*👩❤️👨AUREN ZAMI👩❤️👨*
*WRITTEN BY RUKAYYA IKRA (UMMU SULTAN)*
*WATTPAD@IKRARUKAYYA11*
*DEDICATED TO UMAR ABUBAKAR (DADDY UMAR)*
*SPECIAL GIFT TO*
*KAWATA HINDATU MUSTAPHA🥰🥰🥰*
PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com'/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.come m/pro__writers?s=09
*SHAFI NA ASHIRIN DA SHIDA*
📚🖊️...........Rasuwan malam ba qaramin gigita dukkan ilahirin mutanen wurin yayi ba, ba wurin su kadai ba harta garki village Saida hankalin su ya tashi da suka Sami labarin rasuwan malam,
Makaranta kowa ya yayi baqin ciki sun jajanta rasuwa, haqiqa sunsan rashin malam a gare su babban Rashi ne,
Khairat gaba daya ta birkice ta zamo tamkar wata zararriya ga zazzabi Mai zafi da ya rufe ta, Wanda yayi sanadin dady ya tursasa aka kaita asibiti domin binciko abinda ke damun ta,
Gwaje gwaje suka Mata ba tare da Bata lokaci ba suka gano khairat na dauke da ciki, baqin ciki ya hadu musu da farin ciki don sunsan malam ya tafi har abada bazai dawo ba amman gashi Allah yayi da rabon zasuga jinin shi a duniya,
Sunso su koma wurin da suka fito daman a sanadin malam suke zama a Nan Kuma yanzu bayi Nan,
Da suka sanar da dady haka ya rufe Ido yayi ta fada Yana cewa shi Kenan Bai Isa ya zauna dasu ba su riqe su tsakani da Allah to babu inda zasu je sunzo su zauna tare dasu ne zama na har abada bawai na wani qanqanin lokaci ba Kuma abinda suka mishi tsakani da Allah ne ba don malam ba,
Yayan malam da ya zamo wani iri ya fita hayyacin shi cikin sauri dady ya bada umarnin a dauko bilkisu da gaggawa a aura ma yayan malam domin su samu sukunin rashin malam da sukayi,
Bayan kwanaki da dama khairat tabar gidan ta koma gidan su, momy Bata barta ta zauna a ko Ina ba sai a dakin ta saboda tana zama tare da ita tana debe Mata kewa.
Babyn Nadiya da babyn Salma suna ta girma tabarakallah idan ka gansu gwanin sha'awa kamar yaran turawa sunyi bulbul,
Abinka da yaran masu kudi suna samun abinda jiki yake buqata sai girma suke sosai kansu daya kaman tagwaye idan ka gansu bazakace tsakanin Abubakar da Maryam akwai tazara ba, koman su a tare sukeyi sun shaqu da juna sosai.
*******
Nadiya na zaune a office aka shigo Mata da yaronta Anwar Wanda yaci sunan dady wato Abubakar,
Yan office kowa sai kallon shi sukeyi suna rubibi wurin karban shi, khaleel na ganin haka yace bama zai bar yaron ba,
Ya dauke shi ya tafi. dashi gida ya miqa shi wa khairat sannan yayi gaba,
Khairat na zaune tare da momy suna ta Hira Amman komi nata ya ragu batada sauran walala Bata farin ciki, saiga fa'ud ya shigo,
Magana yazo musu dashi a kan zai koma Amman bazai tafi ba Sai tare da matar shi, dady shi ya dauki nauyin dukkan wasu hidimomin da yakamata ayi wa Nabeela aka daura aure suka Kama hanya sukayi tafiyar su,

YOU ARE READING
Auran zamani
Historical Fictionsoyayya, kiyayya, hargitzi gamida cin amana ga sakarchi, khairat tayi ma rayuwarta illah da zatayi dana sani anan gaba,