121 too 125

125 6 0
                                    

*💕JUYIN RAYUWA💕*
             💕💕💕
                  💕💕
                       💕

*Written By✍*

*FATEEMAH A.Y Umar*
  
  *✍(Zahra Faruk)*

*Gmail*
*xahrahfarooq@gmail.com*

*Wattpad*
*XahrahFarooq*

*Twitter*
*Official Xahrah Farooq*

*Snapchat*
*Official Xahrah Farooq*

*Instagram*
*Official Xahrah Farooq*

*Facebook*
*Xahrahh Faroouq*

*YouTube channel*
*AL'UMMA TV*

بسم الله الرحمن الرحيم
___________________________________

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

https://www.facebook.com/groups/227620608315825/permalink/254851642259388/
*My Facebook Group*

*Special Gift too*
*My Mom (Sawda Edriss*)

K'arin ni'ima
Kisamu sassaken baure ki dafashi sai bayan ya dafu sai ki juye ruwan sai kisamu mazar kwaila ,da zuma ,da kanunfari, da citta, ki zuba aciki ki tafasa kirinka sha safe da yamma hmm..zaki sha mamaki ....

*Page*

*121 too 125*

........Haka Zainab ta ci gaba da zama a gidan cikin k'uncin rayuwa , ta rame ta yi bak'i sai dai ta kasa gayawa kowa tabar abun a cikin ta , tunda Mom d'in ta bata kusa bare ta bata labarin abunda yake faruwa.

Sultan ya koma gida duk hankalin sa a tashe ga 6acin rai , Zainabu ce ta ringa kwantar masa hankali har yaji zuciyar sa tamar sanyi a lokacin.

Kwana biyu Abban Sultan ya d'auka yana binciken lamarin amma ya kasa gano bakin zaren , sannan be'isa ya ce Sultana taje gidan iyayen ta ba domin a gabansa akayi komai uban ta yace shi da ita har abada , to yanzu kuma ga wannan matsalan.

Sultana ce kwance a cikin bargo sai faman rawan sanyi take yi , k'ara min yaro ne ya fad'o dakin bako sallama , yanda ya bankad'o k'ofan ne yasa Sultana d'aga kai dan ganin ko waye, Amir ta gani k'anin Sultan , du bansa take ba tare da tace komai bah har ya iso gaban ta.

Tsawa ya daka mata! , "keh dalla ni dai ki daina kallo na , tunda Ummy na bata son ki ni ma ba sonki zanyi bah .

Sultana baki mud'e take sake duban yaron , sai dai bata ce komai bah .

Amir harara ya watsa mata! sannan yace "dalla kizo , Ummy na neman ki.

Yana kaiwa nan ya fice a d'akin ba tare da yaji me zata cebah.

Sultana ba abunda take yi sai zubar da wasu hawaye masu zafi , ga tsananin ciwon da take ji, dak'er ta iya mik'ewa jiki na 6ari! ta fito ta nufi side d'in Ummy.

Sultana tayi sallama ya kai baki uku Amma ba wanda ya amsa bayan tana jin hayaniyan yara a cikin falon , ciki kuwa harda Ummy .

An d'au lokaci kafin aka amsa mata, falon ta shiga daga gefe ta samu waje ta raka6e, sai faman rawan sanyi take yi .

D'aya daga cikin yaran da ke falon ne ta fara magana , "ke kuma dalla sai wani faman 6ari kike yi , da uban waye yace kiyi cikin aikin banza marar tarbiya, mufida kenan k'anwar Sultan yarinyan bata da kunya .

Mufida juyawa tayi da duban ta gun Ummy , "ni kam Ummy ba nason ganin k'azaman nan sallame ta maza ta bar falon nan.

Ummy ne ta gintse fiska sannan ta fara magana , "wai me kike nufi ne?" da kikaje d'aki kika kwanta uban waye kika ajiye zai girka miki abincin?"ko kina da bawa ne?" , To bari kiji gaba d'aya masu aikin gidan nan nace suje gida su futa zuwa wani lokaci sai kin bar gidan sannan zasu dawo , yanzu kece me yi.

Duk maganan da Ummy take yi Sultana ba tace komai ba , kanta a sunkuye tana zubar da hawaye , sai kuma rawan jiki , Ummy taga hakan amma sai tayi kaman bata gani bah , saboda tsanan yarinyan ya riga ya shige tah .

Ummy ce ta dakawa Sultana tsawa! "Zaman meye kike yi agun ?" , Maza tashi kije kitchen ki fara aiki.

Sunsun Sultana ta mik'e zata bar falon , saidai Ummy ta tsaida ita , saida aka bi kan yaran duka ana tanbayan su kowa ya fad'i me zai ci.

Haka yaran suka ringa fad'a, girki kala biyar suka lissafa.

Sultana ji tayi zuciyan ta ya tsinke! , dan tasan yau akwai aikin indomie kawai ta iya dafawa , duk girkin da aka lissafa bata san yanda akeyi bah....

Fitowa tayi ta nufi kitchen d'in tana ta sak'e sak'e a ranta domin bata iya komai bah , ita yar gata ce a gidan su lallai wannan ake kira da *juyin rayuwa*, ta jima a kitchen d'in ta na tsaye saidai ganin tana bata lokaci yasa ta nufan wajen da gas yake , ashana ta d'auka ta kunna saidai take taji kanta na juyawa saboda warin gas din da bata Soo , hanci ta shiga toshewa amai ne yazo bakin ta da sauri ta fito a kitchen d'in , durk'ushewa tayi tana kwara amai sosai , ta ke duk jikin ta ya sake mik'ewa tayi zuwa gunda fanfo yake tana tafe tana had'a hanya saboda jiri da take ji , dak'er ta isa gaban fanfo ta wanke jikin ta.

Amir ne ya fito ya ga yanda Sultana tayi amai duk gaban kitchen ya 6aci , komawa yayi da gudu ya fadawa Ummy abunda ke faruwa saidai ko a jikin ta .

Saima cewa tayi "ai kad'an ta gani badai cikin shege ba , ai da saura wlhy ba taga komai ba amah.

Sultana takai 1hour agun tana zaune , Sam ta manta da tasa ruwa a wuta .

Ummy ce ta fito zata wuce , idon tane yaje gunda amai yake kwance duk da ya ma bushe dan uwane kawai tunda ba abunda Sultana take iya ci sai moltina , kuma tunda tazo gidan bata samu bah, k'udan da suke bin kan wajen ne yasa Ummy ganewa anan amai d'in yake , dan Ummy mace ce mai masifan tsafta , ba tason ganin k'azan ta ko a wani gun bare kuma a gidan tah.

"Ai ganin wannan amai d'in Ummy batasan lokacin da ta furta kan uba , toh wa ta barwa ya gyara mata?".

Afusace ta nufi kitchen d'in saidai bbu kowa sai gas da yake kunne wuta nata faman ciii, ranta ya masifan 6aci fitowa tayi ta shiga d'akin Sultana saidai bbu kowa a ciki , ta fito zata wuce ta hango Sultana kwance a gun fanfoo, wajen ta k'arisa tana fad'a " ke Wai me kike nufi ne?".

Sultana a raza ne ta d'aga kai ta dubi Ummy , saidai ba tace komai .

Ummy ce ta sake daka mata tsawa "ba dake nake magana bah?".

Da k'er Sultana ta iya magana "Ummy bazan iya ba bani da lafiya neh....

*Vote*

*Comments*

*Shere*

*Love you all my Fans*
💕💕💕

*Xahrah ceh*🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀🏌🏼‍♀

*Show me love to Subscribe my channel*
*AL'UMMA TV*

JUYIN RAYUWAWhere stories live. Discover now