16-20

279 24 0
                                    

🐏🐏🐏
       *SANADIN*
               *RAGON  LAYYA*
           🐏🐏🐏
              🐏🐏
                    🐏

                  _By_
         *Ameera Adam*
    *AmeeraAdam60*
      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        16-20


Hanne fakar idon mutumin tayi ta dan zunguro hajara kasa-kas ta fara yi mata magana, " hajara yanxu motar dabbobi zamu shiga    kodai zamu ce masa mungode mu nemi wata motar ne? "

Wani kallan baki da hankali hajara tayi wa hanne sannan ta bata amsa, " lallai kekam hanne bansan da wane suna zan kiraki ba, yanxu mu wuni a wahale muna neman motar sannan yanxu Allah ya rufa mana asiri mun samu za'a rage mana hanya sannan kice mu bashi hakuri mu nemi wata, ni kam yau ba abinda zai hanani hawa motar nan sai dai idan shi yace ya fasa daukanmu"

"To shikenan Allah ya sauke mu lafiya" hanne ta bata amsa.

mutumin na cen gefe sai gartsar goro yake, bayan ya gama ci ruwa ya bula ya kurkure bakinsa ya watsar gefe, yana nan zaune wani matashin saurayi yaxo gurinsa ya dan rissina yace.
       " me gida ankammala lodun ragunan akwai sauran abunda za'ayi? "

A'a shikenan kacewa Isa ya karaso da motar nan, akwai matan da zamu ragewa hanya, ya hanzarta da Allah kaga garin nan k'ara haduwa yakeyi" mutumin ya karasa maganar yana mikewa tsaye.

       Ba'adauki wani lokaci ba Isa ya karaso da motar, saukowa yayi yaxo ya mik'awa ogansu mukullin.

Motar irin akori kurar nan ce bayan ta abude yake, shanu biyu ne aciki sai raguna da tumaki masu dan dama.

Kallansu ogan nasu yayi ya umarcesu da su shigon sha'aibu su dauko masa buhunhunan shinkafa guda uku daya siya.

       Debo buhun shinkar sukayi suka loda su agaban motar kusa da mazaunin driver, bayan sun rufe suka dawo bayan motar suka d'ane suka hau.

Ogan nasu ne ya leka gurin da su isa suka haye yace, " isa ku dan tura ragunan nan gaba sai kusa musu gora na nan akasa, kudan matsa kuma gaba kunga da bayin Allah nan zamu tafi"

     "Hajiya bismillah ku zo zamu wuce" ogansu isa ya fada yana haye gaban motar.

Su hajara ne suka karaso gurin motar, hanne ce ta kalli dan tudun bayan motar da alama dai ya musu tudu bazasu iya hawa ba.

Magana ta farayiwa isa.
      " saurayi dan Allah taimaka mana bazamu iya hawa ba motar ta mana tudu"

Yooooo wane taimako zan muku ga dai benci cen ku dauko ku taka sai ku hawo.

Ba musu hajara taje ta dauko musu benci ta ajiye, hanne ce ta fara takawa ta haye sannan hajara tabi bayanta suka d'are saman motar, sai ga su hanne cikin raguna.🤣

Atsaye suka tsaye isa yasa hannu ya sa sakatar motar, sannan su hajara suka samu suka jingina.

Magana su isa suka yiwa ogansu sannan ya tada motar suka dau hanyar kano.

Sun danyi tafiya me nisa ba me yiwa kowa magana, suna hanya aka fara yayyafi da walkiya kafin wani lokaci ruwan sama ya dauko.

Ruwa ake tafkawa kamar da bakin kwarya, andan dauki lokaci ana ruwa daga baya ruwan ya tsagaita sai iska da take tashi.

SANADIN RAGON LAYYA CMPLTDonde viven las historias. Descúbrelo ahora