🐏🐏🐏
*SANADIN*
*RAGON LAYYA*
🐏🐏🐏
🐏🐏
🐏_By_
*Ameera Adam*
*AmeeraAdam60*
@: _Wattpad_*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._*_SADAUKARWA GA DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*
_بسم الله الرحمن الرحيم_
21-25
_Sorry for not editing_👏🏼
" Hajara hajara, wai hajara ina ta magana baki amsa ba zo nan maza-maza ki fito" mlm kabiru ya fada yana kara haske rago dake kwance.
Da sauri hajara ta fito daga d'aki abayan katangar dakinta ta lab'e tana leken mlm kabiru, gabanta ne ya yanke ya fadi, ta fara fargabar abinda zata gaya masa.
Jin hajara shiru yasa mlm kabiru ajiye buta ya nufi daki gurunta, hajara najin tahowar mlm kabiru ta fada d'aki ta koma mazauninta, sai raba ido takeyi kamar munafuka.
'Dakin mlm kabiru ya shiga ya tsaya ya fara yiwa hajara magana yace, " hajara bakya jin ina kiranki ne tun daga waje nace a ina kika samu rago? "
Hajara dauke kai gefe tayi zuciyarta na lugude, bata tab'a tunanin zataji shakkar gayawa mlm kabiru maganar rago ba sai yanxu daya tirketa da tambaya.Cikin tsawa ya katse mata tunanin da takeyi yace, " magana nake miki kina jina sai juya kai kike, nace a ina kika samu rago, wallahi hajara ki bude baki kimun bayani tun raina bai b'aci ba"
K'asa-k'asa hajara ta bud'e baki tace, " d'azu ne na siyo shi bayan na fita"
Kika siyo hajara? Dama kinada kudi har wanda zaki iya siyan rago, ke da ba aiki ba ba kuma kasuwanci ba, ko kina wani kasuwancin aboye bansani ba? "
" Mlm jira nake fa dama ka gama cin abincin sai na maka bayani to kuma kazo kanata sababi, dan Allah ka kwantar da hankalinka bafa wani abu bane " hajara ta fada cikin karfin hali.
Hankalinsa gaba daya ya tattara akan hajara yace, " ina sauraronki kimun bayani yanxu basai anjima ba "
Kallansa hajara tayi taga fuskarsa ba alamun wasa, hakan ne yasa ta fara magana tace, " dama dazu ne dana fita na biya gidan lubabatu me adashi, na karbo rancen kudi dubu talatin da biyar nace mata idan ka samu albashinka na watan gaba zaka biya ta, to daga nan sai naje kasuwa na siyo................ "
Cikin tsananin bacin rai mlm kabiru ya buga mata tsawar da har sai da ta sata matsawa cen karshen gado, " zaki rufemun baki hajara ko sai na tattakaki agurun nan, na rasa kedai hajara wacce iri ce idan kina abu kamar me kan tinkiya, na aike ki nace kije ki ciwo mun bashi, wato duk abunda nake acikin gidan kin raina ko baki da gashin wance kice sai kinyi kitson wance, tunda nake dake na taba zuwa gun wani rancen makudan kudi har dubu talatin da wani abu, hajara wannan tozarci har ina a wannan rayuwar da muke ciki wasu fa basa samun ci uku rana, amma ke me kika rasa akan nace miki bazanyi layyah ba duk kike mun wannan tonon asirin, wai kece harda zuwa rance ki sai rago sai kace ke kike aurena , ki bude kunnen ki da kyau kiji wallahi-wallahi ba agidana ba ko ki kai mata ragon ki cika mata kudinta ko kuma ki saida ragon ki maida mata kudinta, amma ni da kike gani biyar dina bazatayi ciwon kai ba "
Idanun hajara ne suka fara raina fata cikin firgici tace, " Dan Allah dan Annabi mlm ka taimaka ka rufamun asiri, dan Allah karkayi mun haka ka fiddani kunya tunda sai karshen watan gaba zaka bi..........
VOUS LISEZ
SANADIN RAGON LAYYA CMPLT
NouvellesBil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wa...