shafi na goma

70 9 2
                                        

**  👩‍❤️‍👨AUREN ZAMANI👩‍❤️‍👨**

WRITTEN BY  RUKAYYA IKRA (UMMU SULTAN)

WATTPAD@IKRARUKAYYA11

DEDICATED TO
 
UMAR ABUBAKAR(DADY UMAR)

SPECIAL GIFT TO

KAWATA HINDATU MUSTAPHA🥰😘

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

*SHAFIN NAKU NE, MAMAN NANA FATEEMA, MY NUSEEY, MUM YUSEEF, MAMAN HANEEF, UMMA, USMAN IBRAHIM, WASILA USMAN, SHALELEN ABBAH, MAMAN MOMCY, DASAURAN DUK WANDA BASUJI SUNANSU YAYAN TAFE INSHA ALLAH INA GODIYA👏👏 😘🥰😘🥰😘💃💃🌹🌹*

            SHAFI NA  GOMA

📚🖊️.....tayi shiru tan juyayin tambayar malama rabi,

"Wallahi malama takaici ne kawa da kuma damuwa, musamman idan natuna yarda naja mata kunne sosai, maigaɗin gidansa da kansa yake sheda mani burin sa akan yasmeen, dan ya jishi suna waya da ƙanwarsa",

Dukkansu suka nisanta mlm rabi tace " tabbas mamy  akwai ɓacin rai, amman matakin dukan bashi bane mafita, babu abinda yafi addu'a da kuma janta jikinki sosai shine zaya fiddata daga cikin irin wannan halin, amman hantara kora duka bazasu gyara lamarin ba, kinga da zaran kin duketa badan tasan salma ba, zata iya komawa gurinsa, musamman idan kikace tabar gidan,

Babanta kuma yarda kika share batunsa alhamdullahi naji daɗin hakan, ki kara rike yaranki dan suzamar maki jigo zuwa gaba,

Sanan sana'arki karda kiyi wasa da ita, munada reshen da muke juyama marayu kuɗaɗansu da kuma kuɗin tallafi, zamu baki jari da kuɗin tallafi wanda za ki buɗe shago babba kina zuba hajarki, za mu maki hanyar mutane mata manya sosai insha Allah,

Ki kama yaranki dan Allah, kifita harkanshi gaba ɗaya, duk sanda yazo maki kiyi marhaba garéshi;

karda kisake kibari namiji ya gane kina cikin dawa kuma ta sanadin sa, toh daganan zaya sami kafar cutar dake da kuma  samun hanyar kara gallaza maki",

Ammi ce tasa bakin ta, "tabbas ni shedace kuma ganauce ba jiyau ba akan harkan mazan, kibishi karda kimasa rashin kunya ko fatan tsiya, domin Allah ya isa ga miji yana bala'in cutar da iyali dan ba kansa kaɗai take tsayawa ba harta ku za ta shafa,

Sabida bakisan inda Allah ya isan zata tsayaba, zata iya tasiri akan wani abunda kune za ku sha wuya,

Dan Allah mamy kiyi haƙuri kiriƙe yaranki, ke kuma yasmeen toh kinji, kiji tsoron Allah, wallahi yau mahaifiyar ki ta faɗi ta mutu tofa kinshiga uku matuƙar kina cikin wannan harkan,"

Haka suka rinƙa nasiha sosai wannan yayi wannan ya amsa, sukayi masu sallama, malama rabi tace


"karda tajira gobe da sassafe tazo ta amsa kuma zata duba mata shago kusa da gida, sai abuga mata babban tambari  dan asan inda take,

Godiya mai tarin yawa tayi ta jerowa, suka barsunan tana ta ƙara jinjina shawar warinsu, tabbas tayi kuskure amman yanzu insha Allah zata gyara,

****

Auran zamaniWhere stories live. Discover now