11-15

246 22 0
                                    

🐏🐏🐏
       *SANADIN*
               *RAGON  LAYYA*
           🐏🐏🐏
              🐏🐏
                    🐏

                  _By_
         *Ameera Adam*
    *AmeeraAdam60*
      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        11-15


Harararta me awarar ta farayi, ta tsugunna tana kokarin daukan bokitin ta, gunguni take yi  kasa-kasa tana fadin, " wallahi badai tawa ba sai dai taki haka kawai zaki dinga zagina "
          Au zagina kikeyi shegiyar yarinya mara kunya, mara tarbiyya kawai.

Sai da me awara ta juya idanu kasa da sama, saman idan nan yasha eyeshadow ga uwar jagira, murgud'a baki ta kara yi sannan tacewa hajara.
              " Ay ba'a  mara kunya daya, ki kara zagina inlissafo miki su" ta karasa maganar tana barin gurin.

Hajara zabura tayi zata dank'o wuyan me awara, da sauri hanne ta dafe mata cinye tace.
            " haba hajara meye haka kike yi ne, wannan yarinyar fa ba sa'ar yinki bace, kina ganin kalubalen da yake gabanmu, ya kamata mu tsaya mu fuskanci matsalar dake tattare damu"

To shikenan, hanne yanxu ya zamuyi? Dan Allah mu karasa gidan malamin nan ki rokar min shi ko bashi ne yayi mun aikin, tunda kinga kun dade dashi, kinga ay na rage zafi"

" Kudin mota kuwa nasan idan mukaxo tasha, nasan zamu samu dan na Allah basa karewa " hajara ta karasa maganar cikin marairaicewa.

Ummmmm hajara banaki ta taki bane, akwai abunda nake hangowa, malamin nan bashi da mutumci ko kadan, indai akan kudi ne baya ji baya gani, kinga mun shafe shekara bakwai tare, amma wallahi akwai lokacin da naje masa da bukatar yayi mun wani aiki akan rabon gadon mu, wallahi ki yayi sai da na koma na ciko masa kudinsa casss sannan yayi mun.
            Bare aikinki yana cikin jerin ayyuka masu tsada da yake yi, aikin miji dana kishiya da yayan miji yafi tsada aduk cikin ayyukan da yake yi"

"To yanxu hanne haka kike so muzo abanza mu koma awofi ga asarar kudin dana tafka, yanxu kina ganin zanji dadi ko nan gaba zaki kara yimun jagora inbiki? "

"A'a ba'ayi haka ba, mu jarraba hajara amma wallahi jikina yana bani mutimin nan bazai miki aiki ba, dan sanin hali yafi sanin kama" hanne ta fada tana gyara tsayuwarta.

Hajara tace, " haba hanne kinji irin mugun bakin da zaki ja mana, tun kafin muje dan Allah kiyi mana adduar Allah ya doramu akanshi.

Hanne dan jim tayi sannan tace, " to " muje ay mutum baya k'in ta mutane, sai angwada..........."

Hanya suka mik'a suna ta tafiya, sai wuce gidaje da shaguna suke, sannan suka yanka cikin wadansu ciyayi, sun dan jima suna tafiya cen cikin wani daji suka nausa ba gida gaba ba gida baya, sannan suka karaso wani dan madaidaicin karamin gida.

Kofar gidan cike yake da manyan motocin masu kudi, da mashina kekuna basu fi guda biyu ba.

Soron gidan suka shiga maza ne sunkai takwas, bayan sun shiga ciki suka samu mata sunkai goma sha hudu, zaune suke atsakar gida kan tabarma, su hajara na shiga matan suka bisu da idanu.

Sannu hanne tayi musu sannan tace, " dan Allah wace karshe?" wata yar matashiyar mata ce da bazata wuce shekara talatin ba tace, " ni ce karshe amma kunsan k'a'idar malam idan yaga mace daya to namiji daya ne zai shiga"  eh, nasani, hanne ta bata amsa tana kokarin zama a tabarma, itama hajara guri ta samu ta zauna.

SANADIN RAGON LAYYA CMPLTWhere stories live. Discover now