YAR TSILLA-TSILLA

61 2 0
                                    

☘️☘️☘️☘️🍀🍀
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
🍀🍀🍀
☘️☘️
☘️

*YAR TSILLA-TSILLA*
_(Sanadin rashin kulawar_ _uwa uba)_

☘️️☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️☘️
☘️☘️☘️
☘️☘️
☘️

Story & writing
By
Khadeejah lawan usman
(Deejerleen)
______✍️______

*TAMBARI WRITER'S* *ASSOCIATION*
🔱(( Home of Expart and talented writers, da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umma.))


*T.W.A*
________________________
https://www.facebook.com/Tambari-writers-association-106345791122870/
________________________

*Follow me on Wattpad*
*@deejerleen*

*Didicated to my* *sweetheart (aysher* *humaira) 💋* 💋💋

_Wannan labarin_ _yafarune dagaske ba_ _qirƙirarsa nayi ba_ _yafarune! labarine mai_ _cike da barkwanci, kunci, nadama,_ _tsilla-tsilla ( rashin zama_ _wuri ɗaya)_ _jarabawa kala kala,_ _sanadin mahaifiyarta da_ _mahaifinta_ .

_Duk wanda labarin yayi_ _daidai da rayuwarta tayi_ _hakuri domin labarin_ _yafarune dagaske._

*_Warning_* 🚫

*Ban yarda wani ko* *wata sujuyamin littafi* *ba ko _wata siga dake_* *_littafin, duk wanda yayi/_* *tayi muhadu a* *kotun _Allah_ .*


True life story ✨

Bissmillahir rahmanir raheeem, da sunan allah mai rahma mai jin kai.

_Page 1&2_

***** Cike gidan yake da mutane anata hidima, babban gidane na qasa mai dauke da ɗakuna dayawa aciki. dagacan cikin gidan akwai wata qofa dazata sadaka da wani madaidaicin gida mai dauke da ɗakuna biyu da faranda, sai madaidai ciyar farfajiya, gidan acike yakeda mutane anata hidimar biki, dana fito daga cikin madaidaicin gidan nahango wani daki cike da ƴan mata da alama anan amaryar take.

Koda na leqa na iske amaryace da qawayenta sunata hira irinta qawaye da amarya, daga can cikin kusurwar dakin nahango amarya sai fara'a take yau zataje gidan habibinta kuma masoyinta hamza, yau takama chuda ne saboda al'adar garin haka take, za'ayi sakin lalle,chuda, yini, sai daukan amarya.

Abu....abu.....abu...! Wata mata keta kwalama wata matashiyar yarinya kira wanda dagani itace ake bikinta, yarinya ce dabazata wuce shekara goma sha shida ba, itaba faraba ita ba baka ba siririyace batada jiki saidai tanada shape daidai gwargwado, fuskar ta tana ɗauke da dogon hanci sai madaidai cin baki da madaidaitan eye lashes tanada gashi mashallah har gadon baya, fuskar ta faffada ce bata da tsayi, gajerace batada tsayi sosai....

Abu dai batada fada sai tsiwa kamar me! ga tsokanar tsiya da tsoro sai dankaran surutu kamar taci maqogaron aku, ga gulmar tsiya.

"Gani"cewar abu da tazo wurin wannan mata, wuri ta nuna ma abu tace" zauna inason magana dake, zama tayi tasadda kai kasa tana sauraron matar mai suna adama,
Fada tashiga yimata irin wanda akewa amarya inza'akaita gidanta kasancewar yau ake yini kuma yau za'a kaita gidanta.

YAR TSILLA-TSILLAWhere stories live. Discover now