🐏🐏🐏
*SANADIN*
*RAGON LAYYA*
🐏🐏🐏
🐏🐏
🐏_By_
*Ameera Adam*
*AmeeraAdam60*
@: _Wattpad_*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._*_SADAUKARWA GA DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*
_بسم الله الرحمن الرحيم_
1-5
Assalamu alaikum, salamu alaikum hajara, hajara ina kika shiga ne nake ta sallama ko kin zagaya makewayi ne, Malam kabiru ne ya shigo yana kwalawa me dakinsa kira, fiddausi ce ta fito daga daki hannunta dauke da kayan wanki sannu da zuwa tayiwa mahaifin nata ya amsa sannan ya shiga tambayarta, " fiddausi ina mamanku ne ko bacci take banji motsinta ba" baba tana cikin daki dazu dai naga idanta biyu bansani ba ko bacci ya dauketa, to shikenan jeki kiyi wankinki, ya bata amsa sannan ya shiga dakin da hajara take ciki.
Duk wanda ya kalli yananin mlm kabiru sai ya fahimci irin farin cikin da yake ciki, fuskar sa da walwala ya shiga dakin yana kara maimaita sallama.
Ledar hannunsa ya ajiye a gefen kujera, hajara na mik'e akan doguwar kujera mlm kabiru ya shiga, amsa sallamar sa tayi ciki-ciki kamar batayi niyya ba, da mamaki ya kalleta yace, " hajara idan ki biyu ko yanxu kika tashi? " dan dago da kanta tayi sannan tace, " ban dade da tashi ba" to taso ki gyara mana kayan miyan nan bari na tsallaka gurin nasiru me nama in karbo mana dan k'ashin miya" ko kurar sa bata kalla ba yana gama magana ya fice.
Kai tsaye tsallaken titi yaje ya samu nasiru me nama na hura wutar balangu cikin barkwanci mlm kabiru ya fara yi masa kirari, " kaga sarkin nama ko ince kafi giwa nama ya kasuwar ya harkoki? " washe baki nasiru me nama ya farayi yana fadin, "kwarai kuwa mlm kabiru suya za'a baka ko danye kai ko duka kake so yanxu zaka ga aiki da cikawa, dariya mlm kabiru yayi yace a'a sarkin nama wane ni da siye duka wannan naman, ay nama dari biyar zaka yankomin ungo kudin amma fa dubu ce dan nasan yanxu kace mun canji wuya yake" nasiru me nama karbar kudin yayi yana fadin, " mlm kabiru kasan kasuwar ce sai godiyar Allah kawai amma abun ba'a cewa komai.
Yanka masa naman yayi yana shirin nad'e takardar, mlm kabiru yace, "kai sarkin nama yanxu naman dari biyar haka ya koma haba kai kuwa ka dan kyauta mana sai kace naman dari uku" hmmm mlm kabiru kenan karfa ka manta yau sallah saura kwana uku kasan dai yanda dabbobi suke tsada, wallahi wannan naman daka gani kawai dai karfin hali ne, haka zamu daddagira har zuwa bayan sallah.
Hakane kam Allah ya iyamana wannan tsadar rayuwa talaka dai yana cikin wani hali, mlm kabiru ya bashi amsa ya karbi naman ya wuce gida.
Yana shiga gida hajara ya samu a inda ya barta, cikin mamaki yace, " hajara wai nikam ko akwai abunda yake damunki naganki duk wani iri" dan ya mutsa fuska tayi sannan tace, " a'a ni lafiya ta klau me ka gani? kawai yanayi ne yasa ni hakan"
To shikenan Allah ya kyauta tashi ga nama na kawo ki hada kayan miyan cen akai markade yamma tanayi.
Bata bi ta kan zancen sa ba ta jeho mai tambaya.
Wai ni mlm tun dazu bayan fitarka ina ka je ne? naji ka shiru banji kukan rago ba, ni nayi tunanin ma ko kasuwa ka tafi tunda naga dai ay kunsami albashi ga alama nan na gani kana cikin walwala.
Hmmmm hajara kenan wai meyasa kinfiya gutsira magana kamar wata karamar yarinya, inace yau kusan kwana biyu kenan dayin maganar mu, ko so kike muyita abu daya agaban yara suna ji, wannan be kamata ba sam kinsan ni naki jinin gutstsira magana.

YOU ARE READING
SANADIN RAGON LAYYA CMPLT
Short StoryBil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wa...