part 12

32 2 0
                                    

💋💋💋💋💋
LALACEWA
💋💋💋💋💋

STORY AND WRITTEN BY
RUKKY

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

G.W.F

HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT AND EXPERT WRITERS WE ARE THE BEST AMONG THE REST.......

DEDICATED TO RUKKY NOVELS FANS

NAGODE DA KAUNAR DAKUKA NUNA MUN NIDA NOVEL DINA INA YINKU MAKARANTA WANNAN NOVEL NAGODE DA ADU'A.

51

Yana nan zaune har ta fito daga toilet din ta nufi kan gado ta kwanta daman tasa kayan bacci bayan shiganta makewayin.

Suraj kallon ta yayi kawai ya girgiza kai dole ne ya tashim ma yar nan zaune cikin dabara yenzu zai sarara mata ya daina neman jikinta har sai ta kara yarda dashi.

Tashi shima yayi ya shige toilet din yayi abunda zaiyi ya fito jalabiya yasanya shima ya wuce kan gadon ya kwanta.

Juya idonsa yayi kanta wanda ta juya masa baya daman saida ya kirata sau uku sannan ta ansa ta juya da face dinta gunsa

"Na'am"

"nafisa kiyi hakuri inshallah babu abunda zai kara shiga tsakaninmu gobe inshallah dakin koma gida next week zanzo in gaida mama".

Kallan shi tayi sosai "dagaske kakeyi suraj".
"Inamaki wasane my love dagakse nikeyi auren ki zanyi nafisa saboda kidaina sa wani tunanin a ranki".

"Allah ya kaimu tou dakuwa naji dadi".

"Amma kaman face dinki bai nuna jin dadin ba"

"A'a naji dadi mana Allah ya kaimu" ita kanta tarasa dalilinta da batawani ji dadin maganar tasa ba amma kuma tasan wannan shine abunda yakamata suyi dan kuwa wannan zaman na bariki bazai dada masu komi.

"Amin " suraj yafada ya juya ya kwanta yana tunanin Allah yabasa sa'a akan nafisa,rufe idon sa yayi wanda bai dade ba bacci yayi gaba dashi.

Ita kuwa nafisa juye juye tadungayi tarasa mike damunta tayi tunanin yafi uku cikin lokaci daya da tunanin kazeem daya adabi rayuwarta wanda ta rasa dalilin haka dakuma tunanin maganan suraj dakuma tunanin zunubin da suke dauka ita da suraj.

Tashi tayi kawai dan neman makanta mafita toilet ta wuce dan yin alwala.

Bayan tayi alwala ta fito daga toilet

Dadduma ta dauko ta shinfida  tafara nafila tana rokan yafiyar ubangiji wanda data gama zamatayi tana tasbihi.

Sai gurin karfe 3 sannan ta tashi ta koma kan gadon sanna bacci ya kwashe ta.

Sai gun 6 suka tashi sukayi sallahn asuba suna iddar da sallahn nafisa ta matsa mai akan itafa yakai ta tasha takosa taji ta a zaria.

"Haba baby kaman kingani dani "

"Suraj inaga baka gane minike nufi ba bawai nagaji dakai bane aa inason kawai inkoma gidanne".

"Tou shikenan yaushe zanzo gunki"

Kallonshi tayi "bakaace zakazo gun mama next week bah".

"Uhm hakane Allah ya kaimu shirya inkaiki to ki hau motan".

Tashi tayi tashiga toilet tayi wanka fitowa tayi ta shirya cikin kimono dinta  white and red mai zannan Flowers green.

8:00 Am

Shidai har ta fito harta shirya bai ma lura ba dan tunani ya isheshi na yarda nafisa keson jamasa zance wlhy.

"Mutafi ko " tafadamai tana jawo akwatinta.

"Tou" yafada ya dauko mukullin motan shi suka fita daga dakin reception ya wuce ya mika masu mukullin dakin suka wuce wajan hotel din.

Mota suka wuce suka shiga ya mata key suka fita daga haraban gun.

Suna gab da isa kawo taji wayanta na ringing daukowa tayi ta duba

Mamanta tagani na kira nan take taji gabanta na fadi

Rage karar volume na wakan motan tayi ta dauki wayan shidai suraj tukin sa yakeyi yana jin haushin yarda bai wani kawashi ganima ba yarda yakamata zuwan nafisa kdn nan.

"Hello "tafada
"Hello nafisa kinajina"

"Eh umma inaji ina kwana ".
"Lafiya lau ya makaranta".

"Alhmdullilah umma dama yau nike niyan zuwa gida inshallah zuwa yamma"..

"Yawwa damma dalilin kiran nawa kenn ki daure yau kizo akwai wani magana ne danikeson miki kuma dole sai kinzo bai fadu a waya ba".

"Tou umma inshallah zan zo anjiman".
"Allah kaimu shikenan"
Kashe wayan sukayi ita kumata kalli suraj "kaga ko umma ke nemana gara ashe da zan koma yau "

"Uhm hakane"

Abunda yafadi kenn daidai suna karaso wa tashan ".

Aljihun sa yasaka hannunsa ya dauko kudi wanda zaikai kaman dubu hamsin  ya aje mata akan jikinta.

"Tou ga wannan kima mama tsaraba "

Dauka kawai tayi ta fita daga motan batare da tace mai komi.

Shima fito wa tayi dan dauko mata kayan tadaga boot.

Mika mata kayan yayi ta karba shikuma ya wuce gun masu motan dan neman mata mota shata ita kadai.

Aiko yana zuwa ya samu kuma akayi dace motan mai kyau.

Zuwa yayi yamata magana suka wuce akasa mata kayan a mota sai sannan ta kalleshi "shikenn baby  sai munyi waya thank you".

Smiling kawai yamata ya rufe murfin motan ya wuce gun motansa.




Typing🤳🏼

LALACEWAWhere stories live. Discover now