** 👩❤️👨AUREN ZAMANI👩❤️👨**
WRITTEN BY RUKAYYA IKRA (UMMU SULTAN)
WATTPAD@IKRARUKAYYA11
DEDICATED TO
UMAR ABUBAKAR(DADY UMAR)SPECIAL GIFT TO
KAWATA HINDATU MUSTAPHA🥰😘
(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*SHAFIN NAKU NE,MAMAN WALEED,MAMAN HANEEFA,AYSHA I IBRAHIM,ƘANWA FADILA,MAMAN HAFSAT,MRS ABDULWAHAB,MAMAN HAJARA,SHALELEN ABBAH,INA ALFAHARI DA KU AKULLUM*
*SHAFI NA ISHIRIN*
📚🖊️.....Jikinta yayi sanyi sosai da sosai, tabbas taso ace salim zata aura yarda take mutuwar sanshi, zata sadaukar mata dashi, su zama su biyu,
Sallama tayi tashiga cikin gidan, radiya zaune bisa kujera tana taya mama gyaran wake,
Gaba ɗayansu suka juyo dan ganin mai sallama, cikin sauri radiya ta miƙe, "oyoyo yau salma ce agidanmu?, shiyasa tun safe muke ta samun alkairin, ashe manyan baƙi ne zamuyi",
Tayi murmushi, tamata iso ta shiga falo, mama nata fara'a tana mata sannu da zuwa,
Ta zauna suka gaisa sosai,
Salma ta ɗaga kai tace "radiya idan babu damuwa dan Allah zamuyi magana da ke, dan gurinki nazo",
Radiya tayi murmushi " inajinki salma babu kowa gidannan dagani sai mama, duk ma aikata ne kowa ya kama kansa sai kuma zuwa anjima, nima dan na ajiye aikinne da yanzu bana gidan",
Tayi murshi, "gaskiya kun burgeni koma yasan zafin neman halal ɗinsa, su mama su kansu sunsami sauƙin rayuwa",
Tayi murmushi, " ai kinganmu ƙwata ƙwata abbah baya jiran abin hannunmu, nasa yakeyi, yace mujira muma ranan da zamuji da namu nauyin nanan zuwa, da kyar yake amsar kyautar hannunmu fa, ko siyayya mukayo yalingi faɗa kennan sai yace muje muyi ta najin gaba dasu, "
Jinjina khai salma tayi sosai "kai amman kam kunyi dachan mahaifi, awannan zamanin ba kowane uba bane zayayi wannan abun, wasu iyayan suna ganin yaransu sun balaga zasu cire hannusu da yimasu komi na rayuwa, sai dai yaro ya dage yanema da kansa,
Sai ku dage ku kuma kusaka masa da alkairi, nadiya nazo ne da kaina dan nema ma salim auren ki idan kin amince!!!?, "
Wani irin faɗuwan gaba radiya tayi, "salma aini anyi mani miji wallahi, bakiga wani yana fita ba da kina shigowa?"
Ta jinjina kai alaman ta gansa,
"haidar ne tabbas naganshi, mijin marganyi ya maryam ba",
Mamaki ta farayi ya akayi salma tasansu haka,
" najima da sanunsu dan munyi sabo sosai da maryam, naji mutuwarta, babu rabon muhaɗu gidan gaisuwa ne, inaganin da kinganni, dan gaskiya mutuwarta ta firgita ni sosai",
YOU ARE READING
Auran zamani
Historical Fictionsoyayya, kiyayya, hargitzi gamida cin amana ga sakarchi, khairat tayi ma rayuwarta illah da zatayi dana sani anan gaba,