41_45

236 19 0
                                    

🐏🐏🐏
       *SANADIN*
               *RAGON  LAYYA*
           🐏🐏🐏
              🐏🐏
                    🐏

                  _By_
         *Ameera Adam*
    *AmeeraAdam60*
      @: _Wattpad_

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home of co-opration, peace,caring and accepting of correction amang us._

*_SADAUKARWA  GA  DUK ME SUNA FATEEMA HAR ABADA BAZAN MANTA DA KE BA, ALLAH YA JADDADA RAHAMARSA AGAREKI._*

_بسم الله الرحمن الرحيم_

        41_45

  _Not Edited_
Ku karbeshi da hakuri

Mlm kabiru kamar Wanda kwai ya fashewa aciki jiki a salube haka ya koma gida lokacin hajara na kwancen cen kuryar gado, sai da ya tsaya ya gama kare Mata kallo Yana wassafa abubuwa azuciyarsa sannan ya Fara bubbuga jikin gadon cikin takaici ya Fara yi Mata magana, " hajara ke hajara tashi" murza idanu ta farayi cikin bacci tace, " mlm Dan Allah ka barni indan matse wallahi barcin Nan bai isheni ba " takaici ne ya Kara rufe mlm kabiru cikin jin haushi ya buga Mata tsawa, " Ke dallah tashi baccin me Zaki karasa kunje kun jajubowa kanku masifa ki tashi mu tafi police station, idan munje sai inji takamaimai lafin da kuka aykata keda kawar taki "
     Rasss gaban hajara ya fadi cikin fargaba hajara tace, " mlm police station Kuma, me zaikaimu police station? "
      Mlm kabiru kallan kin Raina min hankali yayi Mata yace, " wato Baki San me Zaki je yi cen ba ko, da Kika samu zan tafi dake ta lallami idan sune yaushe zasu tsaya suna Miki magana har kina tambayar su, dama darajar aure Kika ci hajara wallahi da tuni na basu umarni sunyi gaba dake tunda ay duk tsuntsun Daya ja ruwa shi ruwa Kan doka " mlm kabiru na gama magana ya fice ya barta zaune tana zullumin abinda zataje ta tarar a police station.

    Hajara idanta ta wanke ta canja kaya ta zura hijabi, gaba daya taya aikin ne Amma hankalinta baya jikinta, bayan ta gama shiryawa rasa abinyi tayi haka ta dinga shiga tana fita kamar wacce taiwa sarki kaya yasa akamota, mlm kabiru gajiya yayi ta shige da ficenta ya rufeta da fad'a ba shiri ta wuce sum sum sum suka fita.

      Lokacin da aka Kai hanne cell gaba daya idanta ya Raina fata Bata taba zatan wannan harkar zata kwabe musu haka ba, tafi tunanin sanya hajara cikin matsala sai Kuma haka ta faru, mugun kallo suka dinga jifan juna dashi tsakanin hanne da dasu gogarma, kowa na aybata Dan uwansa acikin zuciyarsa.

     Mlm kabiru na zuwa ko bi ta kansa police din basuyi ba aka tasa keyar hajara cikin cell, dama tunda hajara ta hango hanne da gogarma ta saddak'ar da cewar kashinsu ya bushe, asirinta ya gama tonuwa, saboda tsabar fargaba jikinta har rawa yake yi, tana tsoron hukuncin da mlm kabiru zai yanke akanta, ita tafi tsoron hukuncin mlm kabiru ma da wannan badakar da suka aykata, yawun bakinta ne ya bushe makogaronta har d'aci yake, cikin zuciyarta take fadin ashe kuka ma rahama ne.

Mlm kabiru takaici hanashi magana yayi jikin bango ya samu ya tsaya Yana watsawa hajara muguwar harara, cikin zuciyarsa Yana mamakin yaushe hajara ta lalace da mugayen dabi'u haka, guntun tsaki yaja yaje ya samu wani police dake Kan kanta ya Fara yi Masa magana, " yallabai barka aiki antashi lafiya?"  Lafiya klau Alhamdulillah meye matsalarka" police din ya bashi amsa.

   "  Dama nine Wanda nace musu zan taho da baiwar Allah cen to kuma ansata cell banji laifin da ta aikata ba " cewar mlm kabiru.
      Police din juyawa yayi y klli cell din sannan yace, " ita Bata Gaya maka me sukayi ba? " Eh bata gaymun ba yallabai " cewar mlm kabiru.
    " To zarginsu ake da ayken sata Kuma da tada tarzoma ba bisa ka'ida ba, sun tura wadancen yan daban sunje sunyiwa mutane satar raguna sun kuma sassaresu " inji police din.

Mlm kabiru ji yayi kamar anbuga Masa guduma aka kansa ya Fara juyawa gefe ya nema Kan benci ya zauna ba tare da ya bawa police din amsa ba, hannuwa biyu yasa ta dafe kansa Yana jin wata irin hajijiya na fisgarsa, afili ya furta innalillahi wa'inna ilahirraji'una.
     Ganin yanayin da mlm kabiru yashiga yasa police din be Kuma bi ta kansa ba ya cigaba da yan rubuce-rubucensa.
      Hajara na cikin cell zuciyarta inbanda lugude ba abinda take yi Bata tabajin Dana sanin haduwa da hanne ba sai yau data kwabe Mata.

Bayan wani Dan lokaci mlm kabiru ne ya tashi ya koma gurin police din yace, " yallabai ina masu ragunan suke "
   " Basu karaso ba sai anjima " police din ya bashi amsa.

    Bakin wata bishiya mlm kabiru ya koma ya zauna Yana tunanin irin hukuncin da zai yankewa hajara, kamar Wanda aka tsikara zumbur mlm kabiru ya Mike ya fice daga police station din Kai tsaye gida ya wuce.

    Yana shiga su fiddausi ya samu sunyi carko-carko suna jimami, suna ganinsa da sauri suka tashi sukayi gurinsa cikin hadin Baki suka Fara tambayar sa, " Abba Ina kuka je kaida umma muna fitowa duk bakwa nan ? "

Dan Jim yayi ganin irin damuwar da yaran suka shiga Yana tunanin irin amsar da zai basu, dabara ce ta fado Masa yayi karaf yace, " yau da asuba ne aka kirata daga karaye anyi rasuwa shine dazu na rakata Tasha ta hau mota, kuna bacci shiyasa ban tashe ku ba Amma bazata Dade ba kwana biyu zatayi ta dawo "
      Sai alokacin yaran suka Dan saki jiki fiddausi ce ta Kara tambayar sa, " Abba ko goggo nene ce ta rasu Dan ta tsufa sosai gashi dama Bata jin Dadi "
    " To da yake dai basu Fadi Wanda ya rasu ba, sunce dai taje anyi rashi Kuma banda abinki fiddausi ita mutuwa ay Bata kyale yaro ba Allah yasa dai mu cika da imani " cewar mlm kabiru, gaba daya yaran suka amsa da Aameen.

   Daki mlm kabiru ya shiga ya kwanta Yana wani tunani afili ya furta, " hajara wannan Karan kinkai ni bango Zaki dandana ba abinda zai maidani police station, Zaki ta zama acen har sai lokacin da kikayi nadama da kanki tukunna zanje inyi bellinki, idan inada Rana Zaki gani idan ma banida ita Zaki gani, samu ba abinda baya sawa jindadi ne yayi Miki yawa Amma wannan Karan zan barki da hannen zanga yanda karshen kawacen naki zai kasance, ay bahaushe yace shiru ma magana ce.

Hajara na  tsaye ta hada Kai da gwiwa tun shigarta ba abinda ta iya furtawa hanne saboda tsabar bakin ciki da takaici, sai ayanxu hajara ta iya samun sukunnin yin hawaye, hanne ce ta kalleta ta kece da dariya sannan tace, " hajara meye abin hawaye Dan Allah....... " Cikin tsananin bacin rai hajara ta bugawa hanne tsawa, " dakata mun hanne wallahi na tsaneki hanne kin cuceni kin cuci rayuwa ta sai yanxu na tabbatar da ke ba kawar arziki vace, kin jefa cikin masifa Kuma yanxu kina tambaya ta kukan me nakeyi, nayi danasanin haduwa dake hanne zamantakewata dake bata amfaneni da komai ba sai tarin nadama, gaskiya hanne ke masifa ce kina gani yanxu aurena Yana cikin wani hali, Allah na tuba ka tafemun abunda na aikatawa mlm, Allah ka tausasa zuciyarsa, Allah karka bashi ikon yanke mummunan hukunci akaina " hajara ta karasa fad'a tana fashewa da kuka me tsuma zuciya. 😭

      Kallan shekeke hanne tayi Mata sannan ta Kara fashewa da dariya sai da tayi me isarta harda rike ciki sannan ta tsuke fuska tace, " hajara yanxu na tabbatar da Baki da hankali ke kina tunanin duk shawarar da nake Baki ta alkairi ce? Inbaki sani ba ki sani wallahi hajara ban taba yiwa wani kyashi ba sai ke, keni wallahi bazan iya fasalta irin haushin ki da nake ji ba, tun farko dawowa ta unguwar gaida na fahimci irin gatatawar da mijinki yake Miki da yanda yake nannan dake, sai na Fara jin inama mijina ne, da farko nayiwa mlm kabiru kallan sha'awa ne da zummar ya zama abokin hulda ta kamar yanda nakeyi aboye, hakan ne yasa na kasa boye bukatata har naje na sameshi, mlm kabiru cin mutumcin da yayi mun tunda nake ba'a taba mun irinsa ba, daga baya ne na fahimci tsantsar kaunar da nake masa, na Kara komawa da bukatat ta biyu Nan ma bai saurareni ba, ke har gurin bokaye Nasha zuwa da bukatata Amma ba nasara saboda tsantsar ibadar sa, wannan ne yasa na kuduri niyyar sai na Bata duk wata kyakykywar alakarku, shiyasa na tsiri shigowa gidanki idan mlm kabiru bayanan saboda nasan idan mlm kabiru ya ga Ina zaryar gidan sa zai dau wani hukuncin akaina, kuskure Daya mlm kabiru yayi Daya kyaleki muke ma'amala ta yau da kullin, na tabbata da nayi galaba, nasan babu wani hukunci da mlm kabiru zai dauka akanki da ya wuce saki, Kinga mun zama daya kenan " hanne ta karasa maganar tana Kara kecewa da dariyar keta.

       Sororo hajara tayi kamar mutum mutumi tana kallan hanne kamar wata me matsalar kwakwalwa, da ace awaya taji wannan kalaman zatayi tunanin wani yake Mata magana amadadin hanne, da ace sako ne hanne ta ayko Mata dashi to zata zaton batan hanya akayi, ba mamaki ba har tsoro hanne ta fara bawa hajara, ja da baya hajara tayi cikin takaici da bakin ciki tana fadin, " Allah ya isa tsakanina da ke kinci amanata Amma Allah baya bacci Allah zaimun sakayyah " cewar hajara.

    Hanne dariya take zuciyarta wasai tana nuna hajara sai ta Kara fashewa da dariya, hajara takai bango a tsananin bakin ciki har Bata ganin gaban ta sosai, jin dariyar da hanne take yi Mata ne yasa ta Kara fusata, aykuwa hajara tayi kukan kura ta tafi da gudu ta damko hanne ta rufeta da duka.

Jibgarta take kamar Allah ya aykota duka take Mata iya karfi ta, ta ko ina tana dukanta, jin dukan da hajara take Mata ba na kare bane yasa hanne ta fara ihu tana neman dauki, kafin police suje tuni fuskar hanne ta haye tayi suntum.

_Vote_
_Comments_
_Share_

     _MUM ASLAM Ce_😉

SANADIN RAGON LAYYA CMPLTTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang