🐏🐏🐏
*SANADIN*
*RAGON LAYYA*
🐏🐏🐏
🐏🐏
🐏_By_
*Ameera Adam*
*AmeeraAdam60*
@: _Wattpad_*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._*_SADAUKARWA GA DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*
_بسم الله الرحمن الرحيم_
6-10
Allah hanne? Shafamun inji a wace unguwar yake? Cikin zumudi hajara take tambayar hanne, murmushi hanne tayi sannan tace, " wallahi wani dan kauye ne sai kin shirya sai muje, saboda shi aikinsa sai kana kudi, inda kudinki to zakiga aiki kamar yankan wuka sabon wa shi.
Hanne kara zugoni fa kikeyi ji nake kamar nayi tsuntsuwa muje gurin, amma to kamar nawa yake yin aikin?
Ehto, ki tanadi kamar dai dubu goma zuwa goma sha biyu, na gaya miki shi kudi sune agabansa, idan kinada uwar kudinki to bakida matsala saboda shi duk sabon da kukayi dashi na tsahon shekaru indai baki da cash to ranar ba magana, amma ki gwada ki gani zaki bani labari dan idan yayi miki aiki wallahi sai kin juya malam kabiru kamar waina a tanda, ke abinda baki sani ba wallahi ko kashi da fitsari inbaki bashi umarnin zuwa ba saidai yayi shi agurin.
Ayyiriri nanaye ahaayye kawata shiyasa nake sanki ta wajena, amma wani hanzari ba gudu ba, wallahi kudin gurina basufi dubu takwas da yan kai ba, yan kanma bance sunyi dari biyar ba, hajara ta karasa magana tana kallan yanayin hanne.
Kallan tsaf hanne tayiwa hajara sannan tace, haba hajara dubu takwas fa kikace me dubu takwas zatayi mana ga kudin motar ma Allah zamuci dubu daya da dari biyar, hajiya ta ki ware bakin aljihu kiga aiki da cikawa.
To shikenan hanne bani zuwa nan da gobe da safe zan nemi cikwon kudin, ke gobe ma zamu je kinsan da zafi-zafi kan daki karfe, hajara ta karasa maganar tana mikawa hanne hannu suka tafa.
Haka nake san ji da zaki wani bada mata, kamar ba mace ba akwakulo da yawa daga hannun mlm kabiru, uwar gida sarautar mata.
Kan hajara ne ya kara girma ta fara murmushi, sannan tace, " hanne kedai ki zauna cikin shiri goben nan fa zamu je.
Haba hajara meye naki na jadadda mun nida ba miji ba, ba tsayayyen farka ba ay ko da dare kika xo muje ni banida matsala.
Cikin dariya hajara tace, " kwarai kam shiyasa kike tsula tsiyarki san ranki" dan canja fuska hajara tayi tacewa hanne, " Kin dai tabbatar da aikinsa na ci ko dan gaskiya banasan nayi asarar kudina, kar inzo indunkule kudina inkai masa azo aiki be ci ba.
Mtsssswww dan Allah kiji zaki b'ata mun rai muna zaune cikin jin dadi, idan aikinsa baya ci zakiji nace zan rakaki ne? Ke yanxu samarin da suke dafifi gurin furaira na banza ne, kin manta da ba shegen da yake zuwa gurinta kamar wacce akayiwa asiri da jab'a, amma yanxu ko ke Shaida ce basai nace komai ba ko ke kin isa ki bawa wani labari.
Dariya hajara ta kwashe dashi tace, " kai kawata gaskiya baki da kyau hanne, ga gidanki nan sai layi ake kamar asibiti.
To ke banda abinki hajara wa yace miki ana zama haka inba sakarai ba, zama haka ay sai Shashan mata, ke bari na zo na gudu yamma tanayi.
To shikena hanne nagode kwarai Allah bar zumunci, sai kinji ni.
Yanxu hajara takaninmu harda godiya? Ni nayi tunanin tun tuni mun zama daya.
Eh mun zama daya hanne amma ay hausawa suka ce yaba kyauta tukwici.
Wannan haka ne hajara, to Allah bamu alheri ina jiranki sai kinzo.
YOU ARE READING
SANADIN RAGON LAYYA CMPLT
Short StoryBil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wa...