🐏🐏🐏
*SANADIN*
*RAGON LAYYA*
🐏🐏🐏
🐏🐏
🐏_By_
*Ameera Adam*
*AmeeraAdam60*
@: _Wattpad_*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._*_SADAUKARWA GA DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*
_بسم الله الرحمن الرحيم_
26-30
_Shima wannan banyi editing ba kuyi sorry._😉
Bil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wari daya akafarta wari daya kuma igiyar ta tsinke, buta a tuntsire ruwan cikinta ya tsiyaye tas, surutai hajara ta cigaba dayi bakai ba fasali, hakan ne yasa mlm kabiru ya kara daga murya cikin azama yana karanto mata ayoyin kur'ani yana tofa mata.
Hajara cikin fusata tace, " mlm wai sai tofeni kake yi ni kabarni inji da abinda yake damuna "
Dan dakatawa yayi da karatun yana karewa hajara kallo, tsab muryarta take da alama ba wasu jinnu da suke damunta, zaninta ya janyo ya rufe mata cinyoyinta dasu, yunkurawa hajara tayi ta tashi zaune tana zubda kwallah.
Cikin tashin hankali Mlm kabiru yace, " hajara lafiyarki me ya sameki cikin dare kike wannan ihun, nasha gaya miki idan zaki kwanta ki dinga tofe jikinki da addu'a, kuma idan mummunan mafarki kikayi basai ki karanta addu'a ki koma bacci ba, idan baccin ya gagareki sai ki yo alwala ki gabatar da sallah ki fawwalawa Allah lamuranki, to hajara kodai gamo kikayi dan naga buta kusa dake " mlm kabiru ya karasa magana yana kallan hajara da fuska ta hade hawaye da majina.
Hajara girgiza kai tayi sannan tace, " babu ko daya malam "
Mlm kabiru kuluwa ya farayi cikin fada yace, " amma ba abinda yake damunki kikaxo tsakar gida cikin dare kina wannan haukan salan mak'ota suce wani abun akai miki ko azaci aljanu kika hau, cire makota ma yanxu da yaran nan sun farka suka fito suka ganki da dan kanfai me zaki ce musu, sai ki tashi ki kamwashe tsummokaranki kiyi gaba, ina cikin baccin na me dadi kin tashe ni "
Hajara bakin ciki ne ya cikata, zafi biyu ga na rashin rago ga sababin da mlm kabiru yake mata, rushewa tayi da kuka cikin kuka tace, " mlm rago ne, wallahi ragon nan ne " sai kuka yaci karfinta ta kasa karasa maganar.
Guntun tsaki yaja sannan yace, " yanxu hajara har kin fara sumbatu cikin dare saboda abun duniya, me akayi da rago da har zaki fara surutai mara fasali, badai rago bane kin siyo to sauran mitar ba meye kuma ?"
Cikin kunan rai hajara tace, " mlm sun sace ragon sun gudu dashi"
Cak mlm kabiru ya tsaya cikin mamaki tace sun sace rago to su waye suka sace ?
Duk abinda ya faru hajara ta kwashe ta gayawa mlm kabiru, asanyaye ta nufi hanyar da rago yake, yana haskawa yaga wayam kamar yanda hajara gaya masa, cikin gida ya dawo lokacin hajara ta shiga falo ta zauna, mlm kabiru guri ya nema ya zauna cen nesa da ita yana kare mata kallo cikin takaici da bakin ciki.
Hajara kukanta ta sharba me isarta, sai da tayi ta gama ta goge hawayenta, sannan mlm kabiru ya ce, " hajara, ki gaya mun ribar Abinda kika samu nawa kika kirga nawa kika samu, yanxu me ragon nan ya amfaneki dashi, wallahi duk wanda be godewa Allah ba zai godewa azabarsa kuma duk wanda beji bari ba zaiji hoho, hajara yanxu wa gari ya wa ya kin ranto kudin mutane kin siyo rago ansace shi, me zaki cewa me kudin idan lokacin biya yayi, duk irin abinda ake guje muku bakwa gani duk abinda zuciyarku ta baku shi kuke aikatawa, to hajara dabara ta ragewa me shiga rijiya sai kisan yanda zakiyi dasu, kinga _SANADIN RAGON LAYYA_ kinsa kanki cikin matsala da tasku, kina zaman zamanki kin jawa kanki ruwa, dama nasha gaya miki ki dinga godewa Allah inba haka ba zaki godewa azabarsa, wallahi kadan ma kika fara gani muddin bazaki canja tsarin rayuwarki ba " yana gama magana ya ja fulo yayi kwanciyarsa.

YOU ARE READING
SANADIN RAGON LAYYA CMPLT
Short StoryBil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wa...