🐏🐏🐏
*SANADIN*
*RAGON LAYYA*
🐏🐏🐏
🐏🐏
🐏_By_
*Ameera Adam*
*AmeeraAdam60*
@: _Wattpad_*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._*_SADAUKARWA GA DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*
_بسم الله الرحمن الرحيم_
36-40
Zille-zille sukeyi suna niyyar direwa ta saman mota, wasu daga cikin su ma ko kwakkwaran motsi basayi saboda sunsha tayi musu karo, kai tsaye police station aka wuce dasu aka tura su cikin cell, inbanda warin wiwi ba abinda yake tashi idan mutum ya gifta ta wajen cell din.
Wani gabjejen police ne yaje ya tsaya ta jikin kofar ya buga musu tsawa yana tambayarsu, " Kai uban waye yace kuje kuyi musu fashi da tsakar rana har kuke neman illa tasu suda dabbobinsu? "
Kallan raini gogarma yayi masa cikin magana irin ta rikakkun yan daba yace, " haka kawai zamu je musa musu kai ne, kai wadancen mutanen nan fa sun raina mana hankali, haka kawai zasu sa akamo mu adinga yi mana wata tambayar ehh yaaane, ni tinda nake ma bantaba ganinsu ba "Cikin fusata dan sandan ya buga mai tsawa, " kai karamin dan iska banasan iskanci da rainin wayo, ina kuka kai musu ragunansu? "
Harara gogarma ya kara watsa masa yace, " babba nifa ban fahimci wasu ehh raguna da kake zance ba, wai ma mu me zamuyi da wasu raguna muda ba iyali ba bare muyi musu layya? "Cikin fusata dan sandan nan ya kwalawa wasu police su uku kira, suna karasowa yace, " kai Abinda nake so ku tambayi yaran nan har sai sunyi laushi, saboda naga sunxo da rainin wayo da alama zasuyi taurin kai "
Tun kafin ya rufe baki suka juya dauko kulkinsu, ba b'ata lokaci suka bud'e cell din aka fara jibgar su gogarma sai ihu suke.Hanne ce zaune ita da furaira suna hira, furaira tace, " inna nifa wallahi kwadayin wainar fulawa nakeji ko insiyo fulawa ki soya mana? "
" Me zai hada furaira dan dai suyar wainar fulawa Allah na tuba anawa take " inji hanne.
" Kai Amma gaskiya bacci nakeji kozan siyo sai na tashi tukunna " cewar furaira.Galala hanne take kallan furaira da mamaki tace, " ke furaira me yake damunki ne ko awa guda fa bakiyi da tashi ba kice zaki kara komawa, nafa lura kwana biyun nan baki da aiki sai na bacci "
Hamma furaira tayi tace, " to inna mutum na gida me zaiyi inba bacci ba "
Wassafa wani abu hanne tayi cikin zuciyar ta nan da nan tsoro ya kamata, sai ta basar ta cewa furaira, " kafin kije ki kwanta dakko mun tukunyar fatan waken nan inciye ta inyi wanke-wanke "
Da "to" furaira ta amsa mata ta tafi tana lumshe ido alamar bacci na kanta.
Tana dauko tukunyar faten waken taji wani wari ya bigi hancinta da sauri ta ajiye tukunyar tana toshe hanci, wani amai ne ya taso mata, da gudu ta karasa bakin rariya tana kwara uban amai awahale.Gaban hanne ne ya yanke ya fadi tsoro ya kamata, cikin firgici tace, " ke furaira me yake faruwa dake ne? Ki gama aman kixo inasan ganinki "
A wahalce furaira ta yunkura ta taso bakinta duk ba dadi, tana tafe tana yatsina fuska ta karasa gaban hanne ta zauna tana dafe kai, kallan tsaf hannr tayi mata sai alokacin ta kare mata kallo, ganin irin d'ashewar da tayi ne yasa ta fara tambayarta, " furaira yaushe rabonki da bakonki na wata? "
Dan sosa kai furaira ta farayi tana sinne kai kasa.
Tsawa hanne ta buga mata ta kara tambayarta, " nace yaushe rabonki da bakon ki na wata? "
" Ina ina inajin dai zanyi wata biyu " furaira ta fada.
Cikin faduwar gaba hanne tace, " muga hannuki" duba hannunta hanne tayi tana duba idanunta, bata gama duba idan ta ba hanne tarufeta da duka.
Cikin takaici hanne take fadin, " yanxu furaira kina nufin ciki ne dake, oh ni hanne yau naga tashin hankali " hanne saboda bakin ciki harda kwallah.Janyo furaira hanne tayi ta makureta jikinta har rawa yake saboda tashin hankali tace, " dan ubanki ki gaya mun waye yayi miki cikin nan, wane shegen ne ya lalata ki? "
Furaira kokarin kwace kanta take, tana ihun neman agaji sai da taji jiki sannan furaira ta fara magana, " Alhajin Abuja ne "
Gwabe bakin ta hanne tayi tace, " shi Alhajin Abujan dan ubanki mijinki ne iyee? " hanne ta tambayeta cikin kumfar baki." Ay yace zai aure ni " inji furaira.
Sai alokacin hanne ta tsagaida da dukan furaira sannan tace, " too too yanxu naji batu, ayda kinmun bayani tun farko da bakiji jiki da duka ba, tashi kije kiyi wanka sai muyi maganar anutse " hanne ta fada.
Bayan magriba mlm kabiru chemist yaje aka yi masa allura aka bashi magunguna, kwata kwata hajara bata da nutsuwa da ka ganta kamar ace keeet ta arce, duk tayi furkai-furkai da ita kamar wacce tayi amai da gudawa.
Mlm kabiru ya lura da yanayinta amma da ya tuna sace ragon da akayi mata sai ya dauka ko satar ce take damunta, shiyasa yayi watsi da ita ko bi ta kanta baiyi ba.*Washegari*
Wacce ita ta kasance ranar idin babbar sallah, su gogarma dake cikin cell sun daku iya dakuwa tun suna gardama da taurin kai har suka zayyanewa yan sanda komai game da bukatar su hanne.
Duku-duku da farar safiya police suka taso keyar gogarma amota tiryen-tiryen har gidan hanne, lokacin ma bacci suke kamar asama sukaji ana bubbuga gida kamar za'a cire kofar, afusace hanne ta fito tana fadin, " bashin ko tara ko naci na wani banbiya ba, da farar safiya adinga mun bugun tashin hankali "Hanne na bude kofa tayi turus ganin yan sanda gefe guda kuma gogarma ne fuska ta haye tayi suntum, da sauri ta ja baya tana kokarin turo kofa wata macen police tayi sauri ta damko hannun hanne, furaira ce ta fito tana fadin.
" inna waye najiki shiru? "
Turus tayi ganin yan sanda, suka tasa keyar hanne sukayi waje.Da sauri furaira tabi bayansu cikin tashin hankali tace musu, " dan Allah bayin Allah lafiya me mahaifiya ta tayi muku, me tayi da zaku tafi da ita? "
Shiru ne ya biyo baya ba wanda ya tanka mata, kara shan gabansu tayi tana musu magiya.
Daya daga ciki yace mata, " zaki iya biyo mu station domin jin karin bayani "Mota aka nufi hanne za'a sata aykuwa da sauri tace, " yallabai nima ba nikadai bace akwai wata makociya ta ga gidanta cen tare da ita muka sasu aikin "
Aykuwa kai tsaye kofar gidan mlm kabiru suka nufa, buga kofa suke kamar yanda suka bugawa hanne kofa, zuwa wani lokaci mlm kabiru ya fito, da mamaki yake kallansu tare da fadin yallabai barka da aiki lafiya naga kun buga mun gida? "
" lafiyar ce ta kawo haka, fito mana da iyalinka muna gayyatarta a office dinmu " police din ya fada.
Da mamaki mlm kabiru yace, " iyalina me tayi muku"Cikin tsawa dan sandan yace, " kai bafa hira ce ta kawo mu ba ka fito da ita ko insa ladi ta fito da ita "
A sanyaye mlm kabiru yace, " basai anyi haka ba, inane station din naku nida kaina zan kawo ta zamu xo tare, nayi muku alkawari "
Kallansa police din yayi yace, " ka tabbata idan baka kawota ba inmuka dawo zamu hada da kai, mun baka nan da awa daya kuje sarada division "" Ke wuce muce " ya bugawa hanne tsawa.
_Zakusha kura-kurarai banyi editing ba._
_Vote_
_Comments_
_Share_MUM ASLAM Ce 😉
YOU ARE READING
SANADIN RAGON LAYYA CMPLT
Short StoryBil hakki mlm kabiru ya dage yake ta karantowa hajara ayatulkursiyyu, ya karanta yafi a irga idan ya karanto wannan aya yana kaiwa karshe zai karanto wata, duk atunaninsa aljanune suka make hajara, mamaki ne ya kara cika shi ganin takalmin hajara wa...