** 👩❤️👨AUREN ZAMANI👩❤️👨**
WRITTEN BY RUKAYYA IKRA (UMMU SULTAN)
WATTPAD@IKRARUKAYYA11
DEDICATED TO
UMAR ABUBAKAR(DADY UMAR)SPECIAL GIFT TO
KAWATA HINDATU MUSTAPHA🥰😘
(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
*SHAFIN NA KUNE MASOYAN ASALI MAMAN NANAH FATEEMA ANND MUM YUSEEF INAYINKU OVER*🥰🥰🌹🌹
*SHAFI NA SHA SHIDDA*
📚🖊️.... Daddy ya jinjina kai da maganan malam, amman aransa baiso hakan ba,
"Amman malam ko anan ɗin inaganin za tafi samun kulawa sabida tana ganinta kusa da gida, sannan komi zatayi dole ana samata ido akan zaman takewar ku, ina ganin kayi haƙurin kuzauna anan ɗin yafi"
Malam bayason musu da daddy ko kaɗan,
"Hakane daddy amman dan Allah kumani uzurin ta zauna achan ɗin koda na watanni kaɗanne sabida iyaye na da dangina, kasan yanzu za kaji anfara zagin mutum, wasu ma zasuce dan dukiyarta na aureta, toh mubari tadan zauna agirina ɗin tunda komi akwaishi aciki, 2 bedroom ne da toilet da kichen acikinsa sai filin tsakar gida da toilet na waje dan baƙi"
Jinjina kai daddy yayi sosai tabbas malam yafisu gaskiya kuma dole ya haƙura yabi umarnin sa, tunda shine mijinta,
Haka sukayi sallama kan cewar zasu sake haɗuwa kafin ɗaurin aure,
*********
Salati keta tashi da koke ko ke, habib ɗin maryam ne ya shigo da gudunsa, yana faɗin,
"Ammi bata mutuba ammi maryma ɗina bayanzu zata mutuba!!, "
Innalillahi wa'inna ilahir raji'un kawai ketashi acikin gidan, mahaifiyarsa ce tayi kansa yarda yaketa jinjiga gawar maryam yana faɗin,
"Ki tashi dan Allah swtheart bayanzu zaki tafi ba, miyasa zaki mani haka!!?" yana kuka maishiga zuciyar mai sauraro,
Ammi da ta daure bata son yin kukan amman yarda habib yakeyi dole yasa ta fara ƙwalla sosai, mahaifiyar marym kuwa ko fuskanta bata ganuwa,
Mahaifin maryam ne yayi sallah yashigo, "dan Allah ammi kuyi masu sutura tunda Allah ya amshi abunsa, ba za'a zauna nata kuka ba gaban gawa, kafin a wuce dasu ya kamata ya bama yaron suna dan ya tashi da sunansa gobe ƙiyama",
Yana gama faɗa ƙwalla cike da idonsa yayi waje,
Umman habib da mahaifinsa ne keta ƙoƙarin shawo kan habib dan ya dawo daga hayyacinsa,
Tuni makaranta ta ɗauka maryam tarasu, fahad zubewa yayi agurin cikin sauri akayi dashi asibiti,
Da ƴyar sukayi shiru a kayima maryma sutura da temakon mahaifiyarta da ammi da nabila, wannan ne ya ƙarama nabila da khairat imani sosai acikin zuciyarsu,

YOU ARE READING
Auran zamani
Fiction Historiquesoyayya, kiyayya, hargitzi gamida cin amana ga sakarchi, khairat tayi ma rayuwarta illah da zatayi dana sani anan gaba,