Typing🖊
BAYA BA ZANI🥥🥥🥥🥥🥥🥥
By
Fadeela Lamido
Wattpad fadilalamido✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*® _PEN: WRITER'S ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
17 -18
_______________________________________
.......Anne?, Ya tambayi kansa sannan yace"
Wanene Kuma Anne?
Kofar gidan ya kallah Babu kowa akofar gidan, shi daya ne, dan haka ya waiga ya Kira Abdullahi"
Wayar ya mika masa ga sako daga Maryam"
Amsan wayar yayi ya duba hade fuskan sa yayi dan gudun kar Dattijo ya gane komai duk da cewa dariya nacinsa"
Dattijo ne yace waye Anne?
Nutsuwa sosai Abdullahi yayi sannan yace, Ina tunanin kuskure ne, muje kawai"
A'a nikam bazan shiga ba, Ina jiran ka anan saika fito"
Kazo har kofar gida ka kasa shiga?🤔
Eh, kawai saina shiga cikin mata, yi sauri kazo muje, kudi ya ciro ya Mika masa kabawa Maryam din"
Gidan Abdullahi ya nufa yaso kwarai Dattijo ya shiga, motar Dattijo ya koma ya zauna lokaci zuwa lokaci yana kallon kofar gidan daga can ya hango Abdullahi yafito yana dariya, bayan sa ya hango wata na biye dashi"
Kallo yabisu dashi saidai Asma'u naganin ya nufo matar Dattijo taja ta tsaya"
Bejin abin da Abdullahi ke fadi Amman da alama lallashinta yake, kokarin gudu take harta juya Abdullahi ya rikota"
Yanayin abin da suke yaso yabawa Dattijo dariya saidai yaki yin hakan, daure fuskansa take tamau saidai cikin zuciyarsa abin yaba shi dariya, afili yace, mayyar yariyar nan ce, dake kadai ce gurin danabi ta kanki da mota"
Da karfin tsiya Abdullahi ya karaso da ita gaban motar yana rike da ita tamau yayin da take cijewa"
Bude bayan motar yayi yace oya shiga"
Karta shigo min nan?
Kallonsa kawai Abdullahi yayi sannan yacewa Asmau shiga muje nace ko"
Bakajin abin da nake cewa halan"
Yaya inaji gida zamu sauketa dan Allah"
Bazan dauketaba kashigo mu wuce Ina da abin yi"
Bata rai Abdullahi yayi sosai kamar me shirin kuka, shikenan kaje kawai sai nazo"
Shiga mutafi bason mgnr banza "
Daukan Asma'u Abdullahi yayi ya daura acikin motar yayin da jikinta ke buga uban rawa, juyawa yayi sannan ya zagaya yashiga gaban motar ya rofe tare da kin kallon Dattijo daya tsareshi da ido"