SHAFI NA SHA TARA

59 4 0
                                    

**  👩‍❤️‍👨AUREN ZAMANI👩‍❤️‍👨**

WRITTEN BY  RUKAYYA IKRA (UMMU SULTAN)

WATTPAD@IKRARUKAYYA11

DEDICATED TO
 
UMAR ABUBAKAR(DADY UMAR)

SPECIAL GIFT TO

KAWATA HINDATU MUSTAPHA🥰😘

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09


            *SHAFI NA SHA TARA*

📚🖊️....Gaba ɗaya gurin kowa ya ɗauka da kabbara daddy da yake zaune da matansa ya kallesu yace,

"Gaskiya kuna ƙoƙari sosai wallahi, yanzu badan jama'a ba, da kuma kunyar ɗiyar tamuce da fa kune zaku zayyano irin wanann  wa'azi haka mai daɗi da faɗa karwa",

Sukayi murmushi,

"ai ba'a kunya amaganan addini,  kawai cine tunda muna da warda zata fanshemu, ai malama rabi tana ƙaƙari sosai tamkar ammi itama",

Masu cikine suka miƴe dan guda narda godiya ga mutane, haka suka rinƴa magana ɗaya bayan ɗaya, daga ƙarshe salma ta amsa,

" ina ma kowa fatan alkairi da rayuwa mai ɗaurewa har zuwa tsofansu arayuwa, tamkar iyayanmu, ina miƙa dinbin godiya ga sirikai na gari, wanda samun irinsu sai an tauna, dan kuwa muɗin muncire tuta, bama banbance iyayanmu acikinsu,

sannan samun mazaje irin yaransu sai anyi da gaske,tarbiya sunsame ta,sannan kulawa kuwa,saindai ayi koyi daga garesu,na basu lambar girma babba agurin,ina fatan Allah ya ɗaga arzikinsu da darajansu fiye da ta kullum,





Allah ya dauwa mar damu cikin jindadi tare dasu har ƙarshen rayuwarmu ameen,ina alfahari da samunsu amatsayin abokan raya sunnan mu,

Daddy momy ammi muna maku fatan alkairi, ango da amarya Allah yasa gaba muce gara da akayi ameen",


Kowa ya mata tafi salim idonsa khair a kanta ya miƙe ya tarota, yace,

"baby ina kunyar kodan kinsa hijab ya ɓoye abunda akema kunyar?"

Murmushi tayi ta wulla masa manyan idanun ta masu rikitashi, tuni ya fara kauce hanya ta sakeshi tabar gurin cikin sauri, sosa ƙyeya salim ya rinƙayi,


"zamu haɗu anjima baby"

Masu raba abinci da kansu suke raba jakka da ta ɗauki tarkace kala kala acikon ta, cikin natsuwa da tsari babu irin hargitsin ƴan zari agurin,

Abun ya kayatar harta masu kallo ta gida sukansu abun ya burgesu,
Sosai salma ta fara gajiya, sakina kuwa sarkin wayo aiko gurin bata tashiba dan karda ta jigata,

Nabila da nadiya kuwa wata shaƙuwa tashiga tsakaninsu time guda gurun bikinnan, ko ina kingansu tare,

Taro yayi armashi, kowa ya koma gidansa cikin koshin lafiya, ango da amarya ma haka,

Auran zamaniWhere stories live. Discover now