domin ya shiga hankalin sa , ya kuma san tafin k'arfin sa....

Ko'a jikin ta bata damu da k'aran da aka kawo nata ba , rana tana d'agawa Kuluwa ta saita lokacin da za a samu malam Iro a gona , Kai tsaye ta biya ta gidan su k'awar ta delu ta d'auke ta domin yi mata rakiya , basu zame ko ina ba sai cikin gona , malam Iro nata faman aiki ga rana Kuluwa ta sand'a a hankali ta isa har bayan sa , wata leda ta bud'e wani gari ne ya baiya na daga laida d'in wani abu nagani Wanda a ke Kira da goga masi , nidai zare ido nayi ina dubanta tare da cewa yau kuma Iro ka banu 😷.

Kuluwa saida taje kusa da shi sannan ta ringa furamar a jiki , ai ko zo kuga tsalle agun ihu ya ringa yi tankar k'aramin yaro yana neman d'auki , haka ya ringa tsalle agun.

Kuluwa hanun Delu ta kama suka bar gun suna kwasan dariya.

Delu ta dubi Kuluwa tace " gaskiya K'awata baki da kyau , mutun ya guji sharrin ki .

Hmmm! "Kedai bar shege , harni zaikai k'ara gidan mu ai shiysa nayi maganin sah.

A wannan karon malam Iro ai ko k'ara baikai gidan su Kuluwa ba , dan cewa yayi yafi tinanin yarinyan ba mutun bace, saida yayi kwana biyu baije gona ba sannan ya koma.

*Kaduna*

Bayan tafiyan sultan karatu da kwana biyu , mahaifin Sultana ya dawo daman ta matsu da ya dawon dan duk gidan ya mata zafi ba mai kulata ga Sultan ya tafi ya barta bare su hadu ya d'ebe mata kewa, ko wayan ma basu yiba tunda ya tafi.

Sultana ce baje a gaban daddy tana bashi labarin abunda suka faru da ita bayan tafiyan sa , Wanda hakan yasa harta rame kuma shima daddy yaga raman , ransa yayi bala'in 6aci kuma ya yarda babu mai iya kulamar da d'iyar tasa , cikin 6acin rai ya had'a mutanen gidan gaba d'aya yaringa sauk'e musu ruwan bala'i .

Hajiya Maryam ya kalla tare da cewa "kekan ai kinyi babbar asara , ace d'an cikin ka kakewa wannan aikin , kin tsane ta meye ta miki?" Akan meye haba Maryam a gaskiya kina bn mamaki...

Hajiya Hauwa ce ta fara magana cikin 6acin rai , gaskiya Alhaji mun gaji da abunda kake mana akan wannan jaririyar yarinyan naka , yarinyan kamar y'ar ido?"  Wata fi ?" K'iri k'iri kake nuna banbanci acikin yaran ka zaka sa su tsane ka , idan hakan ya faru me kayi kenan?" haka zata rayu ba tarbiya ?" Sannan babu karatun addini ?"....

"Keh..... Hauwa dakata , manason kina aibata min yar cikina , Alhaji ne yayi maganan cikin 6acin rai .

Sultana ce tayi gyaran murya sannan ta fara magana cikin kuka!! "Daddy na gaji da abunda akemin a gidan nan meysa suka tsaneni?" Daddy anya mamy ce ta haifeni?" , Tayi maganan tana mai tsare mahaifin nata da ido...

"Ummy nah wallahi itace fa ta haife ki , badan ke take nuna wannan k'iyayyan ba , sabo da nine dan naji zafi amatsayin ki tamai dunan mahaifiya ta , kuma mai kama da ita...

"Ohk daddy kabar damuwa , amma inason na ne mi wata alfarma agunka.

"Ohk ina sauraron ki..

"Daddy inason ka k'ara aure kodan na samu abokiyar shawara ,kuma mai sona......

*Gyaran jiki*

*Kurkum na dauke da sinadarai da dama kamar su, bitamin B6 da bitamin C da sauransu. Kuma yana rike fata yadda ba za a sami rauni . Yawan amfani da hadin kurkum na sanya fata musamman ta fuska laushi da santsi da kuma haske. Don haka, ya kamata kada a manta da wannan kurkum idan an zo kwalliya. ta zama sakakkiya ba. Amfani da kurkum na sanya sabuwar fata fitowa da wuri a inda tsohuwar tAmina Abdullahi*

*A sami garin kurkum da zuma cokali daya da ruwan lemon tsami kwatan kofi. A kwaba su sosai har sai sun yi laushi. Sannan a shafa a fatar fuska a bari ya jima na mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin wannan hadin na hana kurajen fuska fesowa. Za a iya yin wannan hadin kamar sau daya ko biyu a sati domin samin ingantaccen sakamako*

*Amfani da kurkum na rage gautsin fuska. A kwaba kurkum da nono ko kindirmo. Sannan a wanke fuska kafin a shafa hadin a fuska. A jira na tsawon mintuna 10-15 kafin a wanke. Za a iya jarraba wannan hadin a kullum bayan an yi wanka.*

*Idan ke mai yawan aiki a karkashin rana ce, ya kamata ki samu kurkum kadan da kindirmo mai yawa sai ki rika shafa wa a inda kunan rana ta bata fuska. kunan rana na sanya fuska ta zama kamar mai shafe-shafe don haka wannan hadin zai magance wadannan matsalolin.*

*Ko kun san cewa kurkum na magance bakar fatar karkashin hammata? To! A sami zuma kamar cokali daya sai a hada da ruwan lemon tsami kamar cokula 3-4 sai a zuba garin kurkum kadan sannan a kwaba a shafa a karkashin hammata a bari ya jima na tsakwon mintuna 10-15 kamin a wanke.*

*Vote*

*Comments*
       &

*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now