141 toO 145

107 6 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Gmail*
xahrahfarooq@gmail.com

*Wattpad*
*XahrahFarooq*
https://my.w.tt/q5NpdRP3L7

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Snapchat*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

*YouTube Channel*
*AL'UMMA TV*

https://youtu.be/vRkcRYYZdtA
بسم الله الرحمن الرحيم ___________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

https://www.facebook.com/groups/227620608315825/permalink/254851642259388/

*Special Gift too my Mom Sawda Edriss (the writer of Sirri)*

     *Note Editing*🤦🏼‍♀

*Page*

*141 too 145*

......Nan fa allura ta tono garma, sirrin da suka rufe yau ya bud'u lallai son zuciya bashi da wani rana ko ribah, lokacin da aka kai Sultan asibiti bayan Ummy taji abunda ya faru har Sultan ya fad'i taji bak'in ciki bana wasa ba , sannan taji tsanan Sultana sama da komai acewarta Sultana ita ce ta 6ata Sultan saboda abunda idon ta ya gani tun had'uwar su a airport, hakan yasa ta kasa zaune da tsaye shine ta kira k'awar ta Aminiyar ta wato Hajiya Kubra akan ta nema musu mafita dan sun jima da son had'a yaran nasu aure wato Sultan da fauziya y'ar gidan Hajiya Kubra , shi Sultan bema san yarinyan ba itace dai take haukan sonsa, Uwar ta kuma kullun tana cikin bin malamai dan ganin cikar burin su, bawai burin Hajita Kubra ta taimakawa Ummy ba itama cikar burin d'iyar ta kawai take fata, shiysa tanajin zance a hotel aka kamasu da waccer yarinyan tayi alwashin ko ta yaya saita raba su kawai , Dan haka ta kawo shawara ita kuma Ummy ta kar6i shawara da hanu biyu....

Nan suka fara tinanin zuciyar waye za a sanjawa Sultan basu taba tinanin sanja zuciya zai shafi cikar muradin suba , a tinanin su idan an sanja shikenan duk wani son da Sultan ya kewa Sultana ya k'are ashe ba haka bane hausawa sukace wasa farin girki.

Kud'i mai yawa aka bawa dctr kafin ya amince da k'udinsu , sannan yace musu baza a samu matsala bah.

Lokacin da Ahmad saurayin zainabu yazo birni kana ganin sa kaga rashin wayewa kasan bak'o ne , kwanan sa biyu a garin kaduna ranan yahau titi da nufin zallakawa kawai aka bugesa Wanda ya bugesa ya dagashi zuwa mota suka wuce asibitin , Ahmad ba mutuwa yayi ba sanjin zuciya kawai aka mar sannan yanzu haka yana rayu baya dai k'asar ne yana wani wajen dabn a kar'k'ashin kulawar su Ummy allura akamar a wancan lokacin sai yayi dogon suma , alokacin da Sultan ya farka da tinanin Ahmad nason Zainabu hankalin Ummy yayi bala'in tashi dan har tace anemo Ahmad ya dawo asake sanja zuciya , amma sai dctr yace baza ayi hakan ba abari a hankali komai zai dawo normal.

Hajiya kubra taji haushin wannan lamarin amma bbu yanda ta iya dole , dole tasa ido saidai tana ta faman shiga malamai a kullun amma har yanzu ba a dace bah.

Mufida tana jin duk sanbatun da Mahaifiyar ta keyi , itama tashiga rud'u da tashin hankali , ana cikin hakan taji fad'uwan mutun juyawan da zata yi sai ganin Ummy tayi a zube a k'asa.

Wani k'ara tasa cikin sauri ta fara Kiran sunan Ummy amma shiru , da sauri tashiga takira doctor yazo Ummy bata san inda kanta yake ba ahaka aka shigar da ita d'akin taimako gaggawa , jinin tane yahau sosai.

Mufida waya ta d'auka tama rasa waye zata kira , Big Brother din ta tafara kira amma shiru ba a d'auka bah yakai 10 miscalls amma shiru , bbu ynda mufy ta iya dole ta kashe wayan ta ajiye, can kuma ta sake d'auka ta rasa waye zata Kira dan bata son kiran Abba tunda baya gari kar hankalin sa ya tashi , gashi wayan Ummy yana gida dole ta hak'ura ta zubawa saurautan Allah idoo.

Gado suka bawa itama Ummy dan jinin tane yahau sosai har ana tinanin ko tasamu matsaln shanyewan 6arin jiki .

Mufida ce agun mahaifiyarta , Larai agun Sultana duk ma tana bacci kuma bazata tashi da wuri ba dan anmata alluran bacci , shiysa ita ma Larai baccin tayi cikin dare ihun Sultana ya farkar da ita tana da wayyoo cikin ta zata mutu hankalin larai ya tashi sosai duk da ta nemo likita amma tana nan tana zubar kwalla , idan haka ta yanke hukuncin sanar da mahaifiyar Sultana halin da ake ciki tunda daman duk wani labarin Sultana Mamy tana samu ne agun Larai dan har kudi take biyan ta sunsan duk halinda Sultana ke ciki .

Sultana haka ta ringa juyi har a suba , anan ne kuma cikin jikin ta ya zube , ba a 6ata lokaci ba aka mata wankin ciki kawai danta futa gaba d'aya .

Asubar fari Mamy tazo asibitin gun d'iyar ta , ta shiga damuwa da yanda taga d'iyar tata , Allah ya sani tana son Sultana Amma mijin ta Alhaji Musa shine silan komai tabbas kar uwa taga ana fifita mutun daya acikin yaranta taji dadi dan ba abun farin ciki bane a raba maka kan yarah, yanzu duba yanda rayuwar yarinyan nan ta zama , bayan ya bata ta sannan ya guje tah.

Gari na waye wa takira sauran yaran ta suka hallara a hospital d'in, lokaci Sultana na bacci duk bata San abunda akeyi bah sai bayan da ta farka taji dadi sosai tanemi yafiyar su ta zubar da hawaye ba Kad'an bah lallai Dan uwa duk yanda yake akwai dadi .

Bayan farkawan Ummy abunda ta fara yi shine neman doctor din da ya yiwa su Ahmed canjin zuciya , ya kuma zo ta bada umarnin a dawo da Ahmed , da farko dctr din yaso yak'i saboda gudun fitowan maganar nan fili Amma ganin ta rikice masa yasa shi yrda Ahmed zai dawo, saidai sun makara domin wani dctr ya jisu.

Sultan anashi bangaren ashe yana gida bashi da lafiya duk ya birkice kuma yace bazai je hospital ba sannan baza a sanar da iyayen sa bah, Zainabu ido ta sa mar dan bayn da zata yi da shi.

Saida yaga bbu sarki sai Allah ya amince suje hospital d'in , suna zuwa kuwa aka rik'esa , Ummy an sallame ta koda taje gun Sultana Mamy cewa tayi tabar d'akin basa buk'ar ta ta kama gaban ta haka dai Ummy tabr d'akin jiki ba karfi.

Wani ciwon kai ne me tsanani yake damun Sultan ashe zuciyar sane duk abunda ya manta yanzu suke dawowa, dadai alluran bacci ake mar saboda ya samu futu zuciyarsa ta futa , yaran ya farka da safe Zainabu ce a gefen sa yana bud'e ido ita ya fara gani sai binta da kallo yake da sauri ta taso zuwa gabansa tana mar sannu Amma kamar ke da bakya wajen , dama abun ya ishe shi sai ya daka mata tsawa! "Keh wace irin maiya ne ki barni banason ganin ki ha a , ina Sultana ?" Ita nakeson gani ki nemo min ita....

*Vote*
*Comments*
*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now