Typing🖊
BAYA BA ZANI🥥🥥🥥🥥🥥🥥
By
Fadeela Lamido
Wattpad https://my.w.tt/y43QcU2rh7✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*® _PEN: WRITER'S ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
______________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
_____________________________________https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
23-25
_____________________________________
......Abdullahi Wai meyasa bakajin kunyata ne?
Yaya Kai har kanason inji kunyar ka?, Idan bangaya maka ba wazan gayawa, nasamu yariyar da nake so mun daidaita Kuma har nagayawa Baba ya kuma ce za'aje gidan su"
Kai Alhamdulillahi naji dadi daka sanar da Baba da kanka, dan waccen karon nakai kaina ne kawai atada tsohon lbr, yanzon kasan mene?
A'a saika fada"
Bazan zoba har sai naji ansaka maka rana Dan ma kar Baba yayi tunanin matsa min har nayi wani aure"
Hmmm Amman Yaya yaci ance kayi aure"
Zanyi Abdullahi, ai dole nayi kodan farin cikin iyayena amman idan tanine bani da matsala ko kadan, shikuwa Baba ya dauki abun da zafi nan gaba kadan yana iya tsine min idan banyi ba"
Kwarai kuwa Dan gaskiya yana fushi karai dakai daurewa kawai yake yi"
Hmmm, ban da abin su Suma dai, nifa zan zauna da yariyar, idan har yana ganin auren gata ne ni bana ganin shi agata, kawai nauyi ne mutum zai daurawa kansa"
Cikin tsananin Mamaki Abdullahi yace"
Nidai Yaya gaskiya kana bani mamaki, waikai wanni irin hallita ne?🤔
Dariya Dattijo yayi, sannan yace ni mutum ne kamar kowa, amman nafi karfin zuciyata, ko tana son abu ina hana mata"
Kwashewa Abdullahi yayi da dariya sosai, Dattijo ma dake sauraronsa murmushi yakeyi, tare da fadin dariya nabaka?
Eh mana har wani hana mata kakeyi, gaskiya na zaku in ganka da mata, zanci dariya kila har cikina ya kulle Yaya bazaka wani iya soyayya ba, ko Yaya zaman zai kasance?
Hmmm, ai nima bace maka nayi na iya soyayyar ba, ni ai ban santaba, ban tabayi ba Kuma bansan ya akeyi ba, kawai dai nasan mutun nagani yariya ne yaji yana son ta, kenan soyayyar ita ke kirkiro kanta, ko nace Allah ke dasawa mutum son wata cikin zuciyarsa idan soyayyar tayi tasiri sai ta bayyana kanta, toh ni har yanzun Allah be nuna min yariyar data dace Dani ba"
Dariya Abdullahi ya sake yi"
Hmmmm nifa Abdullahi ka dameni Kanata sani surutu gashi ka hanani aiki harna fara jin Bacci"
Shikenan Yaya bara na barka haka"
Sallama sukayi, sosai yaji yasamu nutsuwa dalilin barin tunanin Asma'u da yayi na Dan lokaci, bacci ya daukesa me dadin gaske"
Washegari Alhaji Babba da Baban Asma'u sukaje nemawa Abdullahi auren zainab Basu wani sha wahala ba, nan aka tsaida mgn kansancewar sun san juna da Baban Zainab din tun tuni"